← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 76

Sashe 10

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsananin Zafin rana ke dukansu ga kuka da suka kasa Denawa sai hakan ya fara raunana lafiyansu dan haka daqyar sukai shiru Ayanah sai a lokacin ta dago ta kalli Abaas Wanda kansa ke qasa har qasa lokacin burinsa na zamowa namiji,dan uwa kuma uba dayake fatan wata rana zuriarsa data Ayanah ko daya daga cikin yan uwansa yana narkewa tareda bin iska a yau,zai mutu batareda samun wannan cikar burinba.

Sakina ce cikin tsananin kukan da tasan illa da nakasun da rayuwarsa zata samu daga yau ta saka hannu tana zare ‘yan kunnan azurfan dasuke kunnenta duka guda biyu ta kamo hannun Ayanah dake kuka sosai ta saka mata su ahankali tana Juyawa baya jikinta a sanyaye sbd ita har yanzu baiwar su ce bazata kalla yanda zaa yaga qimar uwayen gidanta ba.

Qanqame abin kunnayen Ayanah tayi a hannunta tana dauke kanta daga kallansu su duka kukanta na Neman tsananta amma dole zata aikatawa dan uwanta hakan.

Zuhrah ce da itama kukan takeyi ta miqe tsaye tareda Kama hannun Ayanah ta kasa maganar da zatai sbd kukan dake zuwar mata sabo mai ciwo dan haka juyawa tayi itama tana Dora hannunta a kirjinta dake ciwo da nauyi.

Rarrafowa Ayanah tayi cikin mummunan gaban Abaas din tareda daga hannuwanta dake rawa sosai takai tafukan hannayenta fuskansa ta tallafo ta kallesa ya Lumshe idanuwansa yana kasa barin taga tsananin rauni da baqin ciki tareda quncin dayake cikinsu sbd kada ya qarasa karya zuciyarta da gangar jikinta.

Bakinta takai kan gefen fuskansa ta sumbacesa hawaye na gangaro mata kafin ta sake dorawa kan goshinsa ta sumbacesa hawayenta na diga kan goshin nasa.

Zuhrah ma cikin karfin Hali tana danne zuciyarta ta juyo ta durqusa gabansa ta Kama hannuwansa biyu ta sumbacesu duka kafin ta sumbaci tsakiyar kansa da gashinsa me tsayi kaman mace yake daure har lokacin.

Tafin hannu Ayanah ta bude ta kalli yan kunnayen kafin ta daga ahankali tareda Kama kunnansa,

Bude idanuwansa yayi ya sauke Akan fuskan Ayanah din wadda cikin idanuwansa take kallo tana masa kallan tsananin kaunar dake nuni da har abada idan kowa zai gujesa su suna tareda dashi har mutuwa sbd su a gurinsu rasa kowace darajarsa ba ta ‘da namiji.

Baice komaiba Bayan rufe idanuwansa da yayi ahankali sbd su kadai yake buqata a rayuwarsa daman kuma idan yana tareda su shikenan zai iya jure komai.

Hannunta ta Dora a kunnansa cikin radadin zuciya ta huda kunnan nasa da karfin da na karfin hali ne,

Zuhrah kaman a zuciyarta haka taji hujin kunnan shi kuwa ko motsawa beyiba sai wasu hawayen da bana radadi bane suka gangaro masa.

Haka Ayanah ta huda Dayan kunnan tana bar masa yan kunnayen a kunnuwansa.

Tallafe fuskansa ta sake yi da hannuwanta tana kallan idanuwansa dake rufe yana riqe kukansa me tsanani dake zuwar masa.

Itama kokarin riqe nata takeyi har saida Zuhrah ta saka hannunta cikin riqe nata kukan itama ta zare daurin gashinsa take gashin ya sauka har kafadarsa,

Wani irin kuka me karfi da gunji suka sake a tareda dukkaninsu suna rungumesa.

Har lokacin Sakinah bata juyoba itama kuka takeyi sosai a yanda take,

Nurat ma kukan ta fasa tana fadawa cikinsu tareda ambatar Ayanah da AMMA itama.

Rigar Zuhrah me dan adon Kayan mata suka zare aka saka masa tasa kuma Zuhrah din ta saka.

Sakinah ce ta matsa kadan gaba ta Debo wani ganye shar ta kawo Ayanah ce ta murza ganyen da hannuwanta biyu ta goga a fuskan Abaas din Wanda bazai bazai taba barin gashi ya fito a fuskansa ba.

Sake rungumesa Ayanah tayi suka sake samun Yar nutsuwa da dangana kafin suka miqe suna kama hannuwan juna suka bi hanya ahankali cikin galabaita Wanda babu ta yanda zaka zan akwai namiji a cikinsu..

Koda rana ta fadi babu me iya tsayuwa sosai a cikinsu sbd tafiya da azaba,
Kafafunsu dukansu babu Wanda bai fashe ba,

Kaman a mafarki suka fara hango ruwa me yawan gaske yake dukkaninsu suka Ji sun samu dan kuzarin daya qare musu.

Ruwan suka nufa suna jin maqoshi da jininsu na sake qafewa.

Ana magrib suka isa ruwan Wanda da rarrafe dukkaninsu suka qaraso sbd qarewar karfi gabaki daya,
Nurat bata iya qarasowa ba sbd ranta dake gap da fita dan haka Abaas ne yayi saurin diban ruwan da hannuwansa biyu yana kawo wa inda take yana bata a baki batareda damuwa sa qazantar dake ruwan ba.

