← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

9&10
By gentle
lady💃🏽


Tasoma sosar jikinta saboda tsananin zafinda tajiii take tasoma bata aikinda akamata Usman yana masallaci labila ma tafita tanabin jam i ana gama sallah suka taso tunkafin sukai dakin sukaji ihunta gabadaya yakarade asivitin

Dagudunsu suka shiga dakin Usman yana gaba labila tana bayansa" sunashiga suka rirriketa labila tasoma kuka tana mom meyasa kikeson jiwa kanki ciwone

Sai alokacin hankalinta yadawo jikinta taga abunda taiwa kanta saita fasheda kuka dasauri Usman yafita Kiran nurse allurar barci akayiwa lubcy

Dasafe da doctor yazo yaga abunda tayi yatabbatarwa Usman indai anason ciwon nan yawarke dole adauremata hannuwa dangudun sosawarda takeyi tanamaida aiki baya

Usman bashida zabi yace ayihakan"" hakan akayi kuwa aka dauremata hannuwa tunda akawanke mata ciwon tasamu sauki batasakejin kaikayinba saida karfe biyu tasake yin mafarki da yaran

Wannan karon kamar mahaukaciya takoma Tanata ihu tana jijjigar gado kaikai takeji kamar bala I babu halin sosawa anacikin hakane su khadij suka isah hospital din

Koda suka kai kofar dakin mutanene sunyi cincirando duk da kofar arufe take cen tahango labila tana kuka dasauri takarasa wajenta tace sahiba

Labila tadago dasauri tana ganinta tafada jikinta tana kuka tuni idanuwan khadija suka kawo kwallah"" tace kiyi hakuri kidaina kuka addua zakiyimata insha Allah zatasamu lafiya

Sannu kan hankali tasoma rarrashintaa hartasamu tayi shiru"" likitocin dasuke dakin da lubabatu take sukafito doctor lawal yasa akadibi jininta akaje lab domin asake aunawa yace duka cutarda take jikinta arubuta dansu San taimakonda zasu bata

Alokacin tasamu saukin zugin dansaida akawanke ciwon dole akabarshi sake ba asa kadaba duk Wanda yake dakin karfin haline kawai yakeyi Dan saboda mugun doyinda dakin yakeyi

Karfe uku dangin lubabatu sukazo harda yayyunta Amman saida Usman yayita basu hakuri dancewa sukai subaruwansu tunda takeda lafiya bata nemesuba saiyanzu dabatada lafiya Ashe sunada rana

Usman yayita basu hakuri yace karsu dubi abunda taimasu sutaimaka suzo dakyar " suka amince sukace zasuzo koda sukazo har barci yasoma daukarta Amman tana kinyi

Danbataso tasake mafarki da wadan nan yaran tanaganin yangidansu kunya takamata dukkansu basuyi mintuna goma dakinba suka fita mahaifintane kawai yadan jima aciki

Yana fitowa kawai yayi waya Aturo masa wadansu likitoci turawa da gaggawa"" dukkansu ciwon lubabatu ya firgitasu""
Bayan angama komai akafitoda sakamakon gwajin jininda akayiwa lubabatu doctor lawal yaduba hankalinshine yatashi yayita maimaita abunda yaganie yadago yakalli Wanda yakawo sakamakon yace katabbatar wannan result dintane?? Yace ah

Shiru yayi yadafe kansa daga bisanie yace kiramun alhaji yace OK sannan yafita lokacin su khadija suka shiga dakin sosai itama hankalinta yatashi

Daganin yanayin da lubabatu take ciki saiyanzu Usman yaganta yace wayakawota asibatin??? Tacemasa driver

Zaiyi magana Wanda aka aiko kiransa yashigo yasanardashi yace masu yanazuwa yafita "" zuwa office din"" doctor din yatura kofar yashiga da sallama yadago yakalleshi yana amsa masa sallamarsa yakarasa doctor lawal yanuna masa kujera yace yazauna jiki sanyaye yaja kujerar yazauna

