← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 12 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

14-15
By gentle
lady💃🏽


*MUMMUNAN LABARI*


Inada wata Yar uwa datayi aure totanada kishiya sosai nasan uwargidan bala ine da itah bataganin girman iyayen mijin"" atakaicedai komijin batadaukeshi abakin komaiba""

Sanda ya auri Yar uwar tawa da agidan mahaifinsa yake saiyayi gininsa danyatare tokunsan uwargida tanayin yan binne binnenta dankar ayi auren

Nikuma alokacin da akace uwargidan tazabi daki saitazabi na kurya akace Yar uwata tazauna nafari

Danaga rawarkan nata yayi yawa nace Yar uwata bazata zaunaba saidai wancen din datakeso ashetasan mugun abunda tayi

Bayan bikin wasu watanni suka shude sai tayi fadada mijin dama nafadamaku zaman hakuri yakeyi da itah naje garin alokacin nasamu tahaihu abun baizo daraiba alokacin duk Kalau suke da Yar uwata

Bayan lokacin sai Yar uwata tasamu ciki " cikin yanawata uku uwargidan tayi fada damijin haryakai yasaketa damakuma igiya dayane yaragemata

Shine tace tundahar yasaketa yakwana dasanin bashi bakara zamadawata matar dashi da aure saidai alahirah idan anayi

Yace yaji ai Allah yafita taje tayi duk abunda zatayi"" hmmm bayan barinta gidan dawadansu watanni sai Yar uwata tasoma rashin lafiya

Takumbure suntul akayita yawon asiviti abutakai har anasaida kayan dakinta ana mata maganie tunda mijin baida hali ciwo yacinye kudin

Harta haihu balafiya atakaicedai sai akamiyarda itah gidan iyayenta" "" batadade ba tace gagarinku naji mutuwarta kamar me😭 bayan kwana biyu yaronda tahaifa shima saiyabita

Bayan anyi zaman makoki an gama mijinkam baisake marmarin kara aureba saida aka kwashe shekara dawasu watanni

Yazo yayi aure suna zamansu lafiya matar tasamu ciki saiga ciwon marigayiya yabayya Na ajikinta kamardai yanda itama tasha wahalar hartahaihu akamaidata gidansu

Shine akakirah maimaganie kawunane dayaje gidan yanashiga dakin yace basuga hayaki yana fita takasan kujeraba

Sukace basuga komaiba yasa akadauke kujerar yace abashi maginie akabashi yafashe wajen yaballe daben dakin

Saida yayi Gina maizurfi saiga tarkacen kaya layu gashinkai waren takalmin Yar uwata da dankwalinta na atamfa mai golden da wani zanenta na engla"" da likafanie dasauran tarkace

Yacirosu sannan yace dole abata maganie Dan aikin yashiga jikinta akasoma karbarmata rubutu tunyaron yana jinjiri batakoma gidan mijinba harta yaye yaron

Batajima dakomawab saiciwo innalillahi wa inna ilaihirrajiun jiya bayan magrib aka kiranie akasanardani bayan la asar takoma wajen mahaliccinta

Inazakidamu duniya??? Menene ribar mace idan tacutarda Yar uwarta shinbata tunanin ranarda zatajuyo gareta?..

Meyasa mata basada hankali kawai bakin kishinki dabakin halinki kuma bakomai yake kawo hakanba sairashin tarbiya

Inada yakinin Tara bisa goma wadanda suke Neman maganie jahilaine basada ilimi uba anaso kasamawa yayanka uwa tagari wacce tafito gidan mutunci Yar datasan yakamata

Mai Ilimi da jahili basataba zama daya kaida kaga wani aikin kasan masani bazaitaba iyah aikatashiba barna darashin tausayi dakuma zalunci duka aikin jahiline shine kawai zai iyah

Zancenda nakemaku itafa tayi auren wani waje hartayi haihuwa biyu Amman saboda zalunci tahana tsohon mijinta shiyazauna data shi matar dama antusa dakarin kwana kunsan idan ajali yazo kobabu ciwoma sai anje

Ina baran adduarku kuce Allah yatonawa wannan matar asiri idan tanada rabon shiruwa Allah yashiryata idankuma batada rabon shiruwa Allah kasani kagaggauta nunamata abunta tun aduniya da itah daduk wasu matan masu hali irin nata Allah yawulakantasu kamar yanda sukeyiwa yan uwansu mata wadanda basujiba basu ganiba Allah yakaremu damu da zuri armu daga sharrin wadan nan matan ameeen

**--**--**--**--**--**-
Mahaifiyar lubabatu hannu tadorah akai🙆🏿 tafasha kuwa nikasaka??? Wlh bansakuba sainayi maganin ka macuci azzalumi sainaga karshenka dakai daduk maibaka shawara.