Daqyar yake takawa yana kai mata ruwa yana zuba mata a baki har shima ya gaza ya fadi yana zubewa a gurin.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

10

*_PRIME SCENT_*
08103155915
Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa?
Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents?
Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites?
Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa?
Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT
Duniyar kamshin da babu kamarsa,
Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba,
PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu.
08103155915
********

Ayanah datai tsananin laushi itama ce ta qaraso gurinsa da rarrafe cikin sauri tana kokarin kamo sa amma hannuwanta rawa sukeyi sosai gashi bata da kuzari sai kuma ta kasa iya Dena kokarin rungumosa jikinta idanuwanta da sukai surfi sosai suna kasa ko hawaye.

Sakinah ce da itama taje Numfashi daqyar ta matso ta fara Debo ruwan itama a hannunta tana tahowa tana zubewa a bakinsa suka samu yasha sosai numfashin sa ya fara daidaita ya rufe idanuwa yana lashe lips dinsa da suka bushe qayau harsun fara tsagewa.

Ayanah ma Sakinar ce ta kawo ruwan ta ringa bata ta dan samu karfi da kuzari itama tana lashe bakinta daya bushe ya tsatsage.

Acan bakin ruwan sakinah tasha ruwan sosai itama kafin ta zube a gurin a kwanta tana sauke Numfashi bakinta itama yana samun sassaucin azabar yankewan bushewa.

Zuhrah kuwa daman tana bakin ruwan tin dazi a kife Jin takeyi kaman ta fada ruwan ta sanyaye jikinta da bakinta da suka bushe har sun yayyanke musamman kafafunsu da basuda kyalla sun fashe kace kaca sunyi wata irin Dauda da munin kalla.

Ba iya kafafunsu ne da munin kallo ba sbd Dauda me yawa hadda su sbd dauda ce sosai a jikinsu tareda jinin da sukayo gwagwarmaya dashi daya bushe a jikinsu tin daga kan na Ammansu dama Abaansu da Ayanah ta taba saina Asamah dama Sauran wainda aka kakkashe tin farkon barowansu babu me Kyan gani a cikinsu sbd sun koma wata halittar sbd dauda da kyama.

Dukkaninsu kwance suke a gurin babu Wanda ya motsa Numfashi suke sauke wa a hankali ba kuzari kuma ma idan sun miqe basu San tayaya zasu tsallaka ruwan ba bare dan haka magana ce ta sake zagayawa dajin zasu yi Neman hanyar da zata fiddasu inda ba ruwa su fice daga nahiyar gabaki daya su fada inda garururwa da Jamaa suke.

Shiru sukai kowa idanuwansa na kasa qaqaro hawayen tashin hankalin inda zasu sake komawa dan Neman hanya.

Kasa tashi kowannensu yayi a gurin anan suka kwana kwance gaban ruwan kowa a inda yake zube anan ya kwana sai asuba suka dan iya tashi suka hade guri daya suka dunqule sbd tsananin sanyin ruwan dayake ratsa su.

Daqyar suka iya sallah Bayan gari yayi haske suka sake Zaunawa guri daya a hade kaman kashin awaki,

Shiru sukai suna tinanin yanda zasu sake komawa su kutsa cikin dajin Wanda basu San ranar fitar sa ba,

Tsananin tsoronsu haduwa da Kusra da suke cikinsa dan haka suke Jin kaman suyita zama bakin ruwan har ransu yabar jikinsu.

Zuhrah da har jikinta ya fara rawa sbd tsananin tsoro da tashin hankali tareda tina azababbiyar tafiyar
kallan Ayanah tayi da idanuwanta da sukai ja sosai ta bude baki cikin tsananin tsoro da sallamawa tace

‘Ayanah wannan itace karshen kaddararmu,
Mu karbeta kada mu koma dajin nan,
Mu fada ruwan nan rayuwarmu tazo Karshe mu huta dan Allah,
Bazan iya ba Ayanah,
Mutuwar tafi mana biyu Hutu da sauki dan Allah Ayanah mu fada ruwan nan mu tafi mubar duniyar nan wlh bazamu iya ba,
Koina bazamu kai ba zamu rasa kanmu dan haka dan Allah mu yankewa kanmu wahala…..

Abaas na Jin hakan yaji zuciyarsa na Aminta da yadda da hakan dan haka Ayanah yake kalla idanuwansa cikeda hawayen rauni da ‘qunci yana Jiran jin tace ta amince da hakan,

Kallansu Ayanah tayi tana jin zuciyarta na yadda da hakan itama sbd tabbas din bazasu iyaba dan haka gwara su mutu anan tin kafin azabar da ukubar tayi yawan da babu iyaka.

Ganin yanayin Ayanah din na itama tana ganin hakan shine zai fi musu yasa Zuhrah Jin dan dadi dan har zuciyarsu gabaki daya sun zabi mutuwar sbd itace hutun karshe da zasu samu a wannan duniyar dan haka miqewa tayi tana Juyawa ta kalli ruwan tana Lumshe idanuwanta zuciyarta cikeda samun nutsuwa ta juya gurin Nurat dake Zaune quri babu alaman tasan komai dayake gudana a rayuwanta yanzu ta durqusa gabanta ta kamo fuskanta da tafukan hannuwanta biyu takai bakinta ta sumbaci gefen fuskanta da gashinta kafin ta hade goshinsu tana cewa

‘Nurat inda su Abaa da Amma suka tafi zamu tafi zamu bar nan bazamu iyaba,ke kin rasa hankalinki bazaki taba gane azabar da zamu shiga ba amma kuma zaki kasance cikin hadari dan haka mu tafi….

Kama hannun Nurat tayi ta miqar da ita ta kalli Abaas ta miqa masa hannu shima ya Kama ya miqe tsaye,

Ayanah suka tsaya akanta suna kallan da jiranta,
Chapter 10 · 0% Book details