← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 76

Sashe 2

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu taba sanin akwai gari a tsallaken ruwan dasuke bi su wuce ba saida tsautsayi yasa suka bi wasu bayi da zasu Kama ba suka gudu har cikin dogayen itatuwan da suka rufe dajin hanyar garin daga Bakin ruwa dan haka Mutum ashirin da suka bi bayin suna ganin sun ratsa itatuwan binsu sukai suka ratsa ciki Wanda suna shiga tin anan mamakinsu ya fara dan haka suka bazu a dajin suka bisu.
#MAMUH
#SLAVERY
#BEST MALE CHARACTER
#LION OF BOYEM
#BEST LOVE STORY
#ROYALTY
#BRAVERY
#HISTORICAL
#LOVE/HATE STORY

HAYATEEM
700
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070

2
Shugaban kusra subawa hanyar da sukabi idanuwa yayi sosai yana kalla yana Jin wani iri a jikinsa sbd duk inda aka samu hanya akabi to tabbas idan an kuwa ankai karshe komai nisa bazaa rasa inda zaaje ba a gurin.

Gudun cetan rai bayin sukeyi sosai suna Waiwaye sbd mashin da ake harbo musu masu tsananin kaifi da dafin da take zai karya duka garkuwan jikinsu matiqar ya tabasu ko kadan ne.

Basusan ina suke jefa kafafunsu ba bare inda suka dosa gudu kawai sukeyi na tashin hankali da tsananin tsoron da zuciya bazata iya dauka ba.

Nisa suke Qarama suna kusantar hanyar ANJOM wadda take cike da hadari batareda sun sani ba.

Cikin tsananin rashin Imani da babu ko Kadan a ran wainda suke biye dasu Wanda yake kaman shugaban Sauran ya bude baki yana tsaya wa daga gudun dayake ya Fiddo harshensa dayake da duhu sosai ya lashi fatar bakinsa dayake baqi qirin ya daga Kai sama yayi wani irin Ihu me karfi kafin ya sake dariya kaman me ciwon aljanu ya bude murya sosai yace

‘Dayan zuciyarsa nakeso a hannuna kafin ta Dena bugawa daga fitowa kirjinsa,
Dayan kuma idanuwansa nakeso zanyi wa dass sarka dasu a wuya’

Sauran na Jin hakan suka qara gudu suna sake Harba musu arrows masu tsananin tsini.

Na farko ganin ya kusa fita bishiyoyin zuwa filin dajin dayake hango hanyar da yasan zai iya samun gurin tsira da sauri ya sake tsananta gudu kafafunsa na fidda wani irin Jini na fashewan kafafunsa da tarin qayar da suke cike da tafi harma da saman kafarsa.

Na bayansa kasawa ya fara yi sbd zuciyarsa dake kasa dauka fara rage gudu yayi kafafunsa na jinin dayafi na gabansa hancinsa ma jini ne yake fita dan haka hannunsa ya daga ahankali ya Zare jakar fatar jikinsa Qarama ta kudin da suke tare dasu ya daga zai jefawa dan uwansa ya bude baki daqyar zai Ambaci sunansa wani irin jini me karfi ya feso ta kirjinsa,.

Cak ya tsaya hannuwansa na dawo wa qasa ahankali idanuwansa na yin jajir kaman zasu fidda hawayen jini sbd tsananin azabar dasuke bayyanarwa,

Ahankali ya saukar da Kansa zuwa kirjinsa ya kalli tsinin mashin daya shigo ta bayansa ya bullo ta kirjinsa.

Sarewa kafafunsa sukai cikin tsananin azabar da bata da Kama a lokacin.

Kafin ya qarasa kaiwa qasa wani mashin ya sake ratsa wuyansa ya bullo ta gaba take wani jinin me yawan gaske ya feso ta bakinsa da wuyan yake ya zube a gurin ba rai a jikinsa.

Suna isowa gurin Sauran basu tsaya ba tsananta gudu sukai dan cimma daya sbd a tarihin kusra basa rasa duk Wanda suke bi.

