← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

5
By gentle
lady💃🏽


-- tayi matukar firgita dataga yanayin yanda lubabatu takejin jiki tatausaya mata ita kam batakoma kantaba dan abunda takeji bazaibar tama iyah gane mutaneba

Doctor din yaduba ruwanda suke fita wajen yataye tamkar wacce takone kuma abun Yakoma kamar kuna dabadan shine yayi aikin dazuba dazaice wutace takonata haka abun yayimatukar bashi mamaki

Lubcy takatsemasa tunani dacewa doctor kataimaka karabani da wannan bala in wlh zan iyah mutuwa

Yanda nakeji ajikina kataimaka kaciremun wannan ciwon"" yadago yana kallon Usman duk shisuke kallo suwaiba da labila dakumashi Usman din sunajirah suji tabakinsa

Yanisa agaskiya alhaji bansan mezancewa wannan al amarinba Abu kamar shirin film yanzu ciwonta yanuna kamar takonene harsuna fitarda miyagun ruwa

Tayiyu sosawarda tayine danhannu define dashi"" baidace kubarta tana sosawaba bari nasake wanke mata Amman karkubari tasosa zuwa safe zansa ayi awon jininta muga tayanda zamu bullowa lamarin

Yafita dasauri basuwani dadeba yadawo tareda wata nurse mai duty aka sake wanke ciwon akasa maganie saitaji Dan sauki har barci yadauketa

Saida tayi barci doctor din yajona mata wasu ruwan da allurai wadanda yakesaran zasu taimaka wajen make kurajen sukaimasu saida safe usman yace yagode

Bayan sunfita yasamu waje yazauna yakuramata ido gabadaya lubabatu tasauya kamar ba itah ba rayuwa kenan lafiya qalaufa yabarta amman yanzun yadawo yasameta gatanan dai

Labila ma gefe takoma tabuga tagumi kowannensu dakalar abunda yakesakawa aransa"" hargari yawaye lubabatu bata farkaba barcinta takeshaka

Khadija kam anacen anata shirin komawa Nigeria kaleed tunda safe yatafi gidan yadauki anwar sosai yanason yaron harcikin ranshi tunkafin yasan babansu daya yasan sosai zaiyi kewarsu idan sukatafi

Karfe bakwai nasafe tagama shiri danbataso tayi tafiyar rana motoci kusan guda bakwai akacika za aimata rakiya kamar wata sarauniya

Sunashiga airport akabasu waje ganin motocin mai martaba"" dama an gama shiryamata komai saibatun shiga jirki dansaura mintuna goma yatashi

Tayi sallama dasu tana kuka maimartaba yahadata dawata kuyanga zaharau dantarika taimaka mata da yaran tayi godiya sosai sukayima addua dafatan Allah yatsareta daga sharrin mutum da aljan

Tayita godiya jitakeyi kamar kartabar danginta yan uwa masu dadi"" kaleed yanagefe yana kallonta"" dasun hada ido saiya saukarda kansa

Matsawa tayi kusadashi tace kayi hakuri yayansu nasan kanajin wani Abu azuciyarka tayiyu haushin mahaifinka kakeji dukda kasan bashida laifi

Nidai inasake baka hakuri amadadinsa kayi hakuri naba hajiya number ta saika karba komai kakeda bukata kasanardani insha Allah zanyi kokarin ganin naturomaka dazaran angama komai zansanardakai koma nazo dakaina mutafi tare

Baice mata komaiba tajuya tawuce zainab tanakallon yanayinsa yasauya saitaji wani iri kallonta yayi yakawar da kansa gefe Sam bazai sanarda Zainab damuwarsaba

Yanaso saiyaga mahaifinsa tukun duk abunda zaiyi inhar babu ubansa awajen aidasauransa"" harjirginsu khadija yabace Asama kaleed baisaniba yayinisa wajen tunani

Muryar Zainab yaji tace ya muje tayi maganar tana zungurarsa da kafada "" yadansaki murmushi yace meyasa zakitureni inda nafadi kumafa???


Ta kwalalo ido 😳faduwar lafiya Yayana gudanawa nake dazan iya tureka saikace Wanda bayacin abinci🙄

Dariya yayi maidan sautii tace waiyaushe sukawuce??? Yayi maganar yana kallon gefensu dabaiga duka moto cin gidansuba

Tamere baki yaushe zakasan suntafi kanacen kana bakin tunaninka tamurguda baki daidai sunkai bakin motar yabudemata tashigà shima yazagaya mazauninsa ya zauna

Yana fuskantarta yace waye yafadamaki tunani nakeyi??? Tace baga zahiriba naganie ninarasa gane kanka tunsanda Anty khadija tazo kasauya kwata kwata

Sam kadaina sakemun fuska damekakeso inji da soyayyarka kokuma dakyaