← Book details Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 76

Sashe 25

Hayateem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakinah dake gabansu dan juyowa tayi ahankali ta shiga tsakiyar su itama idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin tausayinsu musamman Ayanah dake girgiza kai ahankali idanuwanta na tsananta ja hannuwanta na fara rawa ahankali ta bude baki tana kallan Zuhrah dake kallanta tana hawaye masu tsananin rauni da ciwo tace

‘Zuhrah bazan iya rayuwa babu ke ba,
Zuhrah na zabi barin duniya tareda dake mu tafi mu huta…..

Girgiza kai Zuhrah tayi hawayenta na tsananta jikinta a sanyaye tace

‘Abaas fa?’

‘Allah zai zama gatansa amma a yanzu da kike tare dani bazan iya rayuwar da babu ke ba Zuhrah’

Kuka Mara sauti Zuhrah ta sake tana kokarin zare hannunta daga na Ayanaah din tace

‘Sbd ki rayu tare dani din zan zabi hakan,
Inason ki rayu Ayanah ki samu rayuwan da zai baki nutsuwa dan hakanne dole zamu zabi raba jini,
Kina raye Ina raye muna Masarauta daya muna shakar Numfashi guri daya insha Allah zamu samu yancinmu wata rana mu tafi tare’

Girgiza kai Ayanah tayi da karfi tana sake riqe hannun Zuhrah tace

‘Zuhrah idan muka zabi hakan mun rabu kenan har abada,muna guri daya amma bazamu taba nuna mun san juna ba bare Hadin jini,
Bazamu taba sake jin dumin juna ba,
Bazamu taba kallan juna ba,
Bazamu taba dawowa Ayanah da Zuhrah GHAZ ba shikenan mun rabu har abada sai kuma ranar da Allah ya bamu yanci Kinsan da hakan?
Wannan shine doka da qaidar kuma taka hakan a bakin rayuwarka kenan,bazan iyaba Zuhrah.’
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee

23
FREE CLASS ALERT
07068433198
Kinason business dinki ya zama tamkar kamfani me zaman kansa,
Kina da kaya ko sabis Amman tallanki baya Jan hankali?
Mutane suna ganin tallanki Amman basa saye?
Lokaci yayi da Zaki koyi yadda ake vedio advert mai daukar hankali da kawo kwastomomi🥳🎉
Shiga wannan FREE CLASS ki koyi yadda ake hada vedio da zai juya masu kallo zuwa kwastomomi🎉

**********
Sakinah data yadda da indai zasu rayu gwara su hakura din matiqar sunsan suna guri daya yafi a san sunada alaqa tin anan gurin a kashesu a banza kokuma a rabasu duniya daban daban gwara su tsaya guri daya koda babu abinda zai sake hadasu har abada dan haka hannuwansu ta Kama da hannuwanta biyu ta rabasu da karfi Zuhrah na Wani irin kuka Mara sauti zuciyarta na mutuwa a matakin karshe na shikenan.

Ayanaah ma wani irin kuka takeyi mata sautin tana kasa dauke idanuwanta daga Zuhrah wadda itama ita take kalla sakinah ma hawayen takeyi tana sunkuyar da kanta qasa.

Layi na zuwa kansu sunansu AYANAAH GHAZ da ZUHRAH GHAZ Ana tambayan alaqarsu Ayanah ta dago jajayen idanuwanta da suka rine gabaki daya ta zubawa Zuhrah wadda ta goge fuskanta tas ta bude baki tace

‘BABU ALAQAR JINI sunan ne iri daya’

Tana fadar haka take aka buga stamp a sunayensu tareda wata irin stamp ta daban wadda take bada tabbacin ko a toilet daya tsautsayi ya hadasu a kashe dayansu abar daya sbd kawar da zargi hakama duk ranar da dayansu ya kalli daya shima hukuncin daya ne.

Miqa musu Id cards nasu akai tareda jansu zuwa ciki Wanda kowannensu babu abinda yake aiki a gangar jikinsu Bayan kafafunsu dake jansu kaman marasa lakka a jiki.