Mutum biyu ne suka tsaya Akansa ba wata wata suka fidda wata kakkaifar wuqar da ko ice zaa yanka da ita bazaiyi Kyan gani ba take suka fara huda kirjinsa dan cika umarnin shugabansu.

Jemo daya waiwayo yaga dan uwansa rayuwarsa ta riga ta fita take yaji zuciyarsa da jikinsa na sarewa wani irin Ihun kuka ya fasa yana cigaba da gudun da yasan ba tsira zaiyiba

Kuka yake yi sosai sbd dan uwansa jininsa dashi kadai yake dashi a duniya baisan yaya zai yi rayuwa babu dan uwansa
Juyowa ya sakeyi koina na jikinsa na wata irin rawa gudunsa na tsananta
Juyowansa da shigar mashi a goshinsa lokaci dayan hakan ta faru take ya tsaya cak yana zubewa gefe ahankali jini ya gangarowa zuwa idanuwansa take ransa shima ya fita a gurin.

Cikin rashin imanin fa basuda shi suka qaraso suna durqusawa gabansa Sauran kuma hanyar da suke hange suka zubawa ido wadda ganyen Shuke shuke suka rufe amma sunada tabbacin indai akwai shuke shuke a gurin to tabbas akwai mutane kokuma gari sbd shuke shuke ne da qaramin gari sosai bazai iya ba sai garin daya tara mutane da dama hakama kuma indai har akwai gari a cikin gurin to tabbas irin hakan suke so garin dayake a boye Wanda har zasu Kai hari su gama su tafi baa sani ba.

Mutum hudu ne a cikinsu suka tinkari hanyar zuwa shuke shuken da suke hankowa daga nesa sosai suna dake zubawa hanyar ido sosai daga nesa suna kasa yadda da akwai gari a cikin wannan Jejin me tsananin hadari.

Tafiya suke suna sake Sauri sbd wannan abune na farin cikinsu,

Cak suka ga na gabansu ya tsaya tareda kallan qasansa da sauri sakamakon abinda yaji sai kuwa ga maciji baqi qirin yana wani irin qyalli cikin rana.

Wuqar hannunsa ya saka ya fizgo macijin da ita ya rabasa biyu ya jefar suna cigaba da tafiya cikin zalamar son kaiwa inda suke son,

Taku goma suka qara dafin macijin ya fara aiki a jikinsa duk da ya yanka gurin daya cijesa da wuqa dafin ya biyo jini yana fita.

Wani irin zufa da zafi jikinsa ya fara dauka take bugun zuciyarsa ya fara sauyawa ya tsaya cak tareda durqusawa ya sake yanka fatar jikinsa da wuqa yana turo jini waje da hannunsa.

Daga bayansa wani macijin yaji ya kuma sararsa take ya juyo yana kokarin Kai masa hannu ya kashe wani ma ya sake sararsa take ya fara kokarin mine wa amma ba damar hakan sbd sankarewa da jijiyoyin jikinsa suka fara suna Dena aika jini koina.

Ganin hakan Sauran yan uwan nasa basu tsayaba suka cigaba da tafiya sedai ko ina basu kaiba dukkaninsu suka zube a gurin kowannesu kumfar tsananin dafi na fita jikinsu na dafin macizai.

Sauran na ganin hakan suka fahimci me yake faruwa a gurin Wanda hakan ya gama basu tabbacin da suke nema na cewan akwai gari a karshen dajin.

Jiya wa sukai suka koma Bayan sunyi doguwar tafiya me tsayi kafin suka bullo bakin gabar mahaukatan ruwan.

Suna isowa suka sanar da Sarkinsu gabaki daya bayanin komai.

Shiru yayi idanuwansa a rufe wani irin rashin Imani da bushewan zuciya na ratsashi batareda yace komaiba.

Shiru na mintina a hakan kafin ya bude jajayen idanuwansa da basuda haske ko Kadan ya sauke Akan zuciyar da suka kawo masa tana jini ya dauka batareda ta juyaba ya jefawa mahaukacin karensa me tsananin girma da munin kallo tareda tsoron kalla Wanda yaci ya ginu da cin zuciyoyin mutane ko wani idanuwansu.

