← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

8
By gentle
Lady💃🏽


Saurin sauke idanuwanta tayi yajaye hannunsa daga bakinta yace mom tace kindaina cin abinci"" tagyara kwanciyarta tace aikaima haka""

Yajuyo dakallonsa wajenta yace wayafadamaki banacin abinci" tace gazahiri naganie duk karame ""

Murmushi yayi yace aidolene kinkuwaji yanda naji maganganunki??? Aranar wlh nafison asa sabuwar wuka ana yankan naman jikina tsoka tsoka da naji wadan cen kalaman saura kadan nahaukace

Tace nashiga uku hauka Yayana?? Yace sosai kokina mamakin hakanne?? Batace komaiba to indai har mamaki kikeyi tokigwada watarana kiga idan ban haukaceba

Tace bama zansakeba ya kaleed banaso ka haukace yace dagaske??? Tagyada masa kai tana murmushi

Yace tashi nataimaka maki kiwanko bakinki kici abinci bamusu Kuwa tatashi yarikata yakaita toilet tawanke bakinta sukadawo dakin

Yazubamata abinci yanabata abaki sunafirah kafin dare da kaleed da zainab sunware kamar basuba tundaga ranar kaleed baisake gigin yiwa wata maganaba idan sunatareda zainab

Inma yahaduda wacce yasani sauri yakeyi yaboye karma taganshi

********
Yasaki murmushi ya laso busassun labbansa babu shakka saiya razana Zainab idan yahada wannan planning din Dan ihun murna yayi sannan yafito motar yabi sahunta danya rarrashi abarsa

**--**--**--**--**--**-

Khadija koda daya darabi tabuga suna airport din kaduna bayar Usman takirah tayita ringing ba adaukaba takirah ta labila mahaka

Mamaki taji sosai to duk suna ina??? Sake gwadawa tayi Amman basu daukaba karshe saidai sukadau tashar mota takashe kayansu da itah da zahara.u zuwa gida"" ana saukardasu tabashi kudinsa "" maidagi yazo dasauri yasoma jidar
Kayanta yanashiga dasu cikin gidan "" sauran kayan Zahara.u tadauka suka karasa ciki da sallama suka shiga khadija kam gabanta saifaduwa yakeyi

Maigadi zaifita takirashi yajuyo tace ina mutanen gidan suke??? Naga duk yayi kurah??? Yace suna asiviti Amarya

Tayi saurin tarar numfashinsa tace asiviti waye baida lafiya??? Yace hajiyace wlh Amarya idan kika ganta saikin tausaya mata takoma kalar tausayi nidanaganta wlh tashi rugawa nayi dan kamanninta gabadaya sunkoma na aljanu

Hannu khadija tadaga masa bawan nan jawabin nasakaba wanne asiviti suke""??? Yace ai hajiya muhd yana nan bari nakirashi saiyakaiki

Tace to kayi sauri tasaka zahara u tagoya anwar sukafito muhd din haryafito yabude mata baya sukashiga yatayarda motar zuwa asivitin

Lubabatu kuwa tundare da akawanke ciwon nan batasakejin kaikayiba saida safe anagama sallar asuba tasoma fizge fizge acikin barcinta sakamakon wani mugun mafarki datayi

Tanacikin daji tanagudu wadansu namun jeji sunbiyota cikinsu harda masu tashi sama cikibis tayi dawani wagegen rami fadinsa zaiyi fadin kofar gari zurfinsa kuwa zaiyi gaba ashirin

Yanaci dawuta balbal wutar tayi harso harsama dawani zaimatsa kusa dawutar ba shakka wannan wutar zata daye masa fatar jikinsa saboda bala in zafinta bama saika shigaba

Faduwa tayi tafasa ihu tana Neman agaji daga damanta wutace hagunta kuma gawadan nan mugayen halittun kowanne yabude wagege bakinsa

Lubabatu takwamtsa ihu tace bakowane awajen nan ??? Ataimakeni wazai taimakamun"" wadansu kananun yara taganie zaune suna wasa Amman babu alamar tsoro atare dasu kamarma basuga wadan nan hakittunba dasauri tamike tatunkaresu hartana kirewa tana faduwa

Gabansu tafadi guiwa kasa tana rusar kuka tace kutaimakeni zasu kasheni taresuka dago ido suka kalleta saisuka bushee da dariya gabadayansu dariyarsu tasoma amsa kuwwa acikin jejin wadan nan miyagun namun jejin suka sauka kasa Suna kallonsu

Lubabatu tasoma jadabaya dan dariyarsu tasoma tsoratata zuwa kamar mintuna biyar suka tsaya da dariyarsu take sukasoma magana

Ke axxalumace ke macuciyace Ashe kina tsoron mutuwa??? Dakina tsoronta dabaki aikata miyagun laifukanda kika aikataba

Kisani ranar bakincikin ki zatasoma dagayau duk abunda kikadade kina shukawa lokaci yayi dazaki girbeshi da hannunki yanda kika cutarda babanmu kema zaki dandani kadan dagacikin abunda kikayimasu

Dagake har bokanki karshenku yaxo mune zamuyi ajalinku bake bawarke wannan ciwon harkimutu sannan bakar azabarda zakitarar akabarinki talunka wannan dakike ciki saudubu zakiyi mutuwar wulakanci bayan kingama tonawa kanki asiri duniya tayi Allah wadarai dahalinki kibarwa kanki abunfada dake da zuri arki
.
Lubabatu zufa kawai take kanta yakulle yaran taresuke magana kamar computer sunakaiwa nan bat sukabace

Lubabatu tasoma waige tanacewa kuna ina kudawo kufadamun kusuwaye meyasa zaku kasheni kufito kusanardani menaimaku zaku cutardani wadan nan namun jejinne suka tasomata tasomaja dabaya Sam tamanta daramin dayake gabanta


Labila taganie tasheko dagudu tace mom kiyi addua"" cikin tashin hankali tace ban iyaba labila mezance?? batagama rufe bakintaba tazunduma cikin ramin zafinda tajine yasakata kwalla mahaukaciyàr kara!!


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 8 · 0% Book details