Hawaye ne masu tsananin zafi suka gangarowa Ayanah tanajin kusan komai nata na Dena aiki tanason dagowa tayiwa Zuhrah kallan karshe amma damar ta qare hakama itama Zuhrah Ayanah takeson kallan ba damar ta qare sedai hawaye suka sauko mata ta rufe idanuwanta tana bin inda ake tafiya dasu hanya daban da wadda aka tura Ayanah da sakina.

Duk Taku daya da Ayanah ke yi jin takeyi tana rabuwa da ruhinta sbd a yanzu kam takai matakin karshe na rasa komai nata batada Sauran hasken da idanuwanta zasu gani ko miskala zarratan,

Rawa kafafunta keyi zuciyarta na kasa wa sbd bazata iya rabuwa da Zuhrah ba koda hakan zai rabata da rayuwanta ta yadda dan haka ta dakata ahankali daga tafiyan datake,

Dagowa tayi ahankali zata juya ta kalli Zuhrah koda hakan zaiyi sanadin rayuwanta,

Da sauri sakinah dake bayanta ta riqeta cikin nutsuwan da bazata bari a gane su ba ta hanata Juyawa sbd bazata iya barinta Juyawa ta rasa rayuwanta kokari da sadaukarwar Zuhrah ya tashi a banza,

Wasu hawayen ne masu tsananin zafi suka cigaba da gangarowa Zuhrah wadda itama bata juyoba tana Jin ciwo da radadin halinda Ayanaah take a jikinta,

Sakinah ce ta iya waiwayowa a hankali ta zubawa Bayan Zuhrah dake tafiya jikinta na bayyanarda gap take da samun bugawan zuciya,

Tausayinta ne ya rufe zuciyar sakinar sbd ita zata rayu bateda duk Wanda rayuwarta ta taba sani ba dan gwara Ayanaah din ita tana tareda ita,

Koma menene tasan wannan ma wata sabuwar jarabawar ce Allah zaici gaba da jarabtarsu da ita,

Ahankali ahankali aka gama rabasu zuwa bangarori da dama Wanda sai da aka kuma daukansu cikin wasu motocin aka isa dasu can ciki inda duniyar boyem take,

Tsari da yanayin gini da aljannar duniyar dake cikin Masarautar boyem ya wuce tinanin duk wani labarin daular duniya da ake bada labari da tarihin Masarautu,

Tamkar suna tafiya baa cikin duniyar ba haka suke jin kansu sbd koina da ake giftawa dasu madubai ne suke ganin kansu a ciki suna daukan idanuwansu dan haka tsoro duka ya cika su suka sake saukar da kawunansu a qasa suna kama jikinsu dake rawa sbd tsoro suna tattaro nutsuwarsu sbd itace gaba a komai na aikinsu.

Kai tsaye sabon bangaren bayin dake cikin masarautar aka kaisu aka basu daki shima kamar wancan da suka Baro daular bayi sedai wannan Mutum uku uku ne a daki.

Duniyar da aka jefata daban data Zuhrah sbd tsakanin bangare da bangare akwai yar tazara da kuma tsaro sosai dan haka ita kai tsaye ita bangaren imebētiś aka kaita Wanda yake duniya ce guda mai zaman kanta wadda take dauke da part part sun kai hamsin duka na imebētiś ne maana mistresses na sarki,

Duk macen da sarki ya kwana da ita indai ta samu ciki anan zaa bata flat dinta mai shegen kyau da wata irin daula a cikinsa tareda bayi sama da goma wainda sun zama nata zatai rainon cikinta anan ta haihu anan ta reni jini boyem cikin jin dadi da daular da hankali ma bazai daukaba kuma anan zataci gaba da rayuwanta da bayinta cikin jin dadi da yanci har sai jinin BOYEM data haifa ya girma ya kai shekaru goma sha biyar shikenan zaa ware masa nasa muhallin daya zarce tinani acan cikin asalin ginin da sultan yake a zuba masa bayin ya koma can sedai Yazo gaida mahaifiyarsa kokuma ita taje gurinsa.

