← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

23-24
By gentle
lady💃🏽


Gaisuwa tareda fatan alkhairi xuwa gareki takwara *AYSHA MAILITTAFI* naga sakonki Kuma nagode Allah yabar zumuncii . kamar yanda kikai addua Allah ubangiji yasa duk mai makamancin irin wannan halin tatuba tadaina domin sihiri baya dorewa duk sanda kikazama muguwar mace maicutarda mijinki babu makawa akwai ranarda zakiyi kuka da idonki

Idankuma kinada rabon shiruwa idan duniya tayimaki juyin masa saiki saduda kituba kikoma ga Allah tunda sauran lokaci

Kokinsan Allah baya karbar tuban Wanda yake gargarar mutuwa??? Hakan yafaru da fir auna lokacinda yaga bala i kirikiri yasan bazaitaba shaba
Duk wacce take aikata ta asa idan taga mutuwa fili dafili waisaita tuba dantasan tata takare wannan tubar Allah bayakarbar irinta daza ta tsilge tasamu tafita zakasamu takoma ruwa tamkarma komai baifaruba hartamanta wancen Abu

Misali idan mutum yana aikata sabo sai rashin lafiya takamashi maitsanani zakajishi yanata alkawullah idan nawarke zanyi kaza zanyi kaza

Wanima zaice indai nawarke babu shakka sainayi azumie koyace dazaran nawarke nadaina Abu kaza Amman dazaran yasamu sauki duk wancen abun yamanta idanma yafadi kwaraine wani yaji

Idan yatunamasa wane kacefa idan kawarke bazakasake yin Abu kazaba kozakayi Abu kaza saiyace kai manta kawai zafin ciwone yasa nafadi haka bakomaiba

Allah yakiyashemu Allah yasamufi karfin zukatanmu ameeen Allah yakaremu daga shairin shaidan da tawagarsa ameen


Yace kekuma menene naki aciki ??? Kotasanar dakene abunda yasameta???

Lubabatu tace ah ah Amman nasan komai Usman Hakika na aikatamaka babban laifi Wanda nasan dakyarne idan zaka yafemun

Nasan dazaran kaji bazakasake kallona da idon rahamaba taja ajiyar xuciya duk abunda yafaru agidan nan nice ummul haba isi

Nice nakesawa anakashe duk matanda kake aurah dakidaki lubabatu tasoma basu labarin komai harkawowa kan khadija

Usman jiyayi tamkar mafarki yakeyi "" tace wannan ciwon dayake jikina nice nakai kaina kuma alhakin khadijane yakamanie

Anan tasake basu labarin yanda akai takarbo maganie harwadanda sukaimata fyade dakuma yanda tafada maganin gabadaya wajen yayi tsit sautin kukanta kawai kakeji Dana labila

Usman kasacewa komai yayi danyashiga rudanie sosai

Takalleshi idanuwanta suna zubarda kwalla tace kayafemun Usman karkace zakarabu Danie wlh akankane komai yafaru soyayyarda nake makane tajawo hakan Kuma wlh nayi nadama

Wani mugun kallo Usman yawatsamata yace yanzu kikai nadama dakikaga komai yakwabe maki??? Tabbas nasan dazaki warke abunda zakiyi nangaba saiyafi wannan Allah nagode maka daka nunamata abunta tun aduniya wannan ciwon kadai ya isheki ishara dake dasauran mata masu hali irin naki

Tafashe dakuka tace Dan Allah kayafemun Usman wlh sharrin shaidanne

Murmushi yayi yace yanxun zakifadi haka baxancemaki komaiba duniyace gaki gata Allah sarki matata Ina zaman zamana da Iyalina saida kikazo kika tarwatsamun farincikina

Mikewa yayi yahausama dasauriii sukabishi dakallo baiwanie jimaba yadawo damabudan gida yajefa mata yace tashi kije gidana danake sauke baki nabakishi halak malak banason insake ganinki agidana

Kijecen kikarata"""lubabatu tahau kururuwa tace
khadija kisa baki yayi hakuri yanzun yazanyi dawan nan Ciwon katausayamun wlh inasonka bazan iyah rabuwa dakaiba

Usman yayi murmushin takaici yace Allah yawadaran wannan soyyayar taki wacce batada rana

Duk abunda kika aikata zuciyarki tabushe bakyajin tausayin rayuwa tayake kike tuna nin za aji tausayinki

Wlh koda bakida HIV baxansake zama dakeba kince soyayyarda kikemun ce takaiki wajen boka yanxun kinyi ba 1 ba 2

Datun farko kinyi hakuri kinrungumi kaddara tabbas danaje garinku na aureki Cikin mutunci kuma zanzauna dake

Duk abunda kika aikata lubabatu dakinyi hakuri dazaki samu abun nan cikin ruwan sanyi rashin hakuri dakuma garaje shine yake cutar mutane "" gashi yanxu duk abunda kike takamar kinsamu yakubuce daga hannunki kuma gayanda kika koma hakan zakimutu dawan nan ciwon

Lubabatu tace please Usman karkajuyamun baya kaima yanzun banida kowa Saikai ninasan koda naje wajen mahaifina bazai kalleniba gashi mom tahaukace

Kawayena duka sungujeni"" wacce nakeji da itah ma yautanuna mun iyakata

Usman yace kadanma kikaganie badai shaidan yabugamaki gangarsaba kintaka"" to wulakanci yanzun kikasoma ganie aiduk Wanda yasaka wani kuka bamakawa shima saiyayi kuka.

