← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 76

Sashe 48

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

43
Gagarumin radin sunan NUAB ALMAZZ YASAR BOYEM aka fara yi kafin na ASIM YASAR ALMAZZ BOYEM aka ringa barin dukiyar data ringa jijjigar bayin fadar sultan sbd daukan kyaututuka zuwa bangaren iyayensu mata wato bangaren Ayanah dana HAILE dukda yawan kyautikan bangaren uwar magaji ta ringa sauka sbd yanda aka ringa barar masa da dukiya.

Da dare ne bikin wishmah dan haka anfi kwana uku Ana shirye shirye da decoration na fadar inda zaa qaddamar mata da matsayinta Wanda kowa saiya sheda kuma ya bata matsayinta datake dashi na macen farko data karbi matsayin Bayan shekaru masu yawa gata kuma uwa ga ‘da na farko daya haske zuciya da idaniyar mahaifinsa da zuwansa duniya.

Masu kwalliyar wishmah da kanta kusan su biyar ne sbd ado ke na musamman da Ayau zai nuna Itace mace ta farko da kyanta zai dake na queen HAILE hakama macen data motsa zuciyar mai girma sultan dan haka wasu irin sarkokin zinari masu daukan ido da kyau ne aka fara shigowa dasu a tray Layi Layi kowa da abinda ya dauko a cikin bayin da suka fara shigowa suna jeruwa,

Tenya ce ta shiga qarshensu dan itace a tafe dasu,

Fara daukan sarkokin akai aka saka mata Akan wata irin lafiyayyar kwalliyan da akai mata ta maroon doguwar rigar datake jikinta data bi jikinta ta lafe daidai shape dinta mai tsari kaman bata haihuba,

Wasu irin stones dake daddabe a jikin rigar masu daukan ido suka dan sitirta shape dinta daya fito sosai a jikin rigar suka sake qarawa kyanta da adonta kyau,

Gyalan rigar Maron shima akai rolling akanta Ana rufe gashinta mai tsayi daya qarawa kwalliyanta kyau kafin aka saka sarkoki da chains na zinari akaiwa rolling din nasa adon gaske me Kyau kafin aka saka babban transparent mayafin Kayan still mai tsayi sosai haryana ja da qasa aka Dora Akanta aka rufe rabin fuskarta da babu Wanda ya isa ya gani shima akai masa nasa adon da chains na zinari take ta fito tamkar macen da aka saka golden biro aka zana dan kuwa komai nata daukan hankali d jan hankali yakeyi.

Tenya Jin tayi duniyarta ta sake haskaka da farin ciki suka fito da ita a daidai lokacinda zaa fara tana dauke da NUAB a hannunta.

A bisa dolen al’adah sai matansa sun fito sune zasu tarbesa su rakota a tare har inda yake dan haka koda akai sanarwar isowanta kofar fadar tareda bayinta da securities din dake tsare da NUAB da jakadiyarta take HAILE ta Hadiye wani kakkarfan busashen yawun daya saka hannunta rawa tana yagar fatar Dayan hannun nata da karfi yana yagewa,

Cikin sauri da basarwa Aslam dake kusa da ita ta Dora hannunta Akan hannun mahaifiyar tata tareda dan kallanta a natse tana girgiza mata Kai kada kowa ya gani.

MARAKI ma dagowa tayi zuciyarta na daukan Wani irin nauyin zazzafan kishi mai tsananin ciwo da dumama jini ta zubawa AYANAH GHAZ idanuwanta tana kallan Wani irin fitinannen sirrin kyau daya saka kusan koina tsit sbd duk da tana rufe amma gyalan yayi shara shara din da babu abinda basa gani na halittar da Allah ya qera a gurin,

Akan sultan MARAKI da HAILE suka sauke kallansu a lokaci daya zuciyoyinsu na shiga wani nannauyan kishin da babu wadda batajin kaman ta Hadiye zuciya a lokacin ta mace.