Duk macen da sarki ya kwana da ita kuma bata samu ciki ba bangarensu daban bautar suke komawa sedai Ana sauya musu guri a cire su cikin asalin bayi,

To Ayanah a cikin bayin dake kulawa da sabuwar imebētin sultan aka kaita itada sakina ita kuma Zuhrah a can asalin bangaren uwargidan sultan aka kaita dan haka sukaiwa juna Nisan da babu ranar cike gurbin.

Tinda suka iso dakinsu Neman somewa Ayanaah keyi sbd halinda tashiga na rabuwa da Zuhrah daqyar sakina ke kokarin bata taimakon daya hanata somewan sedai har tsakar dare tana fama da ita kafin Allah ya kawo mata dangana ta sakawa kanta karfin halin hakura.

Washe gari tinda asubar fari suka shirya cikin uniform dinsu tsaf suka fito zuwa aikinsu,

Kai tsaye bangaren sabuwar imebetin suka isa su shida ne dan haka suna isa suka bude suka shiga kai tsaye kowannensu ya fara hidimarta tin kafin ma ta tashi.

Ayanah aikin gyara toilet tayi tareda wanke Kayan wankin da ime din tayi amfani dasu ta wanke su sosai da hannuwanta batareda ta saka washing machine ba duk da an koya musu komai da yanda zasuyi amfani da koman a gurin karatunsu,

Tana gamawa sake gyara toilet tayi ta hada mata ruwan wanka masu dumi sosai da Kayan qamshi masu dadi na wanka Wanda duka shima an koya musu dan kusan babu abinda baa koyar musu ba komai kankantarsa,

Tana gamawa ta koma bakin toilet din ta tsaya kanta a qasa tana jiran farkawanta,

Tsayuwan mintina talatin tayi kafin ta fito daga cikin makeken lafiyayyan gadonta mai rumfar dataji ado da dukiya.

Tana qarasowa ko amsa gaisuwan da Ayanah din tai mata bataiba ta zare rigar baccinta ta Sama ta Bari a gurin tareda shigewa toilet din daya gama tsaruwa,

Sunkuyawa qasa Ayanaah tayi a natse ta dauke rigar data zare din tana barin gurin ta kai rigar inda Kayan wanki suke ta dawo ta isa inda towels suke sama da guda ashirin ta dauko guda uku harda na goge kai suna wani qamshi me sanyi ta dawo bakin kofar ta tsaya da towels din.

Tsayi me tsanani tayi a gurin batareda ta motsa ba duk kuwa azabar datake ji ta tsayin hakan take a tsaye kanta a qasa har tsawon lokacin da batasan Yaushe ne ba tukuna ime din ta bude kofar toilet din Wanda Ayanaah tayi saurin miqa mata towel din farko ta amsa ta daura a jikinta kafin ta sake bata wani t rufo jikinta kafin na ukun ta Dora akai dan goge kanta.

Tana wucewa gaban mirror Ayanah ta fada toilet din ta sake gyaresa tsaf ta qamar da ruwan toilet din tsaf duk kaman ba yanzu aka fito wanka cikinsa ba.

Tana gamawa ta fito tana gyara dakin da gadon dakin sakina da wata baiwar daya suka shigo suna busar mata da gashinta tareda gyarasa tana zaune tana kallan kanta a madubi.

Tsawon lokaci suka dauka suna hidimarta kafin suk kammala ta fito cin abincin da Sauran su suka dafa mata sama da Kala daya ta zauna suka zagayeta kowannesu da abinda yake mata.

Har dare suna tsaye kan kafafunsu basu zauna ba Bayan sallah babu abinda sukeyi sai hidimarta wadda bata qarewa.

Sai tsakar dare sosai suka koma daki Bayan tayi bacci,

A tsananin gajiye suke dan haka komai babu Wanda suka iya yi bacci suka buge dashi mai karfin gaske,
Chapter 25 · 0% Book details