← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 76

Sashe 6

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihun da kukan Neman agaji da ceto mutane suka fara Wanda ya saka gabaki daya garin daukan hayaniyan Data saka kowa fitowa Ana gudun Neman ceto sedai yawa da karfin da kusrawan ke dashi ya saka munin lamarin yayi yawan da komai ya lalace.

Kukan kananun yara dana mata da dabbobi ma dake gudun cetan rayuwansu ne yake gauraye gari da dajin ANJOM dayake amsa wa cikin sauti mara dadi da karya zuciya tareda tsananin tausayi.

Wuta kuwa haka take cin wasu mutane harma da dabbobi sbd gobara sosai garin ya dauka kowane gida sakawa wuta sukeyi sbd kada ma mutane su samu gurin boye dan haka komai ya zama tashin hankali mara misali lokaci daya.

GHAZ da fadawansa da askarawansa koda suka fito dan bada ceto ga jamaar gari lamarin ya gama munanar da babu abinda zasu iya sbd Angama cinye garin ANJOM da wuta da jinin mutane dan haka take suka fara cetan wainda zasu iya cikin azabar wuta da tashin hankalin munin gawawwakin mutane da suke tsallakewa da takawa.
#MAMUH
#ROYALTY
#SLAVERY
#BEST LOVE

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070

6

*_PRIME SCENT_*
08103155915
Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa?
Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents?
Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites?
Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa?
Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT
Duniyar kamshin da babu kamarsa,
Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba,
PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu.
08103155915
********

**********
Wani irin zufane yake jiqa Dukkaninsu zuciyoyinsu kaman zasu fado sbd munin tashin hankalin dasuke ciki,

Cikin duhun hasken wutar daya kusa cinyewa Ammah ta dago Idanuwanta da sukai jajir da hawaye masu karya zuciya ta kalli Ayanah kafin ta maida kallanta kan Sauran ‘yayan daya bayan tana hana hawayenta saukowa fuskanta sbd zuciyoyinsu duka a karya suke batason qarasa karyasu gabaki daya.

Juya kanta tayi ta kalli kofar dakin zuciyarta na kasa jurewa ta juyo ta sake kallan Ayanah wadda tayi saurin riqeta cikin mummunan tashin hankali ta bude baki da wata irin murya mara karfi cikin yarensu tace

‘Aāyi Amma, ātadirigi Amma, dan Allah Amma karkiyi hakan, āyi Amma.’

Hawayen da Amman ke riqewa ne suka gangaro cikin tsananin karyewan zuciya ta kalli Ayanah din tace

‘Ayanah dole zan dubosa sbd da hakan zamu tsira gabaki dayanmu’

Wani irin rikitaccen kukan tashin hankali me tsanani Ayanah ta sake tana rintse idanuwanta tareda sake qanqame hannun Amman tana girgiza akai ko magana ta kasa,

Nurat datake qame tin Bayan biyar Abaansu riqe hannun Amman daya tayi Tana girgiza kai itama hawaye masu tsananin zafi na gangarowa daga idanuwanta.

Abaas dake rungume dashi da Zuhrah saurin fadawa jikin Amman yayi ya rungumeta shima dukkanin jikinsa na rawa yace

‘Amma babu inda zaki tafi’

A rufe murya na rawa Zuhrah tace

‘Abaa ya tafi zai dawo Amma mu jirasa dan Allah karki tafi,
Idan kin tafi zan biki mu dubosa tare’

Turesu tayi daga jikinta tana kasa kallan kowannesu tace

‘Ku jira zan dawo,
Ayanah ki kula dasu karki Bari kowa ya biyo koda ban gansa ba zan dawo’

Sake riqeta Ayanah tayi Tana girgiza kai hannunta na rawa sosai muryanta na sake mutuwa kukanta na bayyana tace

‘Amma bazan iya ba dan Allah karki fita,
Amma bazan iya ba,
Āyi Amma dan Allah’

Zare hannu Amman tayi tace

‘Ayanah zaki iya yanzu fa zan dawo,
Nima idan na dade ku tafi kawai zamu taho daga baya ni dashi mu sameku acan
Kawai ki tabbatarda kin kula dasu sbd kece uwa a cikinsu kinji?’

Kasa cewa komai Ayanah din tayi kukanta na qaruwa tana girgiza kai jikinta na rawa sosai,

Su Zuhrah ma kuka sukeyi sosai suna qanqame Amman hankalinsu a tsananin tashe tsoronsu na sake bayyana.

Sake daukan Ihun tashin hankali da tsananin tsoro garin ke dauka hakama wuta tako ina Wanda ya saka Amman kasa riqe kanta sbd tana buqatan janyo GHAZ subar garin dan kuwa ba lallai su tsira ba hakan kawai ya hakura su tafi kawai dan tseratar da ahalinsu.

Tsoronta cirewa yayi tana Jin tsananin buqatan dawowansa su bar garin ta qwace daga riqon da yayanta sukai mata ta fice tareda janyo kofar da sauri ta rufe tana cewa bayin dake ciki tareda su suriqe su karsu Bari kowa ya fito.

Kai tsaye Amman na fitowa gidan taga masifar fata saka kafafunta daukan wata irin rawar tsoro da firgici zuciyarta na Neman bugawa da sauri ta dafa bango sbd jirin daya debeta na ganin wuta koina da jini kaman bana mutane ba.

Bangon dafa jini ne taji a tafin hannunta da sauri ta janye hannunta jikinta na sake daukan rawa.

