← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 24 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

31
By gentle
lady💃🏽


Usman baisanarda su labila komaiba"" hardare bayan sallah babu abunda yake saukodashi abinci kansa kasa cinsa yayi Khadija tayi tambayar duniya meyake damunsa saidai yace bakomai

Gabadaya gidan yayi shiru kamar ba mutane kaleed ma yanayinda dadynsa yake ciki shiya haifarmasa da damuwa

Washe gari Usman yadanji dama dama azuciyarsa bawaima wannan ba yanxu mutanenda sukasan lubcy matarsace zaiji kunyar hada ido dasu

Bayan sunkarya suka fita tareda kaleed dansosai yatara aiki company tunda yarage zuwa sosai komai yanason dakushewa

Tunsanda yadawo yasamu lubabatu ba lafiya baisake zaman kirki acenba """ gashi hadin guiwarda sukayi baimaidamasu amsaba danshi Sam yama manta

Yau akwai aiki agabansa""" koda yaje office dinsa antara masa takardu ciki harda masu Neman aiki"" tare da kaleed suka soma cika takardun masu Neman aiki yazabi wadanda yaga zasu iyah yace saigobe aimasu interview""


Labila tana kwance daki haka kurum takejin gabanta yanata faduwa tunjiya wayarta tajawo tabude data danrabonta dahawa tajima gaskiya

Facebook tahau tasoma duba abubuwanda akaturo cikibis tayi da labari makamancin Na mamanta

Amman wannan aitahaukace akace tsaki taja mata sunajawa Kansu duk wannan fa akan danamijine

Kuma duk ta karkare saikin barshi koki mutu kokuma dubunki tacika kihaukace kokuma asakeki karshedai kinaji kinagani kibar mijin kuma kinakallo yayi wani auren kekuma dake dabanza duk daya

Comments da akayi kuwa yafi dubu kowa datashi kalar tsinuwar la antakuwa tashata yafi cikin kwando

Labila tun tana iyah Karantawa harta daina takara gaba mexata gani wani posting ne kuma irin Wanda tawuto

Saikawai tabuda video din ayya Allah sarki da labila tasan mugun ganinda zatayi Dabatayi gigin budawaba saidai anriga an gama

Bayan yabude tashiga video din saiga fuskar lubabatu tanarawa tana tonawa kanta asiri duk abunda tayi maxa sai ihu sukeyi suna jifanta da duwatsu wasu suna Daukarta hoto suna Daukar gaba gareta

Labila tun tana kuka ahankali hartasomayi kwarai dagudu tafita dakin tayi waje khadija waya takeyi tana murmushi tace kashigo mana wlh bakowa mune kawai agidan

Yace shikenan ganinan tana kashe wayar labila tana kawowa tafada jikinta nashiga uku sahiba yazanyi

Khadija tace menene yake faruwa labila??? Wayar hannunta takunnawa khadija tace kalli mom kalli abunda ta aikata irin wannan ranar nayita hangomata Amman batajiba duba kiganie

Tadanna play dasauri Khadija takauce kanta ta anshi wayar tagoge video din Sannan tace menene amfanin haka su mutane wlh basada hankali

Sunsan sarai kallon tsiraicin wani haramunne to akanme zasu dauki wannan suna yadawa Allah kadai yasan dub ban mutanenda sukaga wannan

Labila ta share hawaye tace nibanga laifinsuba sahiba itace tayi abun fadi meyasa su sauran mata ba ayimasu hakanma??? Aikuma ba ita ce kawai maceba

Khadija tace duk dahaka baidaceba wadanda sukai hakan aisuma sunada iyaye kuma itama tanada Yaya Sam wannan abun baikamata as amu musulmai sunayiba

Amman natabbata wadanda suka yadashi musulmaine"" kiyi hakuri labila wannan kaddarace haka Allah yarubuto za ayi kidaina kukan nan Dan Allah

Labila tace dole nayi kuka sahiba kukama aiyanzu nafarashi yanxu aganinki waye zai aureni alhalin yasan abunda mom dina ta aikata kifadamun waye zai aureni tasake fashewa dawani kukan maicin rai

Bakin kufar shigowa taji ance nine zan aureki"" dasauri tataso dagajikin khadija takalli kofar falon

Cikin mamaki tace ya mukty"" kaiyagyada mata yace kwarai labila karkiyi mamakin jin furucina inhar zanyi aure aduniya tobanida wata matar faceke

Dasauri tajuya takalli khadija itama murmushine akan fuskarta tagyada mata kai alamar hakane""

Kanta tasaukar kasa ahankali ya tako zuwa gabanta""yaciro hankicif dinsa yamika mata

Tadago ahankali takalleshi girah yadaga mata cikin murmushi alamar takarba"" takarba tashare hawayenda suke kan fuskarta


Duk da haryanzu ta gagara tsaida wadanda suke saukowa taja majina tana mikamasa hankicif din tace nagode ya muktar Amman nasan bazaka iyah aurenaba


Samun waje yayi yazauna yace kinada dalilin furta hakan??? Tagyada kai nasan bakasan abunda mom dina tayiwa kanwar kaba

Dakasani na tabbata kallon arxiiki baxansamu daga wajenkaba Bakowane zai iyah auren Yar matarda ta aikata laifuka masu tarin yawa


Ciki kuwa harda kisan kai"" tatushe bakinta saboda kukan da yazomata

Muktar yayi murmushi yace nasan komai labila tunsanda sapna tadawo tasanar Dani Dan lokacinda tafadamun saceta da akayi nayarda

Amman ranarda naganta nasan bagaskiya bane shaida namatsa mata da tambaya Sannan tasanar danie

Tayihakane saboda ke dankarnace bazan aurekiba abunda batasaniba narigada nayi Nisan kiwo babu abunda zaihanani auren ki saidai idan kece kikace bakyasona

Banakuma fatan hakan idanma kikace banyimakiba nasan zan tabbata agwaurona danmuddin kikace bakyasona babu wacce zatasoni

Cewa wai bazan iyah aurenkiba saboda wannan dalilin ba hujja bace dankawai mahaifiyarka ko iyayenka suna aikata barna sai ace baza a auri yayansuba???

Allah yana fitarda rayayye daga jikin matacce yanakuma fitarda matacce dagajikin rayayye zakasamu malami masani mai tsoron Allah Amman acikin yayansa saikasamu fandararre gagare Wanda Sam baiyi halin malam dinba

Sautari kuma zakasamu wasu yan iska lalatattu fandararru saikuma Allah ya azurtasu da Yaya kamilallu saikuma ace baza a auresuba aiwannan ba hujja bace

Kaima nangaba zaka iya Haifar yara kamarsu kaima ace baza a auri nakaba yakenan

Yanisa nidai magana tagaskiya labila banason kowace mata bayanke nadade dasanarda kawarki haka inajin tsoron sanardake dannalurah bakyasona ko kallona bakyayi

Shiyasa nake Dari Dari"" nazoda kokon barana ataimaka akarbi tayin soyayyata!! Yakai karshen maganar yana kallonta""

Shiru tayi batace komaiba yace bakice komaiba nayimaki kodasauran gyara dariya tayi taruga dagudu zuwa sama

Khadija tabita dakallo tana dariya muktar yabita dakallo yana murmushin wani sanyi yakeji aransa koba komai yaudai yasauke nauyinda yake addabar xuciyarsa yanzu yanaji acikin zuciyarsa kamar yawarke daga jinyar shekara daya


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠

.
Chapter 24 · 0% Book details