← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 76

Sashe 50

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akan Zuhrah jajayen idanuwanta da taka suka ringa rikida suna qara rinewa suka sauka tana tsaye tsakiyar tenya da babbar baiwar da aka ware mata tareda wasu bayin sunkai goma a bayansu,

Navy blue Kayane a jikinta da adonsu yake daukan ido fuskanta a rufe da mayafi mai Shara shara da ake iya ganin fuskanta amma ba sosai ba hakama itama tana iya ganin na waje amma ba sosai ba,

Kasa motsawa Ayanah tayi daga inda take tsaye hakama idanuwanta basu motsaba daga kafe Zuhrah datai dasu kaman yanda zuhran itama ta kafeta da nata idanuwan dake son tsiyayo hawaye amma sun qafe qaf sbd halinda zukatansu ke ciki,

Tsananin son ganin fuskan Zuhrah ne Ayanah taji yana danne kirjinta kaman zai kasheta amma Dukkaninsu babu Wanda yakeda ikon bude mayafin daya rufe da fuskarsa batareda ya isa ga Wanda shine kadai yakeda ikon budewa ba dan haka basuda daman ganin fuskokin juna da suke tsananin doki fiyeda komai na duniyar,

Tsit duniyar tayi musu da gurin ma gabaki daya,

Rawa jikin Ayanah yakeyi ahankali tanajin kafafunta na kasa daukanta bakinta wata rawa yakeyi amma ya kasa budewa dan ta Ambaci yar uwarta,

Zuhrah kasa riqe kanta tayi ta daga kafarta tayi Taku daya dan zuwa ga yar uwarta amma tenya ta saka hannu ta riqe hannunta daya batareda tace komaiba ta girgiza mata Kai tana Hana idanuwanta cikowa da hawayen tausayinsu sbd iya abinda zata iya musu kenan na ganin juna amma bazasu taba magana ko rungumar juna ba Bare nuna sanin juna sbd tarin bayin datake tareda su da kuma cameras dake koina dan haka haka sake riqe hannun Zuhrah dake Wani irin rawan jiki tayi gam tana dagowa ta kalli Ayanah dake tsaye kaman an dasata ko baa fada ba kowane lokaci zuciyarta zata iya bugawa dan haka Juyawa tafara yi da Zuhrah a hankali zasu bar gurin Ayanah ta Lumshe ido ahankali ta rufe tana kokarin zubewa kan gwiwanta sbd kafafunta da suka gaza sakinah tayi saurin riqota duk da NUAB yana jikinta,

Zuhrah ma kasa daukanta kafafunta ke kokarin amma tenya ta hanata kaiwa qasa ta tareta jikinta suna ci gaba da tafiya can qasan kunnenta ta rada mata

‘Kada ki Bari sadaukarwar yar uwarki da rayuwar data zaba miki ta tafi a banza dan sbd ki samu rayuwar da zaki rayu da aminci ta zabi rabuwar koda hakan zaiyi sanadin mutuwarta ta riga ta zaba inganta rayuwarki dan haka ki saka dangana indai kunada rabon sake haduwa Allah zai hadaku cikin yadda da amincinsa idan kuma babu rabon sake haduwan shikenan kuwa juna fatan alkhairi ko a raye ko mace amma daga nan kaddarar ku ta riga ta rabu’

Wasu irin hawaye masu tsananin Zafin da Zuhrah batasan dasu bane suka gangaro daga idanuwanta suna sauka fuskarta tanajin tamkar an zare mata Wani hasken rayuwarta yabar jikinta dan haka tenya tafara tafiya da ita batareda tasan inda take Dora kafafunta ba har suka bace wa gurin batareda kowannensu ya sake waiwayowa ba har suka bace sukabar su Ayanah gurin tsaye wadda ta kasa dauke idonta daga Zuhrah harta bace wa ganinta ta sake rintse idanuwanta ahankali tana Jin Wani nauyi ya danne kirjinta daya saka numfashinta kasa fitowa ta daga hannunta ahankali tana son dorawa Akan kirjinta amma hannun bai qarasa isaba bakinta ya feso Wani irin jini da karfin gaske daya fesu a Fuska da showel din NUAB dake hannun sakinah.

Jajir idanuwanta sukai tana bude su ahankali zata sauke Akan ‘danta hakan bai samuba ta zube a gurin,

Wani irin gigitaccen raruma sakinah takai mata tana rungumota jikinta ta hada da NUAB data kasa bawa kowa tana kankamesu tafara kiran sunan Ayanah din da karfin gaske koina nata ma rawa da shiga mafi girman rudanin rayuwarta,

Bayin dake tsaye suma duk tashin hankalin suka shiga inda take akaje da gudun gaske aka kirawo doctors aka dauketa zuwa bangarenta cikeda matsanancin tashin hankali da rikice wa.

Babban tashin hankalin da Masarautar ke shirin shiga shine rasa macen da a wannan Daren duk Wanda yake Masarautar ya tabbatarda itace cikar rayuwar sultan YASAR ALMAZ BOYEM dan kuwa take a qanqanin lokaci wishmah ta zama abar tsananin tausayi da tsoro sbd yanda ta koma fara tas tamkar babu digon jini a jikinta hakama babu alamar ma zata farfado dan hakanne likitocin dake kanta hankalinsu ya tashi da suka gama tabbatarda ciwon zuciyane mai tsananin gaske yake Neman rabata da ranta da a yanzuma basusan yaya ma zasu fara ba dan kuwa tinda ta riga ta fara aman jini abin yayi Nisan da sai wani ikon Allah.

Mummunan labarin na isa kunnuwan sultan kasa yadda yayi da zai rasata dan haka da kansa ya iso cikin bangaren matansa a Karan farko ya isa bangaren Ayanah wadda take kwance fayau dasu oxygen da komai kamar ba ita ba a lokaci daya Allah ya maidata abar tausayin da kowane lokaci zata iya barin duniya.

Tenya da sakinah da duk bayin da suke bangarenta suna cikin tashin hankali da damuwan da batada sauki a cikinta ko kadan sbd ganinta kadai Wani irin kuka mai tsima zuciya yake saka sakinah da idanuwanta harsun fara qanqancewa.

A kuma daidai wannan lokacin yar uwarta daya tak datake da ita a duniyarta datake mutuwa dan babu tabbacin rashinta a wannan kwanciyan datake duk wani mai kaunarta kuka a wannan lokacin ne ake maidata cikakkiyar macen da itama tata zuciyar gap take da bugawa sbd daci da mataccen yanayin dake cikinta tareda sanin yar uwarta na can rai a hannun Allah a lokacin sbd labarin masarautar a take ake sanarwa dan kowa ya kiyaye.

******koda gari ya waye sultan yana Zaune a daddumar da yayi sallah sbd koda minti daya bai rintsa idanuwansa ba rokon Allah yakeyi yana qarawa ya raya AYANAH GHAZ koda shi ne zai tafi a madadinta zaiyi fatar ta rayu sbd dandana farin cikin da bai taba gani a idanuwanta ba ko so daya,

Yana fatar ta rayu taga abinda ‘danta zai zama koda hakan zai bata farin ciki da murmushi koda so daya ne a rayuwarta kafin mutuwarta hakama bazai taba son NUAB ya rayu a hannun kowace macen daba mahaifiyarsa ba dan haka ya ringa fadawa Allah ya tashi kafadanta.

Masarautar BOYEM ta dauki zafi dan kuwa duk manyan likitocin qasar kaf suna cikin masarautar dan Neman lafiyar Wishmah wadda take sake fading kaman ba macen da kyanta yake cike Idon duk mai kallanta ba.

Tenya da sakinah ne tsaf a gurin kulawa da bada kariya ga NUAB Wanda Bayan sultan kaf duniya babu Wanda yake daukansa sai su biyun sbd tsaro,
Ita kanta wishmah din tsaro sosai sultan ya saka a bangarenta na gaske dan kuwa akwai barazana sosai da hadari a yanayin datake yanzu dan haka sosai aka saka ido da tsananin tsaro babu me shiga gurinta idan ba doctors da tenya da sakinah ba sai kuwa shi mai gayyar Wanda hakan y saka HAILE kusan rasa hankalinta.

Tinda aka kafa tarihin masarautar BOYEM babu Sarkin daya taba taka kafafunsa Yazo dakin macensa sai sultan YASAR Wanda hakan ya kafa Wani irin tarihi mai girma da shakka a zukatan matansa da manyan fada da suke ganin kaman zai iya rasa kansa Akan wishmah dinsa dan haka suka fara janyewa daga kaunarta rashin yadda da yar tsana na maye gurbin.

MARAKI ma da batada matsala zuwan sultan bangaren ya saka hankalinta tashi ta qullaci Ayanah har zuwa matakin karshe tana yadda da itace macen data samu zuciyar da shekarun aurensu da jininsu bai samar musu ba dan haka kishinta ya fara komawa qiyayya me karfin gaske datake Neman take ta HAILE a fili.

*****A Karan farko da tsoro da shakka suka darsu a zuciyar sultan me BOYEM gabaki daya sbd ganin macen da zai iya bada rayuwarsa dan karewa tako Ina hadari mai girman gaske yana dabaibayeta dan kuwa manyan fada da gaske a yanzu sun janye duk wata alfarmar su da kaunarsu akanta da gaske a iya matsayin mistress din suke kallanta,
Hakama bangare daya zazzafan kiyayyar maraki akanta ta fito fili ga kuma HAILE da ita har abada yasan idan tanason abu zata iya komai akansa dan haka rayuwan Ayanaah daya NUAB bazata taba fita hadari da halaka ba a masarautar.

Damuwa mai tsananin gaske da tsaro ya qara Akan Wanda yake basu gashi har lokacin bata farfado ba,

Sakinah ma da tenya ta ko ina komai yayi musu zafi dan kusan so uku duk tsaron da ake bawa bangaren Ana samun attempt ta kawo karshen rayuwarta.

Da wannan tashin hankalin sultan da kansa ya dauketa daga qasar zuwa Germany.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee

46
Daga sultan har su tenya saida suka isa qasar Germany suka samu nutsuwan jinyar wadda cikin ikon Allah ta farfado amma bawai samun lafiya gabaki daya ba,

Farfadowanta sabuwar damuwa ya haifar musu sbd gabaki daya ta sauya daga Ayanah zuwa wata halittar daban,
Baqin cikinta ya ninka,
Quncinta ya ninka,
Damuwanta ya ninka,
Shiru da rashin kuzarinta ya ninka sosai ta yanda bata magana kwata kwata hakama bata kallan kowa NUAB ne kadai Wanda take kalla a koda Yaushe.

Wata hudu suka share a qasar Germany na jinya kafin sukai guda daya na hutawa suka tattaro suka dawo BOYEM inda tarin abubuw suke jiransu ciki harda sabuwar rayuwar da basu tana tsamammanin Ayanaah zata samu ba daga sultan dan kuwa sauyi ne me sanyi yafara nuna mata ta hanyar dauke kulawansa kwata kwata akanta da NUAB a bisa wani sirri da shi kadai yabar wa kansa,

Masarautar a yanzu ta dauki Zafi iya zafi na kowa ya zabi inda zai tsaya sbd shirin karban matsayi da mulki tako wane Hali idan lokaci yayi,
Chapter 50 · 0% Book details