← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 32 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

41
By gentle
Lady💃🏽


Washe gari kaleed yabaro Niger zuwa najeria "" yana tareda kewar Zainab Sam baisoma bikinsu yahaura wata dayaba Amman bakomai komai yanada lokaci

Koda ya isah gida Usman yana office wanka yayi yasauya kaya sannan yatafi office din basu suka dawoba saibayan magrib

Suna sauka gida anakiran isha i alwala kawai sukayi sukayi masallaci kaleed yariga Usman fitowa danshi yatsaya magana dawasu dattawan unguwar

Da sallama kaleed yashiga gidan labilace kawai zaune afalon tabuga tagumie Sam batamaji sanda yayi sallamarba saida yayie sallama sau uku Amman batajiba

Karasowa yayi saman kujerar yazauna kusa da itah yakira sunanta labila Amman bata amsaba saida yagirgizata sannan tazaburah harzata mike tana ganinsa tasauke ajiyar zuciya
Tace ya kaleed yaushe kadawo"""

Yace dazu darana tunanin me kikeyi??? Shiru tayi tanadan Sosa kai shikuma yatsareta da idanuwa

Tadago takalleshi yagyada kai alamar yanajinta tace bakomai ya kaleed zaune kawai nake tayi maganar ragowar hawayenda suke fuskarta suka sauko

Yace kuka kikeyi labila??? Tayi saurin girgiza kai tace ah ah bakuka nakeyiba yatsa yasa yalakuto hawayen yanuna mata wannan namenene??

Yake tayi wlh bansan sanda suka fitoba ""
.wannan yanuna kenan tunani kikeyi danashigo sau hudu inayin sallama Amman baki amsaba

Yanisa nasan dole kinada damuwa Amman hakuri zakiyi kirungumi kaddararki kamar yanda tazomaki banason yawan damuwar nan kinji Kanwata
.
Cikin muryar kuka tace ya kaleed inason ganin mom dina"" kansa yadafe 🤦🏻‍♂yace hallau kukan zakisake nafadamaki banason kukan nan please saurin gintse kukan tayi yace indai saboda ummanki kike kuka zanyiwa dad magana yakaiki wajenda take Amman sainaga kinsaki ranki tukun

Labila tayi dariya gahawaye afuskarta tace tozan saki raina kayimasa magana"" murmushi yayi yace angama ranki yadade gyara zama yayi yace Kanwata akwai wani labari dazan baki

Labila tace dagaske kaiyagyada yadauko wayarsa yakamo pic din Zainab yana nunamata. Tace wow kalli wata maikamada sahibata masha Allah Amman tanada kyau

Murmushi kaleed yayi tace kodai itane zaka aurah??? Yace um"" ta sake kallon pic din tana murmushi tace gaskiya Yayana ka iyah zabi gata sak sahibata kamar kanwarta

Kaleed yana dariya yace ashedai kinsan kama kanwartane kanin mamanta dayake Niger shine baban wannan nima wajensa natashi

Kinsan wani abukuwa.. Um um saikafada'""" haryanxu batasan nine Wanda zata auraba


Tace kaihaba Amman meyasa ba asanar da itaba??? Harynzu batasan cewa ba iyayenta bane suka haifeni tanaganin ba aure tsakaninmu gashi tana mutuwar sona tuntana karama

Labila tace wayyo ya kaleed mezaihana kafadamata kartashiga damuwa""

Yace inason bata mamakine """ labila tace duk dahaka nikam tabani tausayi kasan yanda soyayya take axuciyar Dan Adam

Kaleed yayi dariya yace nikam bansaniba Kanwata Amman yaso yake acikin zuciya kifadamun dannakaru nima

Dariya tayi tasa hannu tarufe fuskarta cikin jinkunya shima dariyar yayi yace menene abun jinkunya kinga yayanki baisaniba karnaje na kwabsa watarana

Tace nima ai bansaniba"" yace bawani idan bakisaniba yakikejin muktar azuciyarki

Wata kunyarce ta sake kamata yace inajinki yakike jinsa??? tace kamarkai nakejinsa

Ah ah kam bakamar niba Kanwata kedai kisake magana tana dariya tace dagaske nake daidai shigowar Usman tsaye yayi bakin kofa yana kallonsu khadija ma tana Kansu tundazu tasauko Amman ganin sun raja a wajen firah yasaka bata katsemasu firansuba


Sosai Usman yaji dadi aransa ganin yanda labila taketa dariya" kaleed yana ganinsa yadan Sosa kansa yamike sai lokacin labila taganshi"""

