← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 21 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

26
By gentle
Lady💃🏽


Sosai Zainab tabashi dariya sake kiran wayar yayi yajita kashe yayi murmushi sannan yakirah hassan suka gaisa

Yace masa ya isa lafiya??? Yace qalau " yace dad nakira Kanwata yanxun naji kamar tayi kuka me akaimata???

Murmushi yyi yace mekamata dai""" kaleed yace nikuma??? Yace kaifa bakaika padamata Neman matarda zaka aurah kajeba"" aitun sanda kabar gidan nan ko magana batayiwa kowa """ kaleed ya murmusa yace zan rarrasheta ai Amman dad tadaici abinciko???

Bansaniba saidai katambayi mamanta"yace shikenan hassan yace yakasamu mutanen gidan???

Yashafo fuskarsa yace qalau suke saidai dayar matar batada lafiya dad bakaga yanda tazamaba wajen Neman duniya takai kanta tabaro yanzun harda cutar HIV ne da itah

Yahau sallallami kunji aikin jahilci dama duk macenda zuwa wajen boka yaxama aikinta aikuwa baxatayi karshe maikyauba Allah yakaremu daga fadawa tarkon shaidan Allah yakaremana kunnuwan mu dajin sautinsa kaleed yace ameeen daganan sukacigaba damagana


Lubabatu tana saman hanya tana kuka ko acikin mafarki bata taba tunanin wata makamanciyar rana irin wannan zatasameta ba

Saiyanxu take danasani meyasa tunsanda labila take lurarda itah illar abunda takeyi tun alokacin yadace tabari yanzun menene amfanin nadamar batada amfanie tunda gashi tarasa komai..

Babu Wanda yacuceta sai iyayenta suda suka kasayimata tarbiya takwarai neman duniya kawai sukasama gaba""""
Koda takarasa gidan duk yayi kurah dagabakin kofa kadai zaka tabbatar unguwar shiru take babu mutane sosai haka tafito cikin motar tana tafiya dakyar tabude gidan sannan taja motar tashiga"""

Tunda tashiga gabanta yake faduwa saitsoro takeji towandama bai iyah Addua ba aidole tsoro yakamashi

Tanashiga falon taxauna"" tanata yan kalle kalle. daga bisani tadan gincira dantagaji dazaman

Har magariba takawo jiki lubabatu batayi komaiba tanazaune tana karatun wasikar jaki jitayi kamar ana motsi bayanta dasauri tawaiga bataga komaiba saitaga anwurga tagabanta kamar mutun gashi gidan yasoma duhu ko nepa babu mikewa tayi daniyar fita saiga nefa takawo gabaya haske yagauraye gidan tasaukarda ajiyar zuciya sannan takoma tazauna duk datanaganin haske wani bangaren zuciyarta baidaina jin tsoroba tanazaune har akai isha duhu yagama mamaye ko ina harbarci yasoma dibanta danyanzun batajin masifar kaikayi kamar da

Tasoma gyangyadi kenan saiga wutar gidan tasoma rawa kamar iirin anaruwan saman nan" "" firgigit lubabatu tafarka tahau yan kalle kalle ko mintuna goma ba ayiba kayangidan sukasoma rawa hatta fankar falon dakujeru rawa sukeyi saitaji Anfara cida gashikuma ba lokacin damunaba

Cikin kaduwa tamike tayi kofar fita dasauri kafin takai akaja kofar jikake ramm akarufe dasauri takai daniyar rike marikar kofar saitagajini yana diga ajikin abun cikin tashin hankali tahau duba hannuanta kodai yankewa tayi bataga komaiba saitaji mutum abayanta

Gabanta yahau dukan Tara Tara ahankali tasoma juyowa cikin tsoro da fargabar mexata ganie.

Ihu takwatsa Wanda yakarade ilahirin unguwar duka hankalinsu ya tashi sunji ihu Amman basusan daga inda yafitoba

Dalilin ihun lubabatu kuwa tanawaigowa tayi katari da samrat """" cikin mummunar fuska bakinta yajuye hakoranta zalan xalan taturo harshe yana dalalarda Jinie .