Wani irin kallo ya dago fararen idanuwansa masu kyau da girgiza dan Adam ya saukewa AYANAH GHAZ daga lokacinda ta sako kafa a cikin fadar batareda ya kyafta ba dan kuwa duniya biyu ne aka hade masa guri guda a gabansa ita da NUAB datake rungume dashi suna tinkaro sa.

Yan jarida da televisionsa da duk wani dan media suna gefe daya da aka ware musu sbd tsari da Kyan fadar daga can suke daukan hotinan da flashers kawai ake gani tana haskowa babu kakkautawa.

Haile da maraki ne suka iso gefenta kowacensu da adonta mai kyau da tsari tareda daukan ido itama suka fara tako wa tareda da ita dukansu idanuwansu Akan sultan ta cikin nasu rufar Ayanah kuwa kanta a qasa shi kuwa nasa idanuwan Akan ‘dansa dake hannun Ayanah kawai yake kalla taqaita kallansa daga gareta hana kishinsu Kai illa ga zukatansu.

Isowan AYANAH GHAZ gabansa suka zauna inda aka tanada dan zamanta da nasu take aka fara gabatar da kosher din Wanda yake tamkar daurin aurensu ne zaayi.

Dukiyar kosher datake tamkar sadaki aka gabatar daga jinin BOYEM na manyan cousins din sultan dake qasashe daban daban suna rayuwar mulki da daula tareda hutawa a qasashen turai daban daban dayake dik jinin BOYEM indai suna raye ko a ina kake Ka Halarta dan haka masarautar take shaqe da masu duniya a hannunsu.

Irin dukiyar da aka bayar ya saka masarautar jijjiga take aka karba dukiya aka bawa jakadiyarta sbd itace gatanta wadda kadai take da ita aka fara adduar kosher din tsawon lokaci kafin aka rufe da Amin Wanda Amonsa sbd yawa ya ringa amsawa har wajen Masarauta.

YUNAR KAREEM ALMAZZ BOYEM Shine babban dan wan mahaifin YASAR Wanda yake Zaune a qasar Kuwait da matarsa daya da Yaya uku sai yaya hudu daga imebētinsa daya dan haka shine ya isar da cika Burikan wishmah guda uku Wanda Kai tsaye budar bakinta idanuwanta a kafe kan NUAB dayake kan kafafunta muryanta na tsananta sanyi da karfin Hali tace Abu na farko datake so shine a yanta bayi dari a cikin bayin dake kurkukun masarautar,
Sai Abu na biyu shine tanason a ‘yanta mata baiwarta daya tak sakinah,
Na ukun shiru tayi zuciyarta na yin Wani irin rauni da sanyi ta dago idanuwanta da sukai ja ta saukesu Akan sultan tace tanason ko tana raye ko baya raye idan NUAB ya girma kada a tirsasata hawa mulkin Masarautar BOYEM matiqar baida raayi idan ba shine yayi raayi ya hau dan raayin Saba.

Tsit kowa yayi koina ya dauki Wani irin shiru mamaki na kashe kowa musamman sultan da HAILE da Wani irin sanyi a Karan farko ya dan ratsa zuciyarta ta kafe Ayanah din da ido tana mata kallan mahaukaciyar data rasa tinaninta dan kuwa batada labarin cewa tinda ta fada wannan burin saiya cika koda zata mutu Akan sauya hakan,
Tayaya zata ce idan danta baida raayi kada a basa mulki?
Ta kuwa san menene samun mulkin Masarautar BOYEM?

Sultan kuwa kafeta yayi da idanuwansa Wani irin daci mai karfi yana Sosa zuciyarsa dan kuwa tamkar Kai tsaye ta kallesa ta yaga burinsa daya kullata koda zai mutu ne ta yaga a gaban idonsa,

A matsayin datake dashi harta isa samun wannan tinanin?
Menene nufinta na fara lalata burinsa Akan dansa tin yanzu?
Tabbas tayiwa burinsa na shekara da shekaru tabon da har abada bazai goge ba musamman idan abinda ta fada din ya tabbata.

