← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 76

Sashe 4

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kama hannunta Abaas din yayi cikin kulawa yana sake nasa murmushin me kyau daya qawata tasa fuskar dasuke tsananin Kama dan shi Kansa kyakkyawa ne da ake fadarsa a garin ANJOM Wanda lokuta da dama iyayensa ke tinanin bakin mutane ne ya saka ya kasance me rauni.
#MAMUH
#ANJOM GHAZ
#AYANAH GHAZ
#ABAAS GHAZ
#BOYEM
#BEST ROYALTY/BEST LOVE/BEST ROMANCE

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070

4
Zaunawa Ayanah tayi gefen dan uwanta tana kallansa Fuska cike da murmushi da sakewa tace

‘Godia nake GHAZ Abaas’

Dariya yayi yana sake hannunta yana cewa

‘Ayanaah….

Katsesa Zuhrah tayi batareda ta Bari ya fara fadar maganarsa da ako Yaushe take ta yanda yake Jin bazai iya rayuwa ba Ayanah bane wadda koyaushe damuwansa wani lokacin ta yanda zatai sure wata ran ta tafi tabarsu.

Dariya dukkaninsu sukai ganin yanda ya juya ya harari zuhrah cikeda kauna itama sbd yanda ta katsesa da cewan sun gaji da maganarsa daya kullum.

Fararen idanuwan Ayanah ta juyo ta sauke Akan fuskan mahaifiyarsu dake Zaune Nurat na kwance jikinta ta bude baki tace

‘Amma Barka da hutawa,kin tashi Lfy?’

Hannu Amman ta miqa ta Shafa fuskan Ayanah din tana Jin tsananin son yarta tace

‘Barka Ayanah ghaz,kin tashi Lfy kema’

Murmushi tayi tana dan Dora tafin hannunta Akan hannun Amman dake kan Fuskanta tana Jin kaman ta hadiye tace

‘Lafiya kalau Amma’

Juya wa tayi tana kallan zuhrah tace

‘Ki Dena damar mun da GHAZ Abaas sbd baya buqatan gorinki tareda dashi zan tafi duk inda zani kokuma na zabi zama a cikin ahalina har karshen rayuwata’

Nurat Baro jikin Amma tayi ta dawo gefen Ayanah ta lafe jikinta tana Jin kaman ma hakan ya kasance a rayuwar su kada suyi aure su rabu su tabbata a tare har abada
Bude baki tayi tana kallan Ayanah data kalleta cikin sanyi tace

‘Ayanah inason na tabbata tareda ku duka mu tsufa mu mutu tare banason ko aure ya rabamu,
Zan cewa Abaa(mahaifinsu) koda zamuyi aure abarmu da mazajenmu muyi rayuwa a cikin GHAZ batareda munje kowane gida aure ba’

Wani iri Ayanah taji a zuciyarta na Ina ma hakan zata kasance datafi kowa farin ciki sbd yan uwanta sune rayuwarta amma kuma kaman hakan bazai yiyu ba,

Numfashi ta sauke tareda Kai bakinta cikin kauna ta sumbaci tsakiyar kan Nurat din tana Shafa gefen fuskanta tace

‘Nurat babu abinda zai raba mu a duniyar nan Bayan mutuwa sbd kune rayuwata’

Amma datake Jin kaman kada ta taba aurar ‘yayan nata sbd ganin baza su iya kowace rayuwa batareda junansu ba wani irin sanyi jikinta yayi ta Kama hannun Ayanah takai bakinta ta sumbata tana kallanta tace

‘Kece rayuwansu suma musamman a lokacinda zaku samu Kanku ba iyaye idan tsufa ko mutuwa tazo dan haka Ayanah kici gaba da zama uwa kaman yanda kike kaman mahaifiyarsu a yanzu’

Qurawa Amman idanuwa Ayanah tai tana Jin zuciyarta na sake cika da tsananin kaunar mahaifiyata,

Gyada Kai tayi tana kwantawa jikin Amman batareda ta iya cewa komaiba.