Tasanne kanta Amman haryanzu murmushine akan fuskarta sosai taji dadin firan nan da ya kaleed Ashe haka yakeda fara a"

Ganin yatashi yasa usman yakaraso yamacewa meyasa katashi kucigaba dafiranku"""

Yace aiba magana mukeyiba mungama zandan watsa ruwane""" Usman yace shikenan kayi wankan saika sauko muci abinci yayi maganar yana wucewa sama sukawuce tareda khadija

Murya kasa kasa kaleed yace kitanadi amsar tambayana yawuce yana dariya labila tabishi dakallo itama murmushi takeyi

Tamike itama takoma dakin Zahara u""" kaleed ne yasoma saukowa haryashirya cikin kaya marasa nauyi kayan sunyi masa kyau sosai"" yana saukowa yakwalawa labila kirah

Dama kwance take tamike tafito """"saman kujara tasameshi zaune laptop tana gabansa yana buga game"" tace gani ya kaleed""" yace zauna mana yana nuna mata kujera tazauna tana kallon game dinda yakeyi

Yace coffee xaki hadamun """ tace to sannan tamike tayi hanyar kitchen""" wayarsa yadauko yakirah Zainab

Kamar yasani tanacen tana tunaninsa tana fara ringing tadauka cikin fara a tayi sallama"""

Ya amsa yana saukarda ajiyan zuciya tace Yayana ina nan ina tunanin ko kakai"" dariya yayi maisauti yace saikacedai Wanda xaije karshen duniya

Tunsafe ace bankawoba ai bayan azahar jirginmu yasauka"" tace kasan bantaba zuwaba bansan nisantaba

Toki kwantarda hankalinki indai nageria ce saitakoma gidanki murmushi tayi tace ya hanya to yace alhamdulillah"""

Tace me kakeyi yanxun to"" zaune nake kawai ina game da laptop"" tasake gyara kwanciya tokaci abinci

Ke kincine??? Naci """ anya zanyarda kuwa??? Allah kakirah mom kaji yauduk suncika da mamaki ganin yanda nazage ina firah awaje yanzun ma sallah nayi nadan kwanta ina niyar zanfita saiga kiranka""

Yace basaina tambayeta ba naji chanji tayanayin maganar ki kawai"" sunyi nisa wajen firah labila tadawo taja tebur tadora masa coffee din zata wuce yayi mata nuni tadawo tazauna.

Batareda ta musaba tazauna yacewa Zainab zankiraki anjima yanxun abinci zanci tace shikenan Yayana kagama lafiya amman fa kaci ahankali
.dariya yayi yace angama Kanwata yakashe wayar sannan yakalli labila yace yanaga cup daya ke ina naki?..

au bakaine kace xakashaba yace banason insha nidaya kidauko wani cup din kiraba mana wannan"" damakabarshi ya kaleed

Um um nima bazan iyah shanyewaba yamun yawa "" zatasake magana yadan bata fuska mikewa tayi tadauko wani cup din dakansa yarabamasu yamika mata sunasha yana bata labari

Hmmm su Usman anasama anasoyewa saiyanxu akafito ansha wanka kowannensu saizuba kamshi yakeyi"""

Khadija tace kutaso muci abinci""" kaleed yamike sannan labila sukaje kan dinner din bayan sungama sukadawo cikin falon suka zauna Usman yana tanbayarsa mutanen Niger yace qalau suke suna gaidasu

Yace muna amsawa dama nace kadawone naji dabakinka ina kake sha awar zama anan zaka zauna kokafison wajen dadynka?..

Kaleed yace dad duk yanda kace aihakan za ayie ""
.ah ah bahakaba kam Amman kanemi shawaransa tukun komai yace shikenan nibanida ja"" kaleed yace shikenan dad zankirashi injie...

Shirune yabiyo baya daga bisani kaleed yace dad Usman yadago yakalleshi yace zancemakane ina hajiya take zamuje ganinta gobe"

Kai yadaga yakalli khadija sannan yajuya dakallonsa wajen labila tasanne kanta kasa"" kaleed yace please dad karkace baxamuba Dan Allah

Usman yanisa yace shikenan kushirya goben saimuje""" kaleed yace yauwa dad mungode Allah yabarmana kai

Khadija da labila sukasa dariya danyanda yayi maganar kamar wani dangoye


*Gidan mahaukata*🤣🤣🤣🤣🤣


Aisha✍🏼☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 32 · 0% Book details