← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 76

Sashe 44

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take kowa ya maimaita sunan suna saka masa albarka tareda addua duk da baaji shauqin na ratsa jini da kwakwalwaba kaman farkon amma shima sunyi Murna sosai da kasancewansa sabon prince din boyem hakama yau rana ce mafi girma da tarihi tinda aka haifar musu jaruman babys biyu a daya rana.

Kyauta da tukuici aka fara fiddawa Ana bawa fetto itama sedai kasancewan baa San da haihuwan ba bata samu kyauta irin wadda tenya ta samu ba sultan kuwa kyautarsa da tukuicin sa daidai iri daya yayi da wadda yayiwa NU’AB,

Cikin karfin Hali da dake wani zuciya fetto ta karbi ASIM tareda dagasa tayi masa kikarin daya saka kowa yin tsit dan kuwa Kai tsaye da asalin magajin sarki ta kirasa bayan sultan ya riga ya Ambaci NUAB da magajin BOYEM.

Dagowa sultan yayi da fararen idanuwansa da sukai wani haske da kwarjini sbd yanayin dayake ciki a yau din zai kalli fetto sbd lokacin data fada cewan an haifi ASIM ALMAZZ tabbas kenan ya riga NUAB fadowa duniya sedai kuma NUAB ne Wanda ya fara shiga hannuwansa,
NUAB ne Wanda ya fara cike zuciyarsa da yanayin dabai taba shiga ba na samun magaji,
NUAB ne Wanda labarin haihuwansa ya fara ratsa kunnuwansa da kunnuwan duk Wanda yake BOYEM da zagayenta,
NUAB shine Wanda ya fara dagawa duniya ya ambacesa da LEUL BOYEM…..

Ganin tinanin da sultan yayi shiga Akan tsakanin ‘yaya biyun waye magajin gasken ya tenya zubewa qasa da Wani irin saurin gaske tana daga NUAB da ladabin gaske ta bude Baki tace

‘Allah ya qarawa jini da ruhinka tsarki sultan me BOYEM uban LEUL BOYEM,uban magajin BOYEM,uban NUAB ALMAZZ Zakin boyem,

Ayau magajinka daya ne da duniya zata sani wato Wanda ya fara haskaka zuciyarka da hasken da aka dade Ana jira,
Li’ul ASIM zakinmu ne shima da babu tamkar sa,
Shi din haske ne dazai haske masarautarmu da Zuwan LEUL NUAB ya fara haska mana,
Jini daya ne yake gudana a jikinsu biyun Wanda yake asalin jinin boyem me tsarki da karfin iko da adalci,

A tarihin boyem mai daraja data kafu Wanda ina saka ran jakadiya fetto ta manta dashi shine……..

Kaman daga sama aka rangado sanarwar isowan Queen Haile da kanta.

Gabaki daya duk namijin dayake fatar qasa yayi da idanunwansa cikeda girmamawa da bin al’adar Qin sauke ido ga mace me daraja a BOYEM wato uwargidan sultan YASAR BOYEM.

Bayi da fadanni kuwa qasa suka zube a lokaci guda gabaki dayansu suna qasa da kansu.

Aslam da Meryam ne ‘yayanta biyu suke tareda ita a gefe da gefenta tana tsakiyar su Akan kujera me kyau dr na turota.

Aslam da meryam sanye suke cikin shigar sarautarsu dogayen riguna masu tsananin kyau da suka dan Kama daga sama suka baje sosai daga qasan har suna dan ja da qasa koina na jikin Kayan qyallin stones da bead harma crystal sukeyi,

Aslam dark purple ce a jikinta sai meryam kuma black kowacensu da qaramar rufa a kanta zuwa saman idanuwansu dan basa bude fuskokinsu sosai a bainar mutane dan ba kowane yakeda iko ko damar ganin fuskokinsu masu daraja ba kasancewan su jinin sarautar boyem.

Zuba musu manyan fararen idanuwansa sultan yayi da mamakin zuwansu fada a wannan lokacin batareda ya buqaci hakan ba ya aika musu gayyata dan kuwa kowa yasan iyalan sarautar a killace ganinsu tamkar wata qaramar haramun ne, amma ganin halinda HAILE take ciki da kuma abinda yake gabansu na waye magajinsa ya sakasa kallansu a natse cikeda iko dayake yawo a jininsa ya tsayar da kallansa kan Haile da tana farfadowa kasa nutsuwa tayi Jin takeyi kaman zata rasa ranta sbd tafarfasa da qunar dayake komai baya iya gani daidai sbd asalin baqin cikin daya gauraye kowane jini dake zagayawa cikin jijiyoyin jikinta da zuciyarta dan haka idan bata iso ba bazata ita ji tana gani ba a bawa ‘dan imebeti sunan magajin qasar boyem ba dan kuwa sunansa matacce har shi har uwar tasa dan kuwa bazata taba sauke Numfashi da shaqar iska me albarka ba matiqar ba ganin sun bar duniya tayi ba dan kuwa karshen tozarci ne a gareta macen da ake ganin yafi kowace mace daraja a qasar ace rana tsaka sultan yayi wishmah wadda hakan na nuna alamar SO ne kuma duniya zata sani gabaki daya hakama shikenan matsayinsu daya cif da ita.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