Abaas ne dayake Jin a jikinsa shikam da Ayanah baza su taba rabewa ba koda basa a raye sai yana Jin kaman baza su rabu ba dan kuwa tsananin so da kaunar dayake wa Ayanah da aure ya Halasta a tsakanin yan uwa to da bazai taba barin kowa ya dauke masa Yar uwa ba zata zauna a karkashinsa koda ba aure zai killaceta ya Hana kowa koda ganinta sbd kada kowane ido yayi mata illa,

Duk da ba aure tsakaninsu yanada Alkawari da fatar duka yayan dazai haifa a rayuwarsa su hada jini Ayanarsa,
idan kuma mace Allah zai basa to adduarsa koyaushe a cikin ibadarsa shine ta kasance tamkar Ayanarsa koda hakan shine burinsa na karshe yana fatar Allah ya cika masa shi koda a ranar mutuwarsa ce.

Asamah da dukkanin jikinta yayi tsananin sanyi da kaunar ahalin GHAZ din da baka gane wane yafi wani kaunar dan uwansa Jin takeyi Inama nata ahalin sunanan da yayanta zasu yi girman su zuhrah da Abaas sbd itama ‘yaya mata biyu ne da ita sai namiji daya kaman Abaas,

Hawayene masu tsananin zafi da radadi suka ciko idanuwanta ‘dacin rashinsu na taso mata Wanda daman a tsawon shekarun nan bata taba manta radadin ba koda na qanqanin lokaci ba,

Hadiye hawayenta tayi sbd kada su bayyana a gabansu.

Juya wa tayi Bayan ta gama jere komai ta kalli kakkaifar qaramar wuqar dake kan Kayan da zata bar gurin dasu ta yanka Kayan marmarin taga yanda take daukan ido,

Zuciyarta ce tahau Kai kawo cikin tsananin qunci da baqin cikin daya taso mata na rashin yayanta da tsananin buqatar son dawowan mijinta gareta Wanda zuwa yanzu tasan azaba ta dade da sauyasa zuwa wata mummunan halittar amma tanason abinda a hakan.

Shedan da zuciyarta dake rufewa idan abin ya taso mata Wanda yake tamkar tabin kwakwalwa batareda sanin kowaba suka saka zuciyarta rufewa tafara taku daya na biyun ta saki gabaki daya Kayan hannunta a jikin Abaas Wanda wuqar ta yanki gefen qafarsa take jini ya fara fito wa Wanda ya saka dukkaninsu miqewa cikin tsananin tashin hankali da damuwa

Asamah ma cikin tashin hankalin da tsoro me tsanani ta zube gabansa tareda rigan kowa saka hannunta a kafarsa tana wani irin rawar jiki da kukan dayake fito wa daga qasan ranta tana basa hakuri cikin kulawa sbd a qasan ranta tasan kofar wata rayuwar ce zata bude wa duk Wanda yake garin ANJOM wadda bata San wace iri bace dan kuwa a gefen rigar jikinta ta goga jinin me yawa daga qafar Abaas batareda lurar kowa ba.

Cikin sauri sakon fitar jini a jikin GHAZ Abaas ya isarwa Abaa dinsu wanda ba bata lokaci ya iso gurin Wanda ya saka duk Sauran bayin dake zagaye da gurin na kowannensu dake rumfar ja baya sosai cikin girmamawa.

Wuqar da jininsa ya taba ya fara bada umarnin a karba hakama take aka kawo ruwa masu yawa a babbar tasa me kyau aka saka Asamah wanke duka hannuwanta da jinin Abaas ya taba kafin take GHAZ Ali din da Kansa yasa aka kawo magani ya karba yana kallan Abaas din Wanda hankalinsa yake son tashi sbd fitar jininsu tamkar hadari ne ga dukkanin ANJOM gabaki daya sbd da jininsu ne kadai ake iya karya komai dake ANJOM dan haka Sam baa taba yadda da kowa ba game da duk wani digon jinin GHAZ.
Amma ganin Asamah ce ta raunanasa bada ganganba kuma tamkar ahali take sai hakan na hana zuciyarsa shiga tashin hankali da tsoro sosai.

Kukan da Asamah ke yi ya saka Ayanah rarrashinta tareda Zuhrah

Nurat da Amma kuwa suna jikin Abaas din cikeda damuwa suna kallan yanda GHAZ ya saka masa garin maganin da take jininsa ya tsaya ya Dena zuba.

