← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 31 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

40
By gentle
Lady💃🏽


Yanzun shikenan tarasa farincikin rayuwarta saurin kwabar zuciyarta tayi tace Yaya nanefa saime idan yanason wata.. Saikuma tafashe dakuka

Hakika wannan jarabawa tanada wuyar cinyewa bataganin laifin kowa saina zuciyarta datakeson Wanda babu aure atsakaninsu

Cikin kwana biyu Zainab tazabge takoma shiru shiru Sam yanxun ko magana batason yi

Kullum kasameta tana daki kwance kaleed Sam yakasa ganin walwalarta gashi gobe yakeson komawa Dan Usman yakirashi akan yadawo akwai shirye shiryenda za ayi dawuri

Yana dawowa sallar magrib yawuce dakinta yasameta tana sallah""" waje yasamu yazauna zaman jiranta itakuma tunda tafuskanci haka saitaja karatu datsawo

Bayan kuma ta idar tasoma addua wacce kaleed baisan ranar gamataba waya yajawo yasake shigewa jikin kujera yana latse katse komai yaganie oho kawai yasaki murmushi maidan sauti zainab ta ballamasa harara tace shigiyar yarinya kilanta chat sukeyi
Gashi nan sai murmushi yake nikam naleka naga meyakeyiwa wannan murmushi haka pic din Zainab ne tana karama cikin kayan makaranta tayi kyau sosai kamar wata Yar India uniform din Sundance da kalar jikinta kamar saboda itah akayisu

Kaleed yana matukar son wannan hoton ganin tayi murmushin yayi yawa kawai saita fashe dakuka kaleed hankalinsa yana wajen kallon pic din

Saida tasoma kukan yafarga dasauri yamike yana tambayarta lfy??? Tace ya kaleed waime yasa kakeson cusamun bakinciki??? 😭Dannaga yanda kuke chat shine zakazo dakina kuna magana kana murmushi

Abun saiyabashi dariys aikuwa Yakama dariya saida yayi mai isarsa zainab kam tagama kulewa yatsaida dariyar yace kekam arhar kukane dake abunda baitaka kara yakaryaba shizakiyiwa kuka

Toni ba chat nakeyiba yamika mata wayar kalla kiga abunda nake kallo kanta tasanne kasa taki kalla yace kikalla mana weety tunda kinji haushina ni kukan nan nakine banaso nalura kullum kikaganni saikinyi kuka

Dalilin hakane ma zankoma Nigeria gobe kozaki samu sauki aranki dasauri tadago kai idanuwanta dauke dawasu hawayen tace wayyo ya sultan karkatafi kabarni Dan Allah
Wlh ni auren nan ne banaso kace kafasa Dan Allah kaji Yayana"ni wlh yarinyar haushi takebani banaso ka aureta kaceewa dad bakasonta please Yayana"""

" murmushi yayi maidan sauti yace kema kinsan ban isah nace nafasaba tundahar zancen nan yashigoda manya aciki

Banda kuma abunki kinsan aure sunnar manzon Allah ne manzon Allah yanacewa acikin wani hadisi annikahu sunnaty faman ragiba an sunnaty fakad ragiba anny"" النكاح سنتی فمن رغب عن سنتی فقد رغب عنی aure sunnatace duk Wanda yabar sunnata Hakika baya taredanie mezaisa na kyamaci aure Xainab kekanki zakibani shawara nayi aure dankarna fada ga halaka kokuwa xakiso yayanki dakikeso fiye dakomai yatashi ranar alkiyama ba acikin tawagar al ummar manzon Allah ba? , (S A W)

shiru tayi tana sharar kwallah"tagirgiza kanta hakika gaskiya yafada tadago takalleshi murya raunace tace Na haukace ko ya kaleed tasoma kallon jikinta meyasa nakeyin Abu irin na mahaukata nasan ko matan duniya duka sunkare bazaka taba aurenaba koda babu kowa aduniya mukadai muka rage.

Wannan wace irin jarabawace mai wuya narasa ina zansa raina akullum nayi sallah inarokon Allah yaciremun son Yayana acikin zuciyata Amman danakwanta nafarka sainaji yasake daduwa fiye danajiya..
Nakan zauna inyita kuka ina rarrashin zuciyata Amman tanace sotakeyi inhaukace

Yayana bazan hanaka aureba kanada gaskiyarka Amman Dan Allah kacewa dad karyayimun aure wlh banason mutumen Dan Allah

Kaleed sosai zainab tabashi tausayi yanisa yana kallonta yace zainab zakisoshi kinama sonsa wayarsa datake hannunsa yadauko yakamo pic nashi yace ga pic dinsa kikalla kiganie...

Saurin rufe idonta tayi tace banason ganinsa babu wata fuska dazan kalla muddin bata yayanaba banaganin fuskar kowa dakyau face taka kajayemun shi agabana banason ganinsa..

Kaleed yace shikenan bari natura maki awaya nasan watarana xakiyi sha awar ganie yadauko wayarta dasauri dankar

Tadauke yatura mata pic din yana murmushi yasake matsawa kusa da itah murya kasa kasa yace Kanwata banason yawan damuwar nan kinsan su dad ma basajin dadin ganinki ahaka"".

Kiyi hakuri kiyarda dazabin su dad ninasan saikinyi murna dahakan zatayi magana yadaga mata hannu yace yanzune zantabbatar da sonda kikemun

Inaso kinunawa soyayyata halacci kisaki ranki kicigaba dayin walwalarki tamkar bakomai kibixabin su dad inhar kikai haka nayarda sonda kikemun dagaskene bawai kina fadabane

Shiru Zainab tayi daga bisani tasauke nannauyan ajiyar zuciya tace nayarda zanyi komai ka umurceni koda zancutu Amman kataimaka kaxauna ina ganinka
.
Kaleed yace nima naso hakan Amman akwai abunda zaikaini mai mahimmanci ina gamawa zandawo kinji Amman zandinga kiranki kullum dadare muna fira hakan yayimaki???

Dan murmushi tayi tace kayi alkawari??? Shima murmushin yayi yace nayi alkawari yamike yadorah mata wayar akan kafarta yana kallonta cikin ido cikin wani salo maiwuyar fassarawa nantake jikin zainab yamutu tayi saurin sauke idanuwanta akasa
.taku yafarayi dabaya yana kallonta saitasake dago kai

Murmushi yasakarmata mai tsada itama tamiyar masa cikin wata murya wacce shikanshi baisanshi da itah ba yace kikularmun dakanki saimunyi waya yajuya yafita

Zainab talumshe idonta wani sanyi ne maidadi taji yanabin kafofin jijiyoyin jikinta dasuke kaisako ga zuciya


Aisha✍🏼
[4/26, 7:50 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 31 · 0% Book details