← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 76

Sashe 54

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NUAB ALMAZZ ya zamo uban marasa gatan da rayuwarsu ta lalace ne sakamakon Tsintar matashin da aka kashewa uwa da uba da Kanwa aka cinye masa gadonsa duka sbd son zuciya irin ta dangan mahaifinsa sanadin hakan ya fada harkar taaddanci mai karfi a haka aka kamasa aka shiga kotu dashi aka yanke masa shekaru biyar gidan yari tin yana da Sauran kuruciya,

Shekaru biyar yana fitowa gidan yari NUAB ya daukesa ya tsayawa rayuwarsa tsaf saida ya tabbatarda ya samu adalcin daya kamaci iyayens da basa duniya.
#MAMUH
#LEUL BOYEM

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

49
Tin daga wannan lokacinda ALEEY KUAS ya zama babban yaron da babu kamarsa a gurin NU'AB Almazz,
Aleey ya sadaukar da rayuwarsa ga kowane hukuncin NU'AB ALMAZZ da zai iya sadaukar da rayuwarsa ya bada ita batareda kowace irin second tinani ba indai Akan NUAB ne,
NUAB ya Inganta rayuwarsa ta hanyar sakasa ya qarasa karatun da bai qarasa ba ya hada takardunsa ya zama cikakken mutum da ayanzu ilimin sa yake daukan businesses da mahaukanta kudin da bai taba tinanin a rayuwa zai taba iya ko lissafowa a mafarkinsa ba,
Ya tsayu ya kafu a cikin manyan businesses na qasashe daban daban yana tsayuwa a gaban mutanen da bai taba tinanin zai iya ganinsu idan ba a news paper ba ko tv amma a yanzu a gabansa yake ganinsu tareda boss dinsa harma kusan shine yake gabatar da abubuwa da dama na haduwar da businesses din dan haka rayuwarsa tayi Wani hawa da saman da badai masu qananun matsayibama sedai manyan duniya duk ta Sanadin Ubangidansa da ko rai yace ya dauka to tabbas bazai qara mintina biyu batareda ya cika umarnin ba,

Duk abinda NUAB ALMAZZ yake so ko menene shi aleey yake so ba me kyau bane kuwa hakama abinda NUAB ALMAZZ yakeso to aleey yana sonsa da dukkanin rayuwarsa dan hakanne burin Ammi ya zama qudurarren burinsu da dukkanin Wanda yake qarqashinsu na Neman Abaas a duk duniyar dayake koda hakan na nufi zasu juya nahiyoyi da dama.

Tin daga kan aleey NUAB ALMAZZ ya zama gatan kowane mara gatan,

Sama da daruruwan yan taaddan qasashe daban daban da kaddara ta sakasu fadawa taadanci da shaye shaye NUAB ya tallafi rayuwarsu ya sakasu jikinsu ya kawo sauyi a rayuwarsu suka zama Yaransa cikin sauyawa zuwa masu abin yi,

Duk Wanda bai gama karatu a cikinsu yana sakasa ya qarasa karatunsa ya fara aiki a qarqashin sa wainda kuma Sam basuyi karatun ba suma aikin da zasu iya a duniyarsa yake sakasu dan haka kusan duka wainda suke a qarqashinsa ire irensu ne amma kuma ilimin sosai suke samu dayake ratsa su sun zama yan business din gaske da kamar da saa kowannesu yake yawo dan kuwa tako ina cigaban GHAZ empire ake samu,

Tamkar zakuna suke a cikin duniyar manyan business tycoons sbd tsananin ilimi da saarsu harma da qwanjinsu dayake bayyane Akan zasu iya komai akai ubangidansu da ayanzu kusan koina duniya ta sansa sbd tarin yan amanarsa kuma yan taaddansa dan duk da sun sauya rayuwa sun taka matsayin cigaban rayuwa wannan rayuwar ta rashin sauki da rashin tsoro yana nan a tattare dasu,

Ilimi da kudi tareda power da suke samu daga shugabansu NUAB ALMAZ ya qarawa rashin tsoro da zuciyarsu kafin gaske da basa shakkar komai da kowa a duniya idan ba shi dinba da babu Wanda baya sauke masa Kai idan ya fito sbd girmamawa dan shine ya jasu cikin jikinsa da dukiyrsa ya maidasu mutanen da kowa yake shakka a yanxu dan haka duk da wasu sun girmesa wasu kuma tsarin shekarunsa ne da wainda ma ya girma gabaki dayansu a uban dayafi kowane uba daraja kimar da zasu iya tasa yaqin duniya akansa suke kallansa,

Tsoronsu akeyi shakkar su akeyi sosai sbd uba gidansu yana dukiyar da suke juya duniyar yanda suke so,
Kusan dukkanin yaran nasa babu Wanda baiyi zaman gidan yari ba sbd rashin adalcin sharia amma ayanzu sun Kai sun taka matsayin da koda a gaban mutane zasuyi Kisa babu Wanda zai dago ya kallesu amma kuma ba irin rayuwar suke yiba yanzu dan kuwa business suke me tsafta da class da tsari amma duk da hakan kallan yan taadda masu karfin gaske ake musu Ana tsananin shakkarsu.

