← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 76

Sashe 55

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gurin da towels suke a Jere a tsare kaman bundles na kudi ya nufa ya miqa hannunsa daya ya dauko daya ya daura a kuqunsa kafin ya sake daukan daya a natse cikin asalin nutsuwan sarauta dake yawo a jininsa ya Dora a kan gashin kansa dayake tamkar na mahaifiyarsa yafara gogewa ahankali kafin ya fito sanye da fararen soft sole bedroom slippers yana nufar makeken dresser mirror din dayake closet dinsa mai girman dayafi na daki biyu dan kuwa tarin sutura ce a Jere da basada adadi babu kalar designer din data amsa sunanta da babu a gurin tin daga kan bangaren agogunansa da suke bugun mahaukatan dollars har zuwa kan takarman sakawansa da suke cin manyan kudi da bangaren wandunada shirts da suits da underwears hatta ties na wuyansa da socks dinsa kowanne da bangarensa daban inda aka jerasa.

Ga turaruka suma da pins da combs nasa suna kowanne baida adadin number dan babu abinda ake siya kadan hakama akai akai ake qaro wasu Ana jibgawa.

Cikin nutsuwa da rashin hayaniya ya shirya tsaf a cikin navy blue loro pianas vicuña polo shirt da Michael kors trousers fari tas ya komai na jikinsa na fidda wani tsadadden qamshin Gaultier elixir na yana gauraye niimar duk inda ya wuce da inda yake tinkara a cikin sanyi.

Palonsa na hutawansa y wuce Kai tsaye cikin nutsuwa zuwa palon da dining room dinsa yake inda zaiyi breakfast da aka gama cike dining din a tsare da aji,

Tin daya doso qamshin sa ya sanar da aleey fitowan sa dan haka ya miqe daga Zaunen dayake riqe da iPad me girma dayake wani aikin report da aka turo daga kamfaninsu dake Brazil.

Ajiye iPad din yayi yana dago Kansa ahankali ya sauke Akan hanyar da NUAB ALMAZZ din daya fito kwarjinsa da Kyansa dayake sake cika idanuwan duk me kallansa na cike gurin gashinsa dayaji tsadaddun mai yana sake a kafadarsa ya dago idanuwansa da babu abinda suka Baro na mahaifinsa ya Dora Akan aleey din yana qarasowa kenan wayar sa da iya mahaifiyarsa kadai ke kiransa da wannan layin tayi haske tana ringing mara qara.

Dago wayar da hannunsa yana dakata wa cak ya fasa isa dining din ya isa kan wasu mahaukatan luxury sofas dake palon ya zauna a natse tareda ajiye Dayar wayar hannunsa a gefensa kafin ya daga wayar cikeda nutsuwa da kulawan da baya bawa kowa duniya sai ita ya bude Baki muryansa mai tsantsar nutsuwa da Izzar sa da bata boyuwa yace

‘Ya Ammi….

Katsesa maganarta da muryan data tada tsikar jikinsa gabaki daya da cewa

‘HAYATEEM Inason kasancewanka a tareda ni duk lokacinda Ka samu daman hakan……
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

50
Gashin jikinsa ne suke qarasa miqewa ahankali maganarta ta ratsa kunnuwansa zuwa kwakwalwan kansa da zuciyarsa data tsaya cak gurin bugawa,

Numfashi me sanyi mara sauti ya sake a natsensa dan gasgatar da maganar Ammin tasa da bata taba raayin dawowansa BOYEM ba haka kawai amma Ayau kunnuwansa na jiye masa sabanin kalamanta na koyaushe da kullum,

Bude bakinsa yayi cikin sautin da ita kadai yakewa magana dashi sbd sanyinsa da nutsuwansa yace

‘Ammi,kina buqatan ganina?
Akwai abinda yake damunki Ammi?’….ya qarasa maganar da zallan kulawansa da kaunarsa akanta yana jiran amsarta dan karantar yanayinta dayake cikin sautin muryanta.

