← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 40 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

49
By gentle.
Lady💃🏽


Manzon Allah yana cewa

وقال رسول الله صلى الله عليه وسلم لا يدخل الجنة قاطع رحم

bazai shiga aljannaba Wanda yayanke zumunta"""

Awani hadisi manzon Allah yana cewa man kana lahu akaribu du afa"u walam yuhsin ilaihim wa yadrifu sadakatahu ila gairihim lam yukbalillahu minhu sadakatahu alayanzuru ilaihi yaumal kiyamati


Wanda yakeda yan uwa makusanta talakawa masu bukatar taimako kenan"" Amman kuma baya kyautata masu saidai yadauki sadakarsa dazaiyi da dukiyarsa yaba wani badan uwan nasaba Allah baya karbar sadakar tashi ma ana bashida lada"" muddin Allah bai karbi sadakar dakayiba aikuwa kayi gabanza "" sannan Allah bazai dubeshiba ranar alkiyama wa iyaxubillah

Abundakuma mutanenmu sukeyi yanzu kenan zakaga babban mutum kullum gidansa ana aswaki dacinyar kaza Karen gidan sama danama yake karyawa Amman jeka asalinsa kagano yan uwansa akwai Wanda xaiyi kwana biyu ba adaura tukunya agidan saba idan yatashi kyauta saikaji yaba danwani minista mota koyabawa wata miliyon daya komafi Ankara wa maikarfi karfi kenan

Wanda kodama kabashi bazaiwani godemaka ba dangani yake shimafa yataba rika wadan nan kagwada bawa Dan uwanka kagani har abada bazai manta dakaiba

Ankarbo daga aba hurairata Allah yayarda dashi yace daga manxon Allah tsira da amincin Allah sutabbata agareshi yace Wanda yakeso Allah ya yalwata masa arzikinsa sannan yakara masa albarka ga rayuwarsa toya sadarda zumunta""

Yanzu kuwa aizumunci yayi rauni banaganin laifin kowa saimu mata komai matadai komai mata!! Waime yasaka baxamu gyaraba duk abunda da yayi babban laifin Na uwane

Duk abunda Kawa zatayi Wanda yaturata kawace duk abunda miji zaiyi babban laifin na matarsane

Komai Taurinkan mijinki wlh zaki iyah juyashi dazaran yafara rarraba kayan azumi koya fitarda zakka kicemasa baban wane ina nayan tanbuwal ko ina nayan mada ko kuncin kalgo kona inama idan yayi shiru kenan babu saikice haba kaikuwa tayazakace kafitarda Abu Amman kakasa tunawa dayan uwanka maganganudai masu dadi wlh kobaiyi niyaba zakiga yayi Amman wata kokarinta kawai ataimakawa nata yan uwan yan uwan mijikuma ko oho kasani wannan matar batasonka dankuwa idan Allah yana tambayarka akiyama boyewa zatayi bama zataso kuhaduba

Menene mafita??? kagyara halinka kakyautatawa yan uwanka naka ainakane Amman yanxu kogidan Dan uwanka kaje matarsa saita hanaka ganinsa abincima kana kallo tahanaka daga itah sai yayanta saiyan uwanta kiji tsoron Allah kizama maidaura mijinki akan turbar gaskiya

Usman yace yanzu kakwana biyu anan kamurmuje zamuje wajen aiki taredakai bazan rasa aikinda zakarika yiba kabeer yayita godiya harda hawaye

Usman yace bakomai aiyiwa Kaine idan baiyimasuba wazaiyiwa bayan kwana biyu yasiyawa malam gida dasabon babur yabudamasa shago saiga malam dasabon aure😂
Saiga malam yafara kyalli makudan kudi Usman yabawa kabeer yasiye gida damota sannan yaje sokoto yadauko hajiya hannatu da matarsa yatare gidan

Itakuma sai hurar hanta takeyi danta yayi arkizi tana nan tanajiran ranarda binta zatazo Neman wani Abu wajenta saita karemata magana

Haryanzu kabeer baisanarda itah komaiba agameda Usman itadai saicin dadinta take tanasakawa maigidan kabeer da albarka addua yashata dashi da iyayensa

Cikin labila yana shiga wata Tara tadawo gida haihuwa tuni dama anmiyarda zainab saigashi rana daya suka haihu zainab da la asar labila kuma saikusan shabiyun dare gabadaya maza sukasamu

Zokuga murna wajen angwayen karni"" kaleed yatarkata Yakoma Niger"" bayan kwana biyu da haihuwar hannatu tacewa kabeer yakawota tayiwa matar maigidansa barka danya sanarda itah Yar maigidansa tahaihu

Tare sukaje damatarsa dayaransa shima ahmad da matarsa Amman bata haihuba cikine da itah danbaijima dayin auren ba
.
Tayi Yar siyayya duk Dan saboda Neman Suna saikuma akai sa a hajiya tanagidan Dan tunda labila tahaihu batasamu zuwaba saiyau""

Kabeer yakirah Usman yasanardashi gasu akofar gidan yace tokashigo mana kamardai bako yace to sannan yayimasu jagora zuwa cikin gidan

Dashigarsu da sallama hannatu tayi ido hudu da binta tajuya taga Usman zaune gakuma hafis ga kubra.