Juyawa tafara yi kafafunta na Neman kasa daukanta tafara baza ido Tana kwada kiran GHAZ Wanda bazai taba jinta ba koda yana kusa sbd karfi da qarar wuta da Ihun mutane da gurnanin rayukan da basu gama fita kirjin mutane ba,

Taku kadan tayi Tana kutsa hanyar da mutane ke fitowa suna gudu baa hayyacinsu ba Ana ture juna,

Bata ganin komai sai hayaqi da tsananin hasken wuta dake Kama mutane Tana kashe idanuwanta ga wani irin Zafin azabar da basu taba Ji ba dan haka ja da baya ta fara Tana wani irin Ihun kiran GHAZ.

Gadan gadan kusrawa sukayo bangaren suna sarar mutane tako ina Ana gudu da Ihun mafi munin tashin hankali.

Bude baki tayi Tana sake yin baya da sauri Tana kokarin ambatar GHAZ data hango yana fitowa gurin da gudun shima dauke da wasu yara qananu guda biyu duka mata
Bude bakinta batareda maganarta takai ga fita ba wani irin mashi mai tsinin gaske ya keta wuyanta ya shiga makoshinta ya fita ta baya.

Cak GHAZ daya kawo daf da ita ya tsaya yana cin wani irin birki idanuwansa a kafe sbd mummunan tashin hankali da firgici mafi munin rayuwansa.

Sakin yaran hannunsa yayi yana tarota da sauri ta fado jikinsa babu rai idanuwanta a bude…..

Jininta ne ya fara gangarowa daga wuyanta zuwa tafukan hannunsa dake tallafe da ita,

Mummunan rawa dukkanin jikinsa keyi daya kasa riqeta din ta zame daga jikinsa.

Rufewa idanuwansa sukai baya gani amma a hakan ya miqe ya sunkuceta ya Dora a kafadarsa ya Kama hannuwan yaran da hannunsa daya suka bar gurin da wani irin mummunan tashin hankali sbd gari kam an gama cinyesa wutar ta kawo gurin su sosai dan haka yake tsananta gudu.

Gida ya nufa da tsananin tashin hankali sabo sbd dai dole yabar garin da yayansa sbd kowane lokaci zaa iya kashe su ko kamawa sbd wutar harta fara shigowa gidan nasa sosai.

Yana shigowa ajiye gawar Amma yayi daga gefen dakin ya fizge rigarsa ta sama me dan kaurin saqi ya rufeta da ita.

Ihun shigowan mutane dake Neman hanyar tsira ne da Ihun wainda wuta ke ci ne ta cike gidan nasa dan haka da gaggawa idanuwansa jajir fuskansa duk jinin Amma daya dauko koina ya bata fuskansa hakama hannuwansa da jikinsa koina jini ne.

Tura kofar dakin yayi da karfi Wanda ya saka dukkaninsu miqewa tsaye cikin tsananin firgici da tsoro,

Nurat ce ta fara cewa ‘ABAA’ cikin mummunan tashin hankali Tana nufosa da gudun gaske ta fada jikinsa.

Abaas ya miqawa hannu ya Kama ya janyosa hakama Zuhrah koina jikinta wani irin mazari ya dauka ta fara ja da baya tana fita hayyacinta,

Ayanah ma jinin jikinsa da fuskansa take kallo Tana kasa hawaye ma sai rawan jiki da jajayen ido,

Fizgo Zuhrah Abaa din yayi yana cewa Ayanah

‘Muje,ku fita da sauri,Kuyi sauri ba lokaci’

Daqyar Ayanah ta iya bude bakinta daya bushe qayau sbd masifar tashin hankali tace

‘Abaa Amma bata nan,taje nemanka,
Ina zamu ba tareda ta dawo ba?

Qin kallanta Abaan yayi ya Kamo hannunta itama da karfi ya fito dasu Sauran mutanen da zasu samu kubuta tareda su suna biye dasu.

Nurat dake da kokarin wucewa kaman ance ta juya idanuwanta suka sauka akan gawar Amma dake shimfide fuskanta kawai ne a rufe abin hannunta ta gane take ta tsaya cak tareda cewa ‘AMMA’ cikin wani irin sanyi da mutuwan jikin kasa yadda.

Ayanah ce ta kalli gurin da sauri itama Tana Jin jininta na Neman kafewa,

Abaas ne ya kwace daga riqon mahaifinsa ya nufi gurin da gudun gaske yana isa ya yaye rufar take ya some a gurin,

Nurat ma silalewa tayi a gurin some sbd kasa dauka da zuciyar su tayi

Ayanah ma salalewa qasa tayi zuciyarta na Neman bugawa ganinta yana disashewa Abaa yayi saurin dagota da karfin gaske shima zuciyarsa radadin gaske take kaman zata Dena bugawa amma sbd su bazai iya karyewa a lokacin ba sbd kubutar da rayuwarsu daga garin,

Girgizata yayi da karfi tareda ambatar sunanta yana danne abinda yake Ji a kirjinsa na bugawan zuciyan dayake kokarin samu yace

‘Ayanah karki karye ke uwa ce a yanxu da babu Amma,
Kece zaki zama garkuwan yan uwanki,
Kece Amma yanzu,
Kece madubi fitilar da zata haske hanyar da rayuwanku zatabi,
Karki karye kiyi jarumta ba yanzune lokacin kukan rashin Amma ba,
Ki dake zuciyarki ki kubutar da yan uwanki daga nan Allah ya Riga ya karbi Amma karki Bari burinta na kubutar da rayuwanku ya tashi a banza.’

Wata irin jijjiga jikin Ayanah keyi taba girgiza kai kuka me tsananin gaske na zuwar mata tace

‘Abaa bazan iya ba,
Abaa ina buqatan kai da Amma a gurin zamtowa uwa garesu,
Abaa kune hasken rayuwanmu,kune garkuwanmu,
Abaa kune rayuwarmu tayaya zan iya babu dayanku?’
Chapter 6 · 0% Book details