← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

4
By gentle
lady💃🏽

--**--***---***--**--*
Tamurmusa kayi hakuri banaso intayarmaka da hankali gashikuma abunda katafiyi yanada mahimmanci idan nasanardakai nasan zakadawo batareda Kayiba

Yace tosaime??? Aini lafiyarki tafiyemun komai lubabatu gaskiya banji dadiba kiga yanzu ciwon nan duk yaci jikinki dayawa indama tunfarkone baiyi tsananiba todasauki koyanzudai Alhamdulillah

Lubabatu tace tayi hakuri bazan sake aikata hakanba"" yace shikenan bakomai"" nan sukatayin firah harzuwa marece

Dadare Usman yace labila takoma gida shizaikwana anan dasafe saitazomasu da abun karyawa tace itakam bazataje ko inaba zatakwana anan shiyaje gida bataso takoma gida daga itah saimasu aikin gidan tsoro zatajie

Usman yace kinada gaskiya "" saiwajen larfe shabiyu yawuce gida yabar labila anan"" kodayaje gidan kasa barci yayi saida yakirah khadija sannan yadan samu sauki aransa sunsha firah yasake tabbatarmata gobe tabiyo jirgi tadawo gida danyanzu haka yanagida

Tace shikenan Amman baisanarda itah ciwon lubabatu ba"" sukuma acen sunacen suna firah gabadaya gidan mai martaba cike yake dayan uwan khadija harda gwaggo Husaina da yayanta duk sunzo khadija taga na ima maikamada itah""

Sainan nan akeyida su anwar haryanzu gidan babu wanda yasan ainahin tarihin kaleed ranar saiyazama kamarma anayin bukine agidan sarautar

Masarautar tacika makil tunsafe aketa shigowa dakayan alatu Na abinci dasauransu tsarabarda aka yiwa khadija kuwa saiwanda yagani da ita dahajiya kusan raba dare sukai


Al amarin lubabatu kuwa dareyanayi tasoma jin kaikayi acikin ciwon tuntana daurewa hartakasa tasoma sosawa

Duk tacire kadarda aka manne ciwon da itah saigawadansu ruwa sunafita tajikin ciwon kamar anfasa dunge ragowar inda babu kurji ajikinta shima yasoma fitarda wadansu kurajen

Lubabatu batasan sanda takwatsa ihuba labila tana barci taji ihunta Wanda yakarade gabadaya ilahirin asiviti

Duk Wanda baida nauyin kwana wannan ihun na lubabatu tuni yafarkar dashi yazama nazaune
Dasauri labila takunna wutar dakin takarasa saman gadon mom meyafaru

Saiyanxu idanuwanta suka sauka akanjikin lubcy tace Kalu innalillahi wa inna ilaihir rajiun meyasa kika cire kadar mom

Cikin kuka tace kiramun. Dadyn ki labila yafitardani kasar waje wlh bazan iyada wannan bala inba nagajie Cikin kuka take maganar take labila tafita dasauri zuwa Aron waya tasamu mutane sunyi zazzaune wajen wata Nurse taje tasamu Aron waya takirashi

Yana lazumi yajikiran wayarsa yatadakai yakalli agogo dayace karfe daya nadare gabansa yahau faduwa yamike yadauko wayar yanaganin bakuwar lamba labila tafadomasa arai

Yanashirin dauka tayanke kafin yakirah aka sake kira yadauka tareda sallama labila batasamu damar amsamasa sallamar ba tace dad kazo hospital mom ciwon yatashi gatanan saikuka takeyi" yace subhanallah toganinan zuwa

Yakashe wayar key din motar sa yadauka yafito yana kwalawa maigadi kirah shikanshi yayi nisa cikin barcinsa yajiyo Kiran yatashi firgigit yasheko dagudu ganin Usman a firgice yasaka yawartsake idonsa yace alhaji gani inafatardai lafiya

Yace lafiya maza kabudemun kofa yayi maganar yana shiga motarsa yatayar babu halin maidagi yatambayeshi inazashi Amman yasan bazaiwuce maidakinsa ceba ciwonta yatashi

Yasheka dagudu yabude masa kofa yafita aguje baitsaya ko inaba sai hospital din"" ko marfin motarsa baijira yarufeba yashiga ciki dasauri ""yasamu har lokacin lubabatu batadaina kukanba
Yatafi dasauri wajenta yace meyake faruwa??? Tace Usman wlh mugun kaikayi naji saina Sosa shine duk yatulbe ruwa dukadinga fita kalli kuma wadansu kurajen suna fitowa

Usman yadafe kansa yarasama yazaiyi "" yace waini menene musabbabin wannan ciwon?? Nitunda nake bantabajin labarin mugun ciwo irin wannan ba ""

Tayi shiru batace komaiba "" saida yasake tambaya kifadamun please dannasan ta inda zankama kirabu dawannan ciwon

Tace toyazanyi infadamaka tunda banice na azowa kainaba??? Nima haka kawai nafarka naji kwaikayi tayiyu kwarone yacijeni

Yace shikenann yihakuri bari nasa ayimun magana da doctor din idan sai anfita dake kasarwaje to
Dasauri yafita yasamu wata nurse dayake gidan doctor din yanacikin asivitin yace takirashi

Tace gaskiya baijima dawucewa gidaba Usman yace kitaimaka wlh tanacikin wani hali kicemasa nine nake Kira tace to tadauki wayarta takirashi

Tafadamasa yace togashinan tafe "" ruwa yawatsa yasauya kaya matarsa tarakoshi tare sukaje asibitin dama itama tana karatu ban garen likitanci danyabata labarin ankawo masa wata marar lafiya matar alhaji Usman

Tunda taji an ambaci Usman gabanta yayanke yafadi shinefa tabiyoshi danta tabbatarda zarginta shisam Usman haiganetaba tana ganinsa tafashe dakuka tace meyasamu Anty luba ne???

Yakalleta da mamaki yace dama kinsan tane??? Doctor lawal yakalleta yakalleshi yace kodai shine Usman tsohon mijinki kina nufin lubabatu itace matarda kikace tataimaka maki???

Suwaiba tagyada kai Usman shidai kallonta kawai yakeyi bakisake danshi baima ganetaba haryanzu lawal yayi murmushi Allah sarki kingakuwa mundade taredashi maigida nane Amman bantaba kawowa shidin kike nufiba

Usman yace waime yafaru doctor "" murmushi yayi yace bakomai"" suwaiba tace waibaka ganeniba ??? Nicefa suwaiba tsohuwar matarka saiyanzu Usman yagadota yadan bata fuska yace Allah sarki sannuko yakalli lawal yace muje Dan Allah

Tare sukawuce tanabin bayansu harsuka shiga dakin""


Aisha ✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 4 · 0% Book details