Tajuya wajen kabeer tawankeshi da mari tana huci tace meyasa kakawoni gidan wadan nan matsiyatan??? Bance Karka sake kazo gidan suba kenan koda rantsuwa nayi saidai namutu ko

Kaida nace kakaini gidan maigidanka zaka kawoni wajen wannan algungumar"" kabeer dayake rike da kumatu yana hawaye yace wannan shine maigidan nawa yayi nuni da Usman idanuwansa suna kasa yacigaba

Bansanar dake abunda yafaruba lokacinda nake tallan alewa azaria cikin kasuwa nahadu dashi shine yaxodani gidansa Yakuma daukeni aiki yabani makudan kudi nasiye gida Damota nadaukoku nakawoku nan

Mom Yaya Usman har umma basa biyarki dasharri dasuna biyarki da sharri da dukiyarsu bazatayi albar kaba Amman kedakike biyarsu dashi ina dukiyar take??? Ina kudinda kike ikirarin saikinfisu saisunzo suna maula awajenki??.

Allah bazaitaba taimakawa bawanda yakeda mummunan manufa akan yan uwansaba subasu biyarmu dasharri ya Usman sawa yayi anatayimasa cigiyarmu ana nemanmu dasuna biyarmu da sharri dabasu neme muba Amman kiyi hakuri idan nabata makirai nidai inason Dan uwana kedan kinrabu danaki dangin akan dukiya nibazan rabu dasuba Koda basuda komai kema yanzun gashi kinzama daya dasu Amman bakida mutunci a idonsu danbaki taimakesu sanda kikeda dukiyarba

Kiyi hakuri idan abunda nafada baiyimaki Dadiba"" hannatu kuka take Amman Mara sauti maganar kabeer gaskiyace binta bata taba binta dasharriba.

Duk laifin kawane itah taturata tarikajin haushin binta tacemata wai mijinsu yafison binta da yayanta ahakan yasaka take jin haushinta da yayanta"" jiki sanyaye tataka gaban binta zataduka hajiya tahanata tafashe dakuka Anty kiyafemun Dan Allah Na aikatamaki abubuwa dadama asheke masoyiyatace bansaniba hajiya tana murmushi tace bakomai hannatu nidama wlh banrikeki dakomaiba kidaina kukan nan

Hannatu tashare hawaye tace nagode Anty sanann takalli su Usman tace suyafe mata sukace bakomai komai Ya wuce tacewa su kabeer suma Suzo sunemi gafararsu

Usman yace bamasaisun rokaba anyafemasu "" sukashigo suka zauna nankuwa akabugeda fira cikin nishadi da jindadi yan uwa masu dadi

Sai dare da hajiya zatakoma tamatsa hajiya hannatu tabita sukoma kano tunda gidan babban gidane kuma bakowa agidan daga itah sai yan aiki baidace tana zama acikin surukaiba tunda akwai inda zata zauna Usman yace hakane kam

Damadai babu saita zauna haka tabi hajiya sukaje kano ranar agidan Usman suka kwana jisukeyi kamar karsu rabu"

Anagobe suna aka kawo kayan barka kayankam saiwanda yaganie khadija ma akwati goma tahadamasu labila biyar zainab biyar

Washe gari aka radawa yara suna Dan kaleed Usman lakabi khalifa Dan muktar Muhammad lakabie waleed " tarokam yayi taro tsakanin kaduna da kano dakuma Niger saiwanda yagani taro yawatse bayan angudanarda walima

Bayan sati biyu na ima tahaihu mace kwana biyu tsakani matar sulaiman tahaihu itama mace "" yar na ima akasamata Aisha humairah" Yar sulaiman bilkisu anacemata ameera

Saibayan wata uku matar dahiru tahaihu Dan itah cikinta nafarko barinsa tayi"" saita samu wani namiji tahaifa ranar suna akasamasa abdullahi

Matar ahmad tahaihu akasa sunan baban su Usman Adam anakiransa "" babangida dangikam Kansu yahadu sunzama tsintsiya madaurinki daya kowa yana girmama nasama dashi

Basa rena junansu idan abun jaje yasamu zasu taru ataya juna idankuma abun murnane Ataru ataya juna murna""
Haka akeson yan uwan juna su kasance"""


Bayan shekara biyar
Dajin *hatsabibin boka!* tun sanda hatsabibin boka yakasa samun nasarar shawokan aljana murjanatu hankalinsa kullum atashe yake bayasamun sukuni gashi su hassan saisake kusantosu akeyi

Tuni yadaina aikiwa mutane kodama kabashi aiki dakyarne za ayimaka koma anyi bayaci saboda hankalinsa bawaje daya yakeba

Safiyar talata tazama Rana maimuni awajensa danranar yanagani amadubin tsafinsa gasu husaini nan sun tunkaro fadarsa tuni hantarsa takada"" yabaza aljanunsa sunemesu asararin samaniya tunkafin su iso fadar sugama dasu haka sukatashi da azama dancika umurninsa


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 40 · 0% Book details