Manyan fada dik da shock din da suka shiga take aka sanar babu burinta da baama gama cika wa dan haka take aka bada umarnin a saki bayi dari biyu ma da suke kurkukun,

Sakinah ma take aka yantata tareda kyauta me tarin yawan data saka Ayanaah din rufe idanuwanta ahankali hawaye masu dumi na gangaro mata sbd samarwa sakinah yancin da sukam bazasu samu ba har abada.

Har tsakar dare sosai Ana hidimar sai kusan gap da asuba aka gama kowa ya watse zuwa masaukinsa.

Washe gari da sassafe aka saki bayin da akace a saki,
Koda aka fara fitowa dasu tenya na bakin kurkukun dan cika sabon aikin daya hau kanta na hadawa mai girma YUNAR BOYEM sabuwar imebeti a matsayin tukuicin dukiyar kosher daya bayar ta wishmah daga mai girma sultan YASAR,

Tin farko tasan daman zaa bada tukuicin imebeti ga duk Wanda ya bada dukiyar kosher din wishmah a matsayin tukuici Shiyasa ta fadawa Ayanaah sadaukar da zatai na rabuwa da Zuhrah har abada sbd ita zata bayar dan hakanne zaisa itama ta samu rayuwar da har zata haifa nata yayan amma sun yafe juna kenan har abada sbd daga ranar da aka gane jininsu daya duka su biyun zasu rayuwarsu matiqar ba yayansu sunyi girman da zasu sassauta musu hukuncin hakan ba kuma a yanzu Ayanah ta yadda da hakan matiqar zasu rayu Zuhrah ta Gina tata rayuwar harma zuriar kanta,

Hakanne ya saka tenya take tsaye a lokacinda aka fito da Zuhrah wadda ta fita kamanninta gabaki daya Kai tsaye gurin duba lafiyarta tasaka aka wuce mata da ita dan shiri da gyaran gaggawa zaa fara yi mata na tsawon wata daya cif kafin a Kai masa ita ya wuce da ita qasar kuwait.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee

44
A daidai lokacinda Zuhrah ta sako kafarta wajen kurkukun fata shafe Sheka daya da watanni a ciki a daidai wannan lokacin Ayanah ghaz datake tsaye zuciyarta na Wani irin harbawa da Wani irin zallan kewar datake ratsa ruhi da zuciyarta kafafunta na dan rawa tanaji a jikinta Zuhrah na cikin halinda itama take tsananin son ganint su shaqar da rahamar ganinsu.

Sakinah dake tsaye gefen Ayanah din itama zuciyarta cike take da yanayi na sanyi da mutuwar jiki tareda tsananin so da kaunar ganin Zuhrah wadda shikenan wannan Karan sun rasa juna kenan da gaske har abada.

Tenya ma dake tsaye wajen kofar kurkukun zubawa Zuhrah idanuwanta tayi babu kyaftawa tana Jin tsananin tausayin Ayanah da zata iya rasa ranta idan taga Zuhrah a halinda take ciki daidai wannan lokacin.

Barin sukai da zuhran wadda bata iya Miqewa qyam tsaye sbd yunwa da wahala hakama fatarta tayi duhu gabaki daya ga gashinta duk ya zama abin tsoro da qyama,

Suna barin gurin tenya ta aika baiwa ta isarwa da wishmah sakon Zuhrah ta fito kurkukun da babu komawa insha Allah har karshen rayuwarta.

Sakon yana isowa wishmah Lumshe idanuwanta tayi ahankali tareda silalewa qasa tana bin bango ta zube qasa tana bude idanuwanta Akan sakinah data riqeta tanason magana ta kasa sai kawai ta sake rufe idanunwata tana dora hannunta daya Akan kirjinta dake mata radadin azabar da har abada bazai dena ba sai ranar da ranta yabar jikinta dan kuwa baqin ciki ne da quncin da baida magani.
Chapter 48 · 0% Book details