Shiru tayi itama acan bangaren nata tana rufe idanuwanta ahankali sbd muryansa dake ratsata a duk lokacinda zata ji muryansa tsananin kaunar danta kaman zata qarasata takeji amma hakanan take daurewa shekaru masu yawa sbd koyaushe zuriyarta na hanata barinsa dawowa sbd kada aci gaba da kiransa dan mistress Wanda ako Yaushe aka ambacesa da hakan har cikin ranta da zuciyarta take Jin radadin hakan musamman data ga sunan yana kokarin zama abin alfaharinsa dan baitaba Jin ciwo ko damuwan abinda ake ambatar sa dashiba amma su sunajin ciwon hakan,

A yanxu zuciyarta takai maqurar kasa daurewa da hakurin rashin ‘danta a tareda ita musamman da zuciyarta take cikin rashin sukuni sosai da Wani irin tsoron da batasan na menene ba dan haka jikinta yake Neman rikicewa sbd ko bacci kwata kwata ta rage sosai Wanda shima yake qarawa lafiyarta illa me girma dan haka su tenya da sakinah suke cikin tsananin damuwa da rashin yaya zasuyi gashi basuda ikon sanar da sultan suke gani tinda bata gabansa babu abinda yake gabansa nata likita dayane tinda ya nadasa mai duba lafiyar Ayanah din shikenan baitaba fasa zuwa bibiyan lafiyar taba koda Yaushe a tsawon shekarun nan,

‘Ammi’ ya Ambaci sunanta cikin sanyi da kauna me girman gaske tareda nutsuwan da bayason damar da ita sbd jinta shiru.

A sanyaye ta sauke bayyananniyar Numfashi jikinta gabaki daya a mace ta bude Baki tace

‘NUAB,Yene HAYATEEM,Yene LEUL idanuwana suna son ganinka,
Zuciyana da ruhina duka san ganinka sukeyi kafin na…..’

Katseta yayi da tsananin nutsuwa da cewa ‘AMMI’ sbd yasan kalman mutuwa ne zata qarasa dashi,

Tsigar jikinsa ne suka sake tashi a hankali Wani irin yanayin da mahaifiyarsa ce kadai ke motsa zuciyarsa na ratsashi sbd ya tabbatarda akwai abinda yake damunta ko zuciyarta dayayi girman datake buqatan ganinsa harta furta da bakinta,

Dole wata damuwarce take faruwa da kila batasan tayaya zata iya gane wa ko fada masa ba kawai ta buqaci ganinsa sbd zuciya da ruhinta su sanyaya,

Numfashi mara sauti ya kuma saukewa tareda dagowa idanuwansa farare tas masu Kayar da gaba da suka sauya a take suna dan rikida da ja ya bude Baki a natse yace

‘Ammi bakida lafiya ne?

Girgiza masa Kai tayi a hankali da sanyi kaman yana kusa da ita Wanda sautin ya shigar masa kunne a cikin sanyi dan haka ya rufe idanuwansa ahankali ya kuma bude su yace

‘Akwai abinda yake damunki Ammi?

Nan ma girgiza Kai tayi a natse batareda tinanin ba lallai ya fahimta ba,

Nan ma yaji Gyada kan sbd akwai yan kunnen zinari masu dan fidda sauti kadan a kunnuwanta Wanda ya saka idan ta girgiza Kai sautin su ke shiga kunnuwansa suna narkar da zuciyarsa da babu abinda take tsananin so da kauna a duniya idan ba ita din ba

‘Ammi akwai Wanda ya saka miki damuwa’

Girgiza Kai tayi ya sauke Numfashi me sauti wannan Karan ya bude baki zaiyi magana muryanta ta Katsesa a sanyaye tace

‘Idan zaka taho kazo da Abaas,ina son ganinsa HAYATEEM’

Rufe idanuwansa yayi a Wani irin yanayin da zuciyarsa ke cizo da radadin kasa bawa macen da ita kadai ce rayuwansa abinda takeso sama da shekaru masu yawa.

‘Ammi zan taho gareki ba tareda Abaas ba amma nayi miki alkawarin indai Abaas yana raye zan kawo miki shi a gabanki,
Nayi miki Alkwarin indai Abaas yana raye zan Nemo miki shi zai qarasa rayuwarsa a gabanki bazai taba barin gabanki ba har sai mutuwa ta rabaku…..