Yaransa sune yan uwansa,
Sune danginsa,
Sune yake shiga cikinsu yayi nutsuwa ko babu hayaniya sune ahalin da suka cike gurbin ahali da dangin da baida kaman yanda shima shine ya cike gurbin iyaye da yan uwan jini da suka rasa dan haka Bayan komai akwai kauna mai tsananin karfi a tsakaninsu dasuke wa juna su dashi,

Iya kafuwa da tsayuwa GHAZ empire ta tsayu,
Manyan qasashe da Masarautu ne da manyan tycoons na karshe ne abokan huldarta dan hakkanne NUAB ALMAZ yayi suna da fice a duniya da yake da Wani irin matsayi da girman gaske a idanuwan duk wani marasa karfi da galihu,
A cikin abokan huldarsa kuka shi din Zakin dayake yawo ne da saa a rayuwarsa,
A gurin tarin yaransa da uwansu ya kere na Masarautu da dama shi sarki ne da a duniyar nan idan yace A to A dince idan yace kuma B ce to dince kawai ko uban kowa ya yadda ko kada ya yadda,
Shi sarki ne da ko masarautar ubansa yace su tayar bazaa kwana ba saisun saka jini gudana a cikinta ta shefe kaman baayi kowa a cikinta ba.

Duk suna da tambarin da ake masa Akan zamowa gatan yan taadda bai taba bawa ko yan jarida daman fira dashi ba Akan hakan sbd baya buqatan yiwa kowa a duniya bayani kawai dai yasan yana samun feelings na nutsuwa daga sauya musu rayuwan da yayi hakama kusan yanajin radadin daya sauya rayuwarsu zuwa ga illa sbd yasan ciwo da radadin abubuwa ire iren wainda suke tinda shima tin da qananun shekaru aka rabasa da tasa uwar da haryanzu baiji dumin jikintaba taji nasa,

Fushi ne a zuciyarsa da haryanzu bai huceba,
Zafi ne a cikin kansa da haryanzu wutarsa bata mutu ba,
Qiyayya ce me karfin gaske dayake wa jamaar Masarautar BOYEM da haryanzu bai sauka ba sai ranar da mahaifiyarsa ta shigo hannunsa ne kadai komai zai iya fara sassautowa.

Duk wani Zafi da fushinsa a zuciyoyi da kan Yaransa take ci batareda sun San menene a ransa ba dan haka iya gane menene zuciyarsa amma dai tinda suka sansa sukasan da wannan wutar dake ci a cikin idanuwansa dan haka tasu zuciyar da ruhin basu taba Dena ci da wutar Zafi ba da jiran kowane umarnin sa Akan koma menene ba.

Duka wannan rashin tsoron da rashin shakkar da GHAZs kaman yanda ake ambatar su sbd sunan komai nasa daya mallaka a rayuwarsa sunan mahaifiyarsa ne amma iya GHAZ din suke dashi sun samo izzar hakan ne daga ubangayyarsu LEUL NUAB ALMAZZ da babu sunan shakka ko tsoro bare fargaba a cikin littafin rayuwarsa datake tsaye cak kaman mashi,

Komai Zafi da rashin saukewa kowa Kai a duniya idan ba shi ba basu kamo sa ba ya dame dukansu ya shanye babu Wanda kaf duniyar baya iya dagowa ya kalla da idanuwansa idan ba iyayensa mata ba sai kuma ubansa dabai San yaya zai kallesaba tinda basa tare shekaru.

Izzar dayake bugawa da iko tareda taqama da tsananin power dayake Juyawa da ita sun hadu hade ne da jinin dayake yawo a jikinsa na sarautar BOYEM,

Duk wannan shekarun yayi su ne yana jiran ranar da Amminsa zata furta masa ya taho ta janye kamalanta na kada ya dawo,

Daga ranar da Amminsa ta furta masa tana son zuwansa to tabbas a ranar bazai kwana ba sai jirginsa ya saukesa qasar BOYEM hakama bazai Baro ba saiya tabbatarda uwarsa ta dawo hannunsa.

Wannan kiran shine kiran dayake jira daga mahaifiyarsa kowace daqiqa dan haka aleey ma koyaushe a shirye yake tsaf da jiran kiran ya shirya saukar su BOYEM da me BOYEM din gabaki dayanta duk da baya buqatan mulkinta.

Villa dins datake kamar gari guda kusan fiyeda rabin Yaransa dake Russia suna cikinta bangare daban daban Sauran yaran nasa kuwa suna qasa daban daban inda yake da companies dan haka villa din akwai tsaro mai tsari da rashin hayaniya,

Duk Wanda yake karkashin GHAZss baya cikin wahala ko talauci Bayan kwanciyan hankali da rashin hayaniya sai zallar iko da rashin tsoro dan Sam baya kaunar lusari ko sakaran namijin da bazai iya tsayawa namiji ya cire tsoro a zuciyarsa ba a karkashinsa dan hakanne ya kasance duk Wanda yake karkashin GHAZss babu Wanda ba tsayayyen namiji mai zarra ba hakan ne ya saka koina suke kwarjinsu daban yake bare ace uban kwarjinin nasu na guri.

*******
Hayaqi ne da qamshi yake fitarwa me nutsuwa yake cike da gauraye toilet din  mai tsananin girman da koina daukan ido yakeyi sbd kyallin tsaddan luxury vinyl tiles da komai na Duravits toilets dayake tsare a toilet yana saka jikin duk Wanda ya kalla mutuwa,

Qarar shower ce yake tashi a cikin luxury steam and sauna shower room dake cikin toilet alamar wanka akeyi da ruwan dumin da hayaqinsu yake bada qamshin shower gel dinsa na the Noir,

Tsawon mintina a ciki kafin ya kammala
Hannunsa me tsananin haske da lafiyar fata ya bude kofar kafin kafafunsa suka fito ya fito gabaki dayansaa ruwa na gangarowa daga lafiyayyar farar fatarsa da Hutu da lafiya kawai take bayyana wa tana daukan ido,
Ruwan ko zama basa yi a farar fatarsa Kal sbd santsi da lafiyarta gangarowa sukeyi kawai suna sauka qasa.
Chapter 54 · 0% Book details