40
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291

*******
Duk yanda yayanta da dr suka nuna kulawa da kaunarsu sosai akanta ta hanyar hanata zuwan hakan Sam bai samu ba dan kuwa ta gwammaci ta mutu a hanyar zuwa tasan tayi kokarin isa ranta ya bar jikinta Akan tana kwance a bawa ‘dan mistress matsayin ‘danta da babu kalar shirkar da bataiba akansa da kisa,

Itama doguwar riga me adon gaske ce a jikinta da kawai aka goge jikinta ya sanyo sai mayafi mai adon sarka data Zaune a fuskarta ta rufe rabin fuskarta,

Cikin nutsuwa da kamewa tareda iko mai tsanani daya sirka da kulawa ya kalleta ya bude baki da zallan mulki yace

‘Ina taya queen HAILE murnar haifowa boyem sanyin idaniya jarumin boyem kuma jinin me boyem ina miki fatan samun lafiya da wadattacen farin ciki me dorewa,
Wane irin tukuici kike buqata daya kawo ki da kansa?.

Ajiyan zuciya me zafi mara sauti dake sake yunquro da mummunan baqin cikin datake ciki ta sauke a cikin mayafinta kafin ta bude Baki a hankali tana Hana tsananin weak din datai sbd azabar data sha kuma take ciki bayyana cikin sautin dazai isa kunnuwan manyan fadar dake fadar suma suna cikin tsimayi da mamaki tareda jiran menene yake shirin faruwa dan kuwa tabbas fetto ta fada magana.

‘Allah ya qarawa sultan me boyem tsawon rai da tsarki tareda karfin iko uban LEUL ASIM ALMAZZ magajin boyem,
A tarihi da dokar Masarauta me girman daraja da iko ta boyem ‘dan imebeti bai taba zama magajin LEUL BOYEM ba matiqar a kawai ‘dan da Matar sunnah ta Haifa,
Ayau ni HAILE YASAR BOYEM na haifo jinin sultan YASAR Wanda Koda imebetin sultan ta riga haihuwa to babu ikon danta ya zama LEUL sbd ni Matar sultan na Haihu a qarqashin igiyoyin aure dan haka sultan da manyan masarautar BOYEM duka gakunan a Zaune nake Neman Adalcin bin doka da kaidar BOYEM tin asalin tarihinta a bawa ASIM matsayinsa.’

Tana gama fadar hakan Aslam da meryam suka zube qasa cikeda girmamawa kansu a qasa da sauti me bada girma sosai suka hada Baki suna cewa

‘Allah ya qara maka tsawon rai da lafiya tareda iko ya Abbi me BOYEM muma muna son Ayi adalci ga kowa a bawa me matsayi matsayinsa’

Tsit fadar ta dauka sbd wani girmammen lamari daya ratsa,

Manyan fada kuwa kowa maganarta ta shige sa sbd abinda ta fada haka yake babu gargada babu shakka,

Haile data ga maganarta ta shiga manyan fada wani Numfashi me sanyi da rashin sauti tana Jin sassaucin muguwar azabar datake ji a kirjinta na zallar baqin ciki da tashin hankali hakama abinda ya sa ta zabi maganar anan gaban manyan fada sbd sunada iko me karfi ta wannan bangaren da duk zai shafi goben Masarauta da ikonta da kaidojinta dan haka tasan dole ya yanzu basai gaba ba zaa bawa danta magajin sultan tasan shine tin yanzu me jiran gado.

Sultan idanuwansa ya zubawa HAILE yana ankarewa da abinda tayi din na zuwa fada ta fada adalci take nema wa ‘danta,

Bai taba tinanin zaa fara samun jayayyar matsayin magaji ba da wuri hakan Wanda fara faruwan hakan na nuni ne da zazzafan hadarin da zai biyo Bayan rayuwar mutane da yawa Akan matsayin da rayuwar magajin BOYEM koma wanenen,
Masana sun sanar da duk magadan suka fara jayayyar matsayi a masarautar BOYEM fitina ce da zazzafan hadari yake tafe a cikin Neman mulkin kota yaya dan haka take yaji wani yanayi na tinanin taka tsantsan yabi komai a natse da lissafi dan bada kariya ga Wanda yasan zasu cutu a yaqin mulkin amma ita HAILE a bayyane ya gane me takeson yi na Neman matsayin wa danta ta hanyar ikon manyan fada wainda zasu iya yanke hukuncin waye magajin BOYEM,

Juyar da idanuwansa yayi ga tenya Wadda idanuwanta suke a qasa amma irin riqon datai wa NUAB ba Wanda zata iya shiru bane a bakin rai take da tsayuwa Akan lamarinsa dana uwarsa da batada kowa a duniya tinda baiwa ce da aka saka kudi aka siyo.

Numfashi mai nuna isa da iko ya sauke yana komawa sultan dinsa dan tabbatarda girman matsayin da tenya zata iya zuwa Akan Ayanah ghaz da ‘danta ya bude Baki batareda ya kallo kowa ba idonsa Akan ASIM yace

‘Tabbas Li’ul ASIM ALMAZ BOYEM ‘dan queen Haile Wanda…….

Da karfin gaske cikin tsananin girmamawa tareda gitta rayuwarta tenya tayi saurin daga NUAB tace
Chapter 44 · 0% Book details