Yamike yakalli kaleed yasaki murmushi yace taso muje sama bamusu yamike Usman yaja Hannun khadija yawuce

Saida yayi taku uku yatsaya batareda yawaigoba yace kafin nasauko karnasameki agidan nan kibar ganin nayimaki dasauki wlh darajar yarki kikaci yanakaiwa nan yawuce abunshi haryanzu yanarike da hannun Khadija kam sunagaba kaleed yana bayansu.

Lubabatu kuka takeyi maiban tausayi labilace tatako indatake jiki sanyaye kamar wacce kwai yafashewa aciki

Gaban lubabatu taduke tasake fashewa dakuka cikin kuka tace mekika aikata hakan mom??? Meyasa kikabi rudin shaidan kika aikata manyan laifuka harda kisa mom

Lubabatu tace kiyi hakuri wlh yanzun nayi nadama, labila tace tunyaushe nake sanardake kuskurenki tunbayauba nake nunamaki illar zuwa wajen boka

Wannan ranar nake gudu tazo Amman bakijiba saida kikacigaba gashi ranar tazo kinyi nadama aloakacinda nadamar batada rana

Bazance Allah bazai yafemakiba Dan Allah gafuru rahimunne Amman saiyaduba zuciyarki yatabbatar dagaske kikeyi bawuyace tasaki nadamaba

Koda Allah yayafemaki mom wadanda kika cuta basu yafemakiba danbasa duniya


Yanzu gashi kinga illar yarda da makaryaci dubi yanda kika koma atunaninki soyayyace tunfarko tasaka yakemaki aiki??? Kodaya danshi yabacene shiyasa kuma yabatar daku danyasamu abokan shiga wuta

Menene ranar haihuwar irin wadan nan mutanen aduniya domin kare yaronka dagafadawa mummunar sana a makamancin wannan satane kokuma fashi da makami uwa kikasance kinacin abunda yakasance na halak karkiyi yaki halat yaki haram

Uba yarika tsaftace dukiyarsa daga cin riba bangaren kasuwancine ko sana ar hannu !" Sannan idan zaiyi aure yasamawa Yayansa uwa tagari

Aduk lokacinda zaitara da iyalansa yatabbar yayi addu a idanshi baiyiba kekiyi saboda duk lokacinda wani zairaya dare tareda matarsa shaidan yanakusa

Danyarantse shikuma duk sanda za kayi jima I damatarka totaredashi zakuyi tare zaku saka alkalaminku danashi kazuba maniyinka shima yazuba idan alokacin Allah yakaddaro Daren zakusamu karuwa kaga kenan Dan nakane kuma nashaidane

Shizaisa kaga anhaifi yaro kangararre gagare yagagari kowa har iyayensa baya shakkar kowa idan akaturashi islamiyya yayi wajen wasar banza
.
Kai wani yaron dakaganshi kasan irin shaidanne saikarantsema shaidan yayi rainonsa danbashida imanie kokadan kazo kahaihu kahaifawa mutane bala i adoron duniya

Hartakai uwa tana kuka tana Allah wadarai da haihuwarka tace dama barinka nayi nahuta dawan nan bala in wannan babban kuskurene awajenki

Kisani wannan ma kaddararkice tayiyu kema akwai abunda kika aikata sai Allah yahoraki Tawan nan hanyar

Kinazubar masa dahawaye bakisan wani babban bala ine kike sake jefa rayuwarsaba tunkinayi bayansa kinayi gabansa

Dazaran yayi Abu kihaukuka kina ni asabe wannan yaro ka asheni kamar dandan Allah banie wa iyaxubillah kinanufin dandakika roka Allah yabaki kenan bazaibaki nakirkiba?? Wannan izgiline babba

Sannan kukanki agabansa zaisa zuciyarshi ta kekyashe yaga yasa nahaifiyatai kuka aikuwa komai zai iyah

Idan kuma kina aibatashi sannu kanhankali zaisake lalacewa irinsune sukezama miyagun yanfashi marasa imanie sutareka sukarbe kayanka sannan sukasheka babu shakkun komai aransu

Basa tunanin haduwarsu da Allah totaya zasuji tausayinka bayan basajin ta iyayensu zuciyarsu tabu she babu sauran imanie ajikinta

Wanda yakeda dansauran imanin shizakasamu koda ance yakashe wani inyan uwansa sunbada baya saiyabarka

Kinga kinhaifi annoba keya gagareki kinbarwa duniya Manzon Allah Annabi Muhammad (S A W) saiyakoyar damu adduar da zakayi domin gujewa shaidan "" *Bismillah Allahumma janab naa'shaidana wajanie 'shaidana marazaktana ""
((( بشم الله. اللهم جنبنا الشيطان؛ وجنب الشيطان مارزقتنا)))


Mom neyasa kikai haka meyasa"" tasake fashewa da kuka lubabatu kamar ranta zaifita tace kidaina kukan nan haka labila abunda na aikata rudin shaidanne dakuma Neman duniya namanta Duk abunda yake rabonka saika sameshi duk hadamarka baxakataba cin rabon waniba


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 19 · 0% Book details