.idonta daya asaman goshi dayakuma bisa kuncinta lubabatu tana kwamtsa ihu samrat Tashakureta ko kwakkwaran numfashi takasayi

Sosai tashakureta lubabatu sai kakarin mutuwa takeyi dakyar tasamu takwakule hannun samrat daga wuyanta tafita dagudu tana bude wata kofa Ashe kitchen ne tafada aikuwa kamar walkiya saigakuma samrat tafito lubabatu tasoma jadabaya duk fawannan abun datake haryanzu kukatake takaici daya batasan yazatayi addua aba domin tatsira sai ihu takeyi tana Neman agajie

Mutanen unguwar sunajin ihunta sunfito kofargida Amman basu shiga gidanba dansunganshi kulle da kwado suntabbatar bakowa cikin gidan watakil sautin daga wani wurinne daban

Haka suka kare dube dubensu suka koma gidensu Amman basudaina jiyo iface iface ba" lubabatu tararumo wani kwano takwadamata akai kogezau batayiba

Komai tasamu tajefa mata Amman gabanza tasake kaimata shaka cikin lalabe lubabatu tajawo wuka talumamata gefen wuyanta saiwukar talume maimakon taga tafadi saita tintsire da dariya
Nantake tabace wata murya taji marar dadi tanacewa dagayau lubabatu kinyi Bankwana dajindadin ayanda tasanadinki narasa maatata Yayana matsayina kwanciyar hankalina duka nayi Bankwana dasu

Kema yazama dole saikinrabu dasu narabaki da mijinki yarki mahaifanki narabaki dajindadi kisani bazantaba mutuwa nidayaba dole mu mututare yanagama fadar hakan saigashi yabayyana cikin mummunar shiga take lubabatu takwallah kara tazube wajen somammiya

*************
Tunsanda kaleed yafita gidan yabar labila tana kukan nadamar abunda Taiwa Khadija


Khadija anacen ana soyewa saida akayi kiran la asar Usman yayi wanka yasauko kasa labila tana ganinshi tamike kallo daya yamata yadauke kansa yawuce bakinta tatoshe saboda kukanda yazo mata shikenan maganar ya kaleed ta tabbata dad yana fushi da itane

yana fita sukai cikibis da kaleed zaishigo sunahada ido kaleed yasanne kansa kasa Usman yayi murmushi yace inakaje tundazu???

Cikin jinkunya yace banyi nisaba nadan zagayane inga unguwar"" Usman yayi murmushi yace yazakafita kaida bakasan gariba karfa kabar gida kakasa dawoda kanka

Kaleed yayi dariya maidan sautii yace bazan bataba dad yanzun ma tareda wannan maisurutun mukatafi

Usman yace waye kuma maisurutu??? Kaleed yace Wanda yadaukoni airport"" Usman yace muhd kenan kaleed yagyada kai Usman yace jeka dasauri kayo alwala muje masallaci kaleed yace to sannan yashiga gida"

Tare sukaje masallaci kowa yagansu saiya tambaya waye dankamar tabaci yace masu kaleed ne sukanyi mamaki inayashiga tsayin shekaru harsuma suka manta dashi saiyanzu wadanda sukasan amenatu suke tunowa da itah

Shikuwa Usman cemasu yakeyi wajen Yar uwarsa yake shiyasa sukadaina ganinsa"" bayan sundawo sallah yakai kaleed hangarensa yayi wanka sukafita Yawo tare

Saidare suka dawo kaleed Rabin hankalinsa yanawajen zainab danharyanzu baisake samuntaba

Dadarema saida sukaraba dare suna firah labila kasa zama tayi acikinsu tashige bangaren lubcy idanuwanta duk sun kunburah saboda kuka

************-
Kamar an mintsileta tamike zunbur tasoma kallon wajenda take tana kallon jikinta tatuno da dalilin sumarta kuka tafashe dashi tace nashiga uku meya aikeni gashi inacikin masifa waye zai taimakeni


Kuyi hakuri kwana biyu bakujiniba banajin dadi kuma saigarashin nepa shiyasa nadaina hawama""

Nagode sosai da kulawarku gareni naji sauki sosai Allah yabar zumuncii ameeen

Sakna Adam nagode sosai da soyayyarki agareni

Salimat annuri naga sakonki nagode sosaiii


Kema tauraruwace *Aisha mai littafai* nayi katari da sakonki banada bakinda zanyi jinjina agareki saidai nace nagode sosai dakulawarki

Magana cikin sanyin murya yan uwana Allah yasa ba soyayyar novel kukemunba saboda duk soyayyarda aka dorah tubalinta akan wani dalili bamai dorewa bace

Inaso duk Wanda zaisoni yasoni Dan Allah sannan yakinie Dan Allah duk Wanda yakesona Dan saboda novel banajin nidin zansoshi banasonma soyayyar tashi

Kugina soyayyarku akan tubali nagaskiya wato saboda Allah har abada zakuga daidai bawai nishadiba inaso kufahimceni nagode nidai inasonkuu wlh saboda Allah badan wani daliliba


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 21 · 0% Book details