Danganin yanayin doctor din yasan akwai Matsala yatattara ragowar natsuwarsa duka zuwa gareshi

Shiru yayi yakasa magana dazaran yadago kai yakalleshi saikuma yayi shiru"" Usman yace kayimagana mana doctor nikasani cikin rudanie

Kasanardani meyake damun matata danna nema mata maganie banason ganinta cikin wannan rashin lafiyar

Doctor Lawal yanisa yace agaskiya dangane daciwon matarka bamuga wata cuta dazata haifarmata dawan nan ciwonba saidai abunda mukasamu wanda bashi mukayi zatoba yayi matukar dauremun kai

Yadauko takardar yana dubawa nayi mamaki sosai danaji wannan cutar wai ajikin matarka yayi shiru Usman takardar hannunsa yakarba yana dubawa jerin ciwarwatanda suke jikinta

Batada ciwon sugar Amman akwai hawan Jinie akwai maleria akwai ulcer nakarshenne yatayarwa Usman hankali yamike yana Zare ido yace doctor mehakan yake nufi??? Wannan karyane ina matata zata samu wannan cutar bayankuma munada cikakkiyar lafiya

Wannan ba result din matata bane doctor"

Doctor lawal yace kazauna alhaji nasan dolene kayi mamaki nikaina nayi mamakin hakan Amman sun tabbatarmun da cewa result dintane Amman yanzu muje taredakai zandibi jinin dakaina muje dakin awon hardakai dankagani da idonka

Yamike yawuce Usman yakasa tashi daga zaunenda yake saida doctor din yadagashi suka wuce yanabashi baki kakwantarda hankalinka

Komai zaizo cikin sauki Dan cutar batayi nisa ajikintaba inhar zata kiyaye dokokinda zamubata zata iyah rabuwa da ita gabadaya

Usman yace kamadaina furta hakan ni matata qalau take shiru doctor yayi suka karasa dakin sunsamu hajiya tazo da Abdul aka sake diban jinin lubabatu sukawuce lab tare
Yakirah khadija sukawuce tare
Akasake aunawa yatabbata lubabbatu tanadauke dacutar HIV jikin Usman neyasoma rawa ina lubabatu zatasamu wannan cutar???


Yacewa doctor ya auna na khadija itama akadibi nata ita batasàñ meke faruwaba itama aka kawo nata result din batada cutar

Usman yashiga rudanie Ganin yashiga tashin hankali doctor yasa shima aka dibi jininsa aka auna

Tunkafin afadi sakamako Usman yasan yanama da ita danyayi Imanin cewa lubabatu bayar iska bace to inazatasamu wannan cutar sai idan shine yalakamata

Toshimadai baitaba Neman mataba"!!! Yasalam kuma yasan ba khadija bace tunda gashi an aunata batadà cutar

To ina lubabbatu tasamu wannan cutar??? Amsar wannan tambayar bazaisameta abakin kowaba sai lubabatu

Muryan doctor ce tadawo dashi hayyacinsa yana murmushi yace ina tayaka murna bakada wannan cutar acikin jininka

Usman yakalleshi da mamaki kaiyadyada masa yanuna masa result din Usman yakarba yana dubawa tabbas bashida itah

Lallai dolene lubabatu tasanardashi inda tasamo wannan cutar result din lubabatu yadauka dasauri yafita doctor da khadija sukabishi dakallo doctor"" usman yabashi tausayi

Lallai dole hankalinsa yatashi Allah ma yatsareshi baikwasaba"" itakuma haryanzu khadija batagane komai ake magana akaiba


Gaisuwa dafatan alkhairi agareku masoyan wannan littafin inasake tunardaku badan nishadi nakeyinsaba saidanku amfana inasonku sosai😍😘


Aisha✍🏼
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 9 · 0% Book details