Ihu tasakeyi tasoma tikar rawa tanacewa yasakeni??? Baisakeniba " yasakeni??? kai baisakeniba "" tacire mayafinta tawurgar tacire dankwalin kanta tawatse gashin kanta

Waje tasheka dagudu lubabatu Ashe tasuma saboda tashin hankali"" tanafita tatasamma kofar asivitin dagudun tsiya""

Mutanenda sukaga fitowarta sukayi ihu akai Tara Tara aka kamata"" tace kusakeni inkasheshi kunajifa waiya sakeni???


Wlh bansakuba dole yazauna danie saikuma tafashe dakuka nacutarda rayuwarsa nabashi jinin hailana yaci acikin abinci yasha futsarina kuma yace zaisakeni ??? Wlh baisakeniba

Takuma shekewa da dariya tace Dan ubanku kusakeni ko insa akasheku daibayan daya inakallonku duk Wanda yakalleni saiyamutu

Saikuma tasoma gurnani tana turjewa saida akaimata allurah wani daki aka Kaita akadaureta da sarka

Lubabatu babu Wanda yasake bitakanta dan yanzu ko irin masu zama harabar wajen danshan iska sundaina saboda doyi suwaibace taturah kofar dakin hannunta yana Dade da hancinta

Takarasa bakin gadon tasamu lubabatu bata motsi takwalla kara dagudu tafito zuwa apishin lawal mijinta tafada jiki yana rawa yanaganin yamike yace lafiya suby meyakawoki nan??

Cikin muryar kuka tace naje dakinda aka kwantarda Anty lubane nasamu batamotsi batagama rufe bakintaba yaja abun awo dasauri yafita tabi bayanshi hartana hadawa dagudu

Yanazuwa yataba zuciyarta yaji tana bugawa sumane tayi ruwa yadibo yasoma shafamata take tasaukoda ajiyar zuciya tabude idonta tana kallonsu sannu kanhankali tatuno abunda yafaru

Saita sake fashewa da kuka suwaiba tace Anty Dan Allah kidaina kukan nan""" lubabatu ko saurarenta batayiba tacigaba da kukanta ganin hakan yasa lawal yayi mata allurar barci dantasamu natsuwa

Saida barci yadauketa sukafita dakin suwaiba saida tayi amai danbakaramin dauriya takeyiba saboda tanaganin mutuncin lubcy batajin zata kyamaceta kodakuwa kowama yagujeta


Bayan Usman yakoma cikin dakinsa baisake saukowaba su khadija sungama komai sunzuba Na asiviti dawanda zasuci taresukaci nasu dankofar dakin Usman arufe take

Ana kiran magrib Usman yasauko khadija tamike dasauri tace dad mungama shiryawa kaimuke jirah mutafi "" batareda yakalletaba yace zuwa ina???

Tace yahaka ??? Asibitin mana dama badanmuyi abinci kace mudawo gidanba?? Yace nayidake??? Kaitagirgiza tace Amman basai kayidaniba nasan abunda yadace

Yace tobazakuba yacigaba da tafiyarsa tasha gabansa dasauri tace dad wajen momfa zamuje bawani gurinba yakalleta kasa kasa yace nafiki sanin hakan

Kuma nace bazakiba saikifadamun menene alakarki da itah??? Khadija tarude dajin furucinsa tajuya kallonta wajen labila sutake kallo
Khadija tace please baban anwar bajimawa zamuyiba kayi hakuri idan bazakajeba mukabarmu mutafi

Tsuke fuska yayi yace waike yaushe nafara Wasa dake??? Har inace bazakuba kicigaba danacewa inadai nafiki kusanci da itah Dan matatace tokuma nine nace bazakiba karki sake yimun musu kawai kiyi abunda nace indai baso kike kiga bacin rainaba yana kaiwa karshen maganar yawuce yabarta
Baki sake tabishi dakallo"" saida yawuce tajuyo jiki bakwari tadawo wajen labila ga mamakinta murmushi tagani afuskar labila Sabanin taga damuwa

Tace sahiba lafiyarki kuwa ahanamu zuwa wajen mom kuma kiyi murmushi??? Tace tomezanyi sahiba??? Aikowa yasiyi rariya dole tazubarda ruwa tayiyu tasanadin hakan mom taga isha ra tatuba tadaina abunda takeyi

Akoyaushe. Khadija tana nunawa kamar Batasan komai agameda halin lubabatu ba aganinta cin fuskane tasanarda labila itama tasan halin mahaifiyarta

Tace hmm kedai kawai kice bakyason ran mahaifinki yabaci yanxu yazamuyi??? Labila tace mefa kawai tunda yace bazamuba muhakura zuwa gobe tayiyu yahuce Dan inajin akwai abunda akaimasa asivitin nan khadija tace kowama yamasa ai tsakaninsune baidace yashafi mom ba yanzun towaye zaikwana wajenta???

Labila tace ai hajiya tazo nasan koda alhaji Yakoma dakyar idan zatakoma saitaga yanda jikin yayi kwana biyu muje muyi sallah kinji""

Kaitsaye bangaren khadija suka nufa Dan gabatarda sallar magrib


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 12 · 0% Book details