Sashe 76
Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kuka sosai Maa sakinah din tafasa tana kasa riqe kanta sbd har abada sunyi rashin da bazasu taba manta radadin sa ba,
Sunyi rashin da shine mafi ciwon rashin da sukai a baya Bayan nan.
BAHAR dake kwance shiru zuciyarta bata iya komai Bayan bugawa ahankali sbd komai ya tsaya mata cak tana jin sautin kukan Maa sakinah yana shiga kunnuwanta a hankali yana ratsata sbd tasan kukan rashin Abaa dinta ne akeyi.
Bude idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga cikinsu a sanyaye tana sake Numfashi me sanyi Mara sauti batareda ta motsa daga kwancen datake a jikin matar da bata taba saniba a zahiri Sai a tarihi amma ayanzu da ita kadai zatai rayuwa.
Tafiyar kusan wuni guda sukai kafin jirginsu ya sauka a qasar BOYEM suka fito tareda securities din NUAB din duka da aka hado su dasu shikuma daga shi sai aleey suka koma.
Motocin alfarmar GHAZ ne suka daukesu daga airport zuwa Masarautar BOYEM me tarin abubuwa da tarihi dama Wani tarihin da zaa kafa.
Ko a cikin mota hannun BAHAR din yana cikin na Maa ta riqe cikin nata tana bata dumin dazai Haba gangar jikinta qarasa rasa kanta.
Duk duniya da Aljannar duniyar dake tin daga babbar gate din farko ta masarautar bai shiga idanuwan Bahar ba bare zuciyarta sbd komai na rayuwarta a yanzu rufe yake gap babu kowane irin Sauran shaawa ko burgewa a rayuwa da zai shigeta dan haka idanuwanta a kafe suke kawai a waje tana kallan wajen amma kwata kwata tinaninta baya jikinta ko daya tayi nisa a tinanin rayuwar datai a baya da mahaifinta Wanda a yanzu yana kwance cikin qasa,
Tafiya sukai suka sake wuce gate na biyu har zuwa gate na uku suka shige akai parking motocin bakin hanyar da zata kaisu bangaren cikin gida kai tsaye aka bude musu motocin dukansu su biyun a lokaci daya.
Maa ce ta fara fitowa a natse cikin sanyin jiki ta sauke ajiyan zuciya da Numfashi kafin ta zagayo ta miqa hannu cikin motar ta Kama hannun BAHAR wadda bata motsaba tinda aka bude mata motar ta janyota a hankali cikin kulawa ta fito motar,
batareda ta saki hannunta ba ta jata a natse zuwa ciki suna tafiya babu me karfin jiki.
Duk Taku daya da Bahar ke yi Wani siririn sautin sarkar kafarta ta mahaifiyarta data gada ne yake tashi tareda Wani irin sakar da nutsuwa da saka son juyowa ga duk Wanda sautin ya shiga kunnensa dan hakane duk tayi Taku daya bayin dake jere a hanyar sai sun sauke kansu qasa cikeda girmamawa ga Maa sakinah wadda kowa yasan matsayinta na shaqiqiyar Wishmah kuma jakadiyar bangaren wishmah ta biyu.
Kai tsaye hanyar bangarensu Maa ta nufa da BAHAR wadda har lokacin duk inda Maa ta jata saka kafa kawai takeyi ba Wani kuzari a jikinta.
Isowarsu gap da hanyar data raba bangaren Queen HAILE da bangaren Wishmah Ayanah a daidai wannan lokacin Li’uli ASIM ALMAZZ ya fito bangaren mahaifiyarsa cikin shigar sky blue cashmere mai fitinanniyar tsada qamshinsa yana sauya niimar gurin take dukkanin bayin dake hanyar suka sauke kansu qasa suna tsayawa cak inda suke har saiya wuce.