Wasu hawaye ne suka gangaro idanuwanta da suka saka hankalin sakinah dake tareda ita a palo Zaune tashi sbd bata kuka Sam a yanzu sbd kuncinta da baason ya dawo dan haka a natse ta iso gurinta ta zauna gefenta ta kalli wayar hannunta ta miqa hannu tace

‘Nima zan gaisa dashi’

Miqa mata wayar Ayanah tayi cikin nutsuwa tana cewa ta yadda da NUAB zai cika mata wannan alkawarin ko Bayan ranta ne zai nema Abaas.

Maganar tata har kunnuwansa ta sauka ta shigesa a hankali ya Lumshe idanuwansa yana Jin wata wuta mai Zafin gaske tana kunnuwa a zuciyarsa ta son kasancewa da mahaifiyarsa da tabbas lokaci yayi da zai dawo da ita hannunsa dan kuwa daman magana daya ce duk ranar daya saka kafa a BOYEM to bazai taba tafiya batareda mahaifiyarsa ba,

Babu me buqatarta a masarautar da qasar gabaki daya hatta Wanda take zamansa baya buqatanta ya watsar da ita tin tanada kuruciya dan haka shi babu abinda yake buqata a rayuwarsa sama da ita a basa ita kawai shine cikar duk wani burinsa na rayuwa Bayan hakan baya buqatar komai a rayuwarsa.

Saukar muryan Maa sakinah a kunnuwansa ya sakasa bude idanuwana jajir yana bude baki a natse da kulawa yace

‘Maa akwai abinda yake faruwa ne??
Akwai abinda ya kamata na sani ne??
Amminah na da damuwa ne?
Akwai abinda yake faruwa a masarautar ne daya taba Amminah?

A Jere ya jerowa Maa sakinah tambayoyin da suka saka jikinta sanyi ta sauke ajiyan zuciya mara karfi tareda bude Baki cikin nutsuwa ta manyanci tace

‘Babu komai dayake faruwa kawai dai yanayi ne na kewanka datake yi shine kadai ya saka amma ka damu babu abinda yake faruwa’

Shiru yayi itama Maa sakinan yana karantar yanayin muryanta datai sanyi sosai,

Kai tsaye yace

‘Maa akwai abinda yake damunki kema?
Menene yake faruwa a masarautar nan?
Waye ya tabaku?

Katsesa tayi da sauri tana kokarin daidaita kanta cikin sauti da dan sauri sbd Jin yanda muryansa ta fara sauyawa tana daukan Zafi da fushinsa da babu me iya kashe wutarsa tin yana yaro tace

‘Babu komai Ka yadda da hakan LEUL,kada Ka bata ranka ko kadan dukanmu muna cikin kwanciyan hankali da lafiya’

Kasa nutsar da zuciyarsa dake daukan zafi yayi ya bude Baki cikin sassauci yayi sallama da ita Kai tsaye wayar Maa tenya ya kira yana bude idanunwansa da sukai jajir Akan Agogon dayake palon dan kuwa matiqar yaji ya tabbatarda akwai damuwan dasuke ciki babu abinda zai Hana jirginsa sauka BOYEM kafin fitowan alfijir din asubar gobe.

Maa tenya dake dakinta ta gama sallar nafila wayarta dake kan marble center table din dayake lafiyayyan dakinta da babu duniyar da babu a cikinsa koina na Qamshi da sanyin ac tafara ringing.

Hannunta ta miqa a sanyaye ta dauki wayar tareda dauka ta Dora a kunnanta cikin sanyi tayi sallama tana miqa masa gaisuwan data zama kaman dole kasancewansa jinin BOYEM kuma asalin magajin karagar mulkin.

Bai amsa gaisuwan sarautarsa ba ya miqo mata tasa gaisuwan ta zamanta uwa a garesa kafin ya Dora da cewa

‘Maa idan akwai abinda yake faruwa ki sanar dani sbd ina rasa hankalina anan sbd Amminah akwai abinda yake damunta kuma Inason saninsa koma menene’

Ajiye Numfashi me sauti sosai tayi kafin ta sake shiga sanyi da nutsuwa tace
Chapter 55 · 0% Book details