Ajiyan zuciya GHAZ ya sauke yana dagowa ya kalli Abaas din cikeda kulawa da qara tabbatar masa da tsananin mahimmancin jinin dayake yawo a jikinsu.

Cikin nutsuwar mulkin dayake yawo jikinsa da kulawa tareda tabbatarda kiyayewa GHAZ ya bude baki yace

‘GHAZ Abaas ya koma dakinsa a tabbatarda an kiyaye danyen yankan kafarsa ta warke da kyau batareda ya sake fitowa ba’

Gyada Kai kowa yayi suna amsa wa da cewa

‘Angama’

Juya wa yayi ya bar gurin kowa yayi tsit cikeda damuwa da alhini har saida ya fice kwata kwata kafin Abaas din ya dago ya kalli Asamah kaman zai yi magana sai bai ce komaiba ya maida idanuwansa Akan Ammansa dake miqewa tabar gurin tana bin Bayan GHAZ Ayanah kuma hannu ta miqa masa ya Kama ya miqe suka nufi hanyar dakinsa tana cewa

‘Yankan qaramar wuqar cin tufa bazata girgiza jarumin anjom ba GHAZ din anjom me zuwa’

Yar dariya yayi yana kallan kafar tasa tareda cewa

‘Shekarun nawa basu Kai ba ai tukuna amma insha Allah idan nakai shekaru ashirin a duniya zan fara fita a matsayin jarumin na anjom wata ran harma na zama Garkuwa ga dukkaninku’

Har cikin ranta taji dadin abinda ya fada tana fatan hakan koda kuwa a mafarki ne.

Rakasa tayi dakinsa Wanda acan suka zauna ta tayasa fira sai ga su Zuhrah da Nurat sun taho suma sbd sunsan saiya kwana biyu kafin ya fito koina sbd tsaro da dokar GHAZ din tin asali duk Wanda yake jinin GHAZ yaji rauni har jininsa ya fita to saiya kwana biyu a killace batareda fito wa koina ba sai Raunin ya qame,

Hakan ne ya saka yan uwansa zuwa dan tayasa fira da debe kewa,

Kayan ciye ciye da dafaffiyar madarar raqumi me dumi aka kawo aka ajiya musu sunata firarsu da hutawarsu cikin kwanciyan hankali da nishadin farin cikin kansacewa da juna,

Anan suka wuni dan hatta ibadarsu anan sukayita,

Da yamma ma mahaifinsu shigowa yayi cikinsu cikeda Shakuwa da kaunar juna suka cigaba da farin cikinsu anan cikinsu yayi sallah tareda iyalansa har cikin dare tukuna dukkaninsu suka watse kowa ya nufi makwancinsa.

Ayanah na isa dakinta zare Kayan jikinta tayi ahankali tana rufe jikinta duka ruf da wata kakkaurar doguwar rigar wanka me Kama da alkyabba amma ita ta yadin saka me kyau.

Baiwarta Sakina ce take biye da ita dauke da wutar haskawa.

Gurin wankansu ta Nufa Wanda yake cike da ruwa masu tsafta da kullum ake sauyawa ta zare rigar tana zaunawa gaban ruwan tafara wanka a natse.

Sakina ajiye mata hasken tayi ta koma kofa ta tsaya daga waje tana jiran fitowarta.

Gama wankan tayi ta fito tana qamshin madarar flower me dadi.

Dakinta ta shiga ta zauna Sakina tana tayata goge jikknta harta gama ta shirya ta nufi lafiyayyan gadonta na sarauta ta haye.

Washe gari ma haka suka wuni gurin Abaas tareda iyayensu Wanda kwata kwata GHAZ ayau din bai fita koina ba yana cikin yayansa tausayin Abaas haka kawai yake shige masa zuciya sbd ganin kaman zuciyarsa tayi sanyin da bazai iya mulki ba idan ma yayi wahala zaisha sosai,

Akan ‘yayansa mata ya maida idanuwansa yana kallan yanda suke dariya suna Wasagu da juna sautin dariyarsu na shiga kunnuwansa zuciyarsa na na cikewa da tsananin kaunarsu yanajin kaman ya maidasu cikin Mahaifiyarsu sbd basu tsaro da kariya daga dukkanin wata cutar duniya da wahala.
Chapter 4 · 0% Book details