Maa sakinah dake gap da shigewa da Bahar bata juyowa tayi a natse dan basa girmamawa itama a natse Banda Bahar da batasan me takeyiba daga kafarta tayi tana cigaba da Takawa ba karfi a gangar jikinta ko kadan.
Sautin takunta ne da sarkar kafarta ke fiddawa a natse a gurin daya dauki tsit tamkar babu rai ko daya a gurin sbd bada girmamawa garesa ya sakasa tsayawa da takunsa cak yana dakatawa.
Sake ratsa kunnuwansa sautin yayi Wanda ya sakasa juyowa da Wani irin nutsuwa da mamaki yabi inda sautin ke fitowa da kallo a daidai lokacin Maa Sakinta ta riqota cikin nutsuwa da juyo da ita a hankali sbd inda yake dosa ba can zasu nufa ba.
Kafafunta dake rufe cikin doguwar rigar dake jikinta ash Kala wadda batada adon komai sedai daidai jikinta take ta sauka qasa sosai harma tana dan ja da kasa kadan mayafin rigar ne kadai yakeda adon dayake qawata rigar da fuskar da zata saka kayan ya tsayar da idanuwansa yana kalla amma babu ta inda kafarta ta fito se sautin.
Dagowa yayi a natse ya maida kallansa kan fuskarta zuciyarsa na dauka Wani irin Zafin mamaki da jin abinda bai taba ji ba a bayi sedai yayan sarautar ne kadai sukeda iko da wannan damar dan haka mamakinsa ya dan qaru yana bude idanuwansa da kyau a kanta.
Fuskarta dake bayyane ya zubawa idanuwansa yana kasa daukesu daga kanta mamakinsa na sauka ahankali tamkar wutar da aka zubawa ruwa,
Bin fuskarta yake sakeyi da kallan dayake sake saka zuciyarsa mamaki da jin Wani irin yanayin daya sakasa kasa dauke kallansa akanta.
Shiru gurin ya sake dauka musamman da Bahar din bata sake ko motsawa ba har tsawon mintina kafin ya dauke idanuwansa daga kan kyakkyawar fuskarta ta jinin GHAZ ya juya a natse batareda yace komaiba ya wuce zuciyarsa na riqe kamanninta da kai tsaye suka isa gareta.
Yana barin gurin Maa sakinah ta Kama hannunta suka nufi kofar da take aka bude musu ita gabaki sbd girmamawa suka shige aka rufe.
Babban palon dayake na farkon isa suka shiga Maa sakinah ta sake ajiyan zuciyar samun isowa gida cikin Amintci.
Dakinta kai tsaye ta wuce da Bahar,
Komai na dakin a gyare yake sbd babu ranar da baa Shara so biyu a kunna qamshi,
Ac ne kadai baa kunne ba sai wuta dan haka kai tsaye remote ta dauka ta kunna komai Wanda take haske ya haske dakin gabaki daya tamkar fitowan rana,
Makeken bedroom ne dayake dauke da royalbed me kyau da girma sosai sai Sauran set din royalbed din su wardrobe da dresser tareda bedside da wata lallausan Turkish carpet da table sai couch masu Laushi da tsari,
Duk wani jin dadi da tsarin dayake bayyanarda Hutu da kwanciyan hankali shine a dakin komai a tsaf ga sanyin ac din ya fara ratso wa yana kokarin Kama dakin.
Zaunar da ita Maa sakinah tayi tareda zare mata rufar kanta a hankali gashinta dayake rufe ya zubo a hankali yana bayyana Maa ta sake sauke ajiyan zuciya tana kallan baiwar data shigo dakin dauke da babban tray da kayan sanyi da fruits masu sanyi ta bude baki tace
‘Ki hada ruwan wanka masu dumi’
Gyada kai baiwar da ake da Salmah tayi tana ajiye tray din ta juya kanta a qasa ta nufi toilet din dayake dakin na Maa ta shige dan hada ruwan wankan.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
End of part 1