← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 28 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

36
By gentle
Lady💃🏽


Washe garima haka sainadinga wasar buya Dan banason ganinta watarana ina wajen aiki naji kawai raina yabaci kuma babu Wanda yabatan rai.
Sainaji kamar anaturani gida

Nabaro wajen aiki dasauri zuwa gida ina shiga kaitsaye dakinta nashiga tana zaune hartadauka nahucene duk da itah Batasan tayimun laifiba..

Kawai nahauta da duka kamar zan kasheta tunda nake bantaba dukan maceba wandama yake dukan matarsa kallon jahili nakemasa

Saigashi wai dakaina nadaki matata wacce nakeso fiye dakomai aduniya "" sanadin hakan cikinda yake jikinta yabare inaganinta cikin jinie Amman zuciyata tagama bushewa natsallaketa nabarta kwance yaronta sai kuka yake..


Bansan wayakaita asibiti ba danbansake wai wayartaba saidarenda Allah yakaddaro darabon za asamu wannan yarinyar.. Yayi shiru daga bisani yacigaba nayan shudewar watanni tasameni dakina muna zaune da rukayya take sanardani batajin dadi zataje asibiti

Nikuma nace bazataba daga tacemun dame zataji da wulakancinda nake mata koda ciwo kamar jiraye nake da ita nace nasaketa

Tanemi tayi idda dakinta tunda saki biyune"" kawai sainace mata tatafi Na iyar kuma nace tabarmun gida alokacin karfe dayan dare

Haka tafita nadauko muktar naturashi waje narufe gida bansan yanda suka karkareba

Tunda taga wannan aikin yayi saitakoma takarbo na mallaka""
Tamallake gidan tazama miji nikuma nazama mata"" nine dafa abinci nine wanke wanke shara wanki kai hatta gyaran dakinta ninakeyi ""

Haryakai tana karbo kayan kannenta ina wankewa" nakoma injin wanki dakarfi dayaji"" Dan zalunci dagas take girki Amman saitace wai abincin murhu yafi dadi tasani siyo itace nakoma Dan daudu

Cikin wata daya nazabge yan uwana duk wacce tazo gidan saitayi mata fata fata kuma tasa nayimasu iyaka dagidana kuma babu yanda zanyi saina korasu

Gabadaya kowa yadaina zuwa gidan har kana nan yara
Aikina tuni nadaina zuwa"" " natare agida itakuma saiyawo kamar wacce taci kafar zomo

Kai in takaice maku labari sallah zuwa masallaci ya gagareni dankuwa kayan jikina kamar na mahaukaci gefen wandona tattasai gaban rigata bakin tukunya gefen fuskata markaden kayan miya Duk yanda nabata jikina saita hanani yin wanka koma nayi wankan saidai namiyarda wadanda nacire hartakai ina kyankyamin kaina dakaina """

Ahakan aketa tafiya aboka naina dasukaga nadaina fita aiki sukazo hargida danjin ba asi tana barci sukaxo nafita kofar gida muna magana Ashe tafarka

Ta dauko ruwan wanke wanke masu daddagin tuwo damiya bamusan meke faruwaba saidai mukaji saukar ruwan ajikinmu duk Tajika abokaina sannan tazuba masu kwandon rashin mutunci Wanda kokare akaiwa wannan saiyaji badadi ballanata mutum sukuma tundaga ranar suka Dauke kafarsu dagidana.
Alokacin nagammace mutuwa da rayuwa yanda kasan Dan fursuna ni inaganima yafini danshi yanada yanci kuma zaici yakoshi nikumafa


Shekaru sunja abubuwa duk sunfaru alokacin taga haukar banza take duk tsayin shekarun nan tasan kulba Dade muktar zaidawo sannan ga faruq kenan sune zasucinye dukiyar Muhammad" aduk abunda nayi yatashi abanza Kenan


Saitaje wajen kawarta tasake fadamata damuwarta" suka sake rankayawa wajen bokansu tasanar dashi itafa haihuwa take so kota halin kaka

*hatsabibin boka* yace aitunfarko itah tayi garaje aidayanzu tayi biyar yabata maganie yace tasa inhar tasha komai yayi daidai sukayi godiya tadawo gida tanawani kankanba ita gamaiciki
Bayanshudewar watanni uku saitafara rashin lafiya tanata amai takirah kawarta sukaje asiviti akatabbatar mata tanada ciki saimurna tacewa kawarta waidatasani Aida tun shekarun baya tasanardashi matsalarta Dan itah haihuwar tafiye mata komai

Sanda tadawo tasanar dani kokadan banji dadiba banyi murnaba aikuwa tahau bala I waisanda fateema tanada ciki rawar kafa naitayi akanta wato Fateema kawaice ta iyah haihuwa tonima nayi cikin danhaka duk abunda kasan kayiwa fateema nima haka zakayimun danni Yaya biyu zanhaifa kuma duk maza

Nakalleta da murmushi nace cikin watannine dake taya zakisan abunda yake ciki macene ko namiji bakisaniba Dan babu wanda yasan gaibu face Allah

Tace tonidai nafadamaka Yaya biyu zanhaifa kuma maza danhaka komai nakeso kaine zakamun hatta wanka yanisa tundaga ranar nahau bauta tayi amai inkwashe kazanta Kuwa ko mai tsohuwar hauka ya sallama mata
.
Idan mace tanada ciki kunsan babu wanda yakaita son tasauke abunda ke cikin nata tahuta

Amman wlh alokacin nafi rukayya son tahaife cikinta kozan sarara kullum cikin lisafi nakeyi sainaga kamar ana karawa yini tsayi darekuma dazaran Nashinfida kafaduna zakaji takwalamun kira yiwannan yiwannan.

A haka akaita gurgurawa harcikin yadan taso tarage amaye a maye sai shegen kwadayi kamar kura

Indai fannin kayan kwalama kudama zasu sallama mata


Tasha wuya nima nasha wuya cikinta yana wata biyar tasoma zuwa awo saidai an tabbatar mata batada isasshen jinie danhaka tarikacin kayanda suke Karin Jinie kafin lokacin haihuwarta

Haka nayita siyen kayan Karin jinie Amman kullum tsamurewa takeyi ahakadai harcikin ya isah haihuwa ranarda tasoma nakuda da darene narasa yazanyi Dan tayi fada damakota bata shiri dayan uwana

Towaye xankirah ya taimaka mana??? Tasha wahala sosai naje makotanmu kozansamu mai taimakona duk inda nabuga kofa maigida idan yafito nafadamashi taimakonda nake nema saiya mere baki danharsu rukayya bata raga masuba


Mutum dayane nasamu yayarda yaje tado matarsa itakuma tace rukayya tayimata rashin mutunci idan maye yamanta ai uwarda bazata mantaba degiya bikice kowayayi Dan amayarmasa.. To itah batayi abunda za a miyar mataba dama irin wannan ranar suke jirah itama tadandanie abunda kowace uwa take dandana""

Illai kuwa rukayya takusa leka barzahu danko nishin kirki tadaina""


Aisha✍🏼
[4/24, 6:48 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ☠ *HATSABIBIN BOKA!!.*☠
Chapter 28 · 0% Book details