Gashashen maman Dabbar ruwa da aka kawo masa ya miqa hannunsa ya fara ci batareda ya wanke ko goge hannu ba.

Yaransa ya sake dagowa ya kalla wainda adadin yawansu baisan iyaka ba dan tsananin yawansu ya bude baki muryansa me tsananin kauri da rashin dadin saurara yace

‘Idan gari ne a dajin nan kaman nisansa daga yanzu ya zama na kusra,
Dukkanin me rai tin daga kan dan Adam har dabbar datake da rai sun zama a cikin lissafin kusra,
Wannan Karan bayin na musamman ne sbd lokacin da kusra zata gina Masarautarta da qasa me sunan kusra yayi dan kuwa bayin da masarautar BOYEM take buqata daga gareni zasu fito dan kuwa acan ne kadai zan Kai bayi na mallaki cikar Burina da aka haifan dashi,

Babban burin iyaye da kakanni na Akan kusra takai matakin mallakar qasar kanta da mulkin kanta Akan siyar da bayi shine kai Bayi a BOYEM,

Buri ne da kakana bai cika ba,babana bai cika ba dan haka nine zan cika wannan burin kota halin yaya,

Bayin BOYEM na musamman ne sbd farashin d ake zubewa a siya Wanda yake sauya rayuwan duk me siyar da bayi,
A guri daya BOYEM ke siyan bayinta bata taba sauyawa ba sbd tsaro da izzarsu dan hakan ne kusra basu taba samun wannan babbar damar ba duk kuwa qwarewansu a harkar bayi a tarihi dan hakanne duk wani kusra dayake duniya yasan burinsu da macimmarsu daya ne wato shiga BOYEM Kai bayi Wanda daga ranar da BOYEM ta siya bayi daga gurinsu sun samu yancin kafa daularsu yawo ya qare musu sedai azo daularsu a siya bayi koda zasu Kai sama da bayi rai dubu dari.

Hadiye Naman bakinsa yayi yana sake bawa Kansa tabbacin wannan garin shine garin nasararsa sbd zai dauki bayi daga garin harya haura qasar baa saniba sbd a boye suke labarin harin da suka kaiwa garin bazai fita ba bare ya samu tangardar tafiya duk da baa taba kamasu ba amma bibiyan da ake musu idan ya kaiwa gari hari ya kwashe mutane yana basa Tangardar mutuwa bayinsa sosai sbd basa tsaya wa duk tsananin rashin Kyan ruwa haka suke tafiya a cikinsu batareda sun tsaya kowace qasa ba dan hakanne bayin da sukayo safara suke mutuwa sosai sbd rashin sabo amma a yanzu idan baa saniba tafiyar kwanciyan hankali zasu yi ba jigata bayi har zuwa BOYEM Wanda tsafa da Kyan bayinsa zaisa wannan Karan su samu shiga BOYEM din.

Tutar bada izinin farauta ya miqa hannu ya fizgo ya daga sama cewa

‘Cikar burin kusra’

Cikin tsananin Murna da sauti me karfi na mutane masu yawan gaske ya ringa tashi suna amsa wa da

‘Cikar burin kusra’

Dajin gabaki dayansa da ruwan haka maganar ta ringa amsa wa dan haka take aka juya kan Jirgi zuwa baya inda suka baro zaa tsaya.

Da Asuba suka isa inda Jirgin ke tsayawa kuma a cikin asubar suka hawo qananun Jirguna suka koma kusan su sama da dari biyu suka yada zango a cikin dajin inda zasu zauna kafin fadawa garin.
#MAMUH
#ROYALTY
#WEALTH
#LOVE
#BEST MALE CHARACTER
#NUAB ALMAZ BOYEM
#GHAZ
#KUSRAH
#BEST LOVE/ROMANCE

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070

3
Daga wannan ranar burin kusra gabaki dayanta ya koma Akan ANJOM,
Chapter 2 · 0% Book details