← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 17 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

21
By gentle
lady💃🏽


Yadafe kansa dayaji yana Sarawa Khadija tace innalillahi to ina mom zataje ita dabatada lfy ????

Tace ganinan munafuka gaba dayansu suka dago kai har Usman suna kallonta"" karasowa tayi gabansu tacewa khadija Ashe kinada wasu yaran bayan wadan nan???shine kikaboyewà kowa

Khadija tasanne kanta kasa batace komaiba cikin fada lubabatu tace tambayarki nake kinyimun shiru

Labila tace haba mom yaxakiyi mata irin wannan tambayar??? Bayan kinsan wadan nàn ne yaranta nafarko lubabatu tadaga mata hannu alamar tayi shiru tace sonakeyi najii daga bakinta gaskiyane ko karya

tarage murya kamar maishirin yinkuka tace abunda yasa nakeson nasani wadansu yarane biyu sukebani tsoro sune sukahanani barci alhalin inajin barcin khadija dagaske kintaba haihuwar wasu yaran bayan wadan nan ??

Usman da labila Khadija kawai suka tsurawa na mujiya murmushi tayi mai daukar ma ana biyu tace Wanda yafadamaki haka gaskiya najinjina masa domin wannan Karon baiyi karyaba

Alokuta dadama yanamaki karya ciki kuwa harda daurewar farinciki aduniya bayankuma kuntauye tawasu taya zakaji dadin rayuwa bayankuma kacutarda wanie???

Tanisa tabbas yaranane kokinji mamakine ??? Yayanane hassan da husainie zunbur Usman yamike tareda labila sunamata kallon mamaki Usman yace khadija kina nufin kinada yara bayan wadan nan tosu waye ubansu nidai nasan budurwa na aureki totayakuma zakice kinada Yaya aiwannan zancen iskane

Khadija tace yayankane sune yayun su anwar kayi lissafi lokacinda mukadawo nayo tsaraba tosune yaranda nahaifa

Murya tanarawa yace to to inakika kaimun yarana??? Tabuda baki kenan zatayi magana wayarta tasoma ringing tadauko wayar tadauka daguntun murmushi tana kallon lubabatu

Tanarayawa aranta komai yaxo adaidai Hartana tunanin tayaxata sanarda Usman yanxukam komai zaiwarware

Tanadauka tace kunkawo??? Yadagakai yanakarewa gidan mahaifinsa kallo saiyanxu yakedan tunu yarintarsa agidan yashaki iska yalumshe idonsa yabude sannan yace ah munkawo

Tace OK kashigo ciki yanxu yace OK sannan yatasamma kofar shiga gidan" """

Khadija ta aje wayar tanabinsu dakallo tana murmushi tace mom barikiga wani abun mamakin Wanda yafi wannan yauxakisake tabbatarda rashin nagartar hatsabibi yauzakisan shidin bakomai bane bai isah yayi abunda Allah baikaddaraba tun akaina yadace kiyarda makamanki

Domin kinga darasi sainaganie shidin idan zaitsira daga hannun yarana"" labila tace waimeyasa kikehaka sahiba mahaifiyatace fa kikegayawa magana

Khadija tajuya damurmushi tana kallonta tace nasani labila danma tana mom ne nakedagamata kafa dabadan hakananba wannan ko darajar kare bazatayi awajenaba

Afusace labila tadaga hannu zata mareta kawai taji anrikemata hannu kafin tajuya tagawaye kaleed yawanketa da mari yace aiwannan kare ma yafita Dan koshi baxai aikata abunda ta aikataba

Gabadaya kusan tare suka kalleshi Usman Wanda yamike danshi yaga lokacinda kaleed yashigo fuskarsa yahau shafawa kamar yanagaban madubi waye wannan maikama dañie ????

Labiila ma bakisake take kallonsa tanadafe da kumatu tasake juyawa takalli dadynta murya narawa tace dad... waye wannan.???

Lubabatu kanta tarude idan takalli Usman tajuya takalli kaleed kowannensu tambayace abakinsa """ komawa tayi tazauna tace yayansu zauna mana bamusu yasamu kujerah yazauna yadorah kafadaya akan daya

Ganin kallonda suke binshi dashi yasa yadauko wayarsa yasoma latse latse

Usman yakalli khadija yace Deejarh kinsamu arudanie kuma kimbarmu datarin tambayoyi azuciyarmu shin waye wannan???

Khadija tamurmusa tace dama inajirane naji kokai ko mom waninku yatambaya sannan infadamaku yanzun kai baka ganeshiba???

Tajuya wajen lubabatu kema mom bazaki iyah tunawa dashiba??? Tayi dariyar jindadi tace Alhamdulillah nadade inajiran wannan ranar alkawarinda nadaukarwa kaina zandawoda kaleed gidansu yacika

Takalli Usman tace wannan yaronkane kaleed gaban Usman yabada rasss lubabatu kam saisakin fitsariii nikam nace kamar amalala kullum saifitsari kodayake nadolene dantsabar firgita batamasan sanda yake fitowaba

Khadija tacigaba shine babban yaronka Wanda kafara Haifa da matarka tafarko ameenatu mace tagari wacce kukai soyayya ta gaskiya Allah yahada kanku yadasa maku kaunar junanku rana daya akasamu wasu shaidanu suka rabaku. Harsukai sanadin mutuwar matarka wacce kakegani tamkar acikin mafarki kukai rayuwa

Dad ba mafarkibane gaskiyane katabayin aure kuma wannan shine yaronka gabadaya maganganun Khadija sukarika yimasa kuuuwa acikin kwakwalwarsa jiyake kamar anamasa magana da muryoyi daban daban

Kunnensa yadade dahannuwansa biyu yarumtse idonsa dakarfi yace karyane!""" Karyanee!"karyane!""

Saikuma sukaga yasulale kasa sume Khadija tareda kaleed sukayi kansa labila da lubabatu tamkar mutum mutumi haka suka koma.

Khadija tasoma jijjigashi tana kuka kaleed yace samomun ruwa please dasauri khadija tamike hartana faduwa tadauko ruwa takawo masa yaballe murfin ya yayyafa masa Sannan yashafamai afuska

Usman yasaukarda sassanyar ajiyar zuciya yabude idonsa ahankali yakalli Khadija wacce fuskarta Duk tajike da hawaye tana masa murmushi

Yajuya dakallonsa wajen kaleed yalumshe idonsa hawaye sukazubo masa tagefen ido hannun kaleed yalalabo yarike kam cen kasan makoshi yace kaleed

Cikin sanyin murya yace Na am dad Usman yafashe dakuka kamarwani karamin yaro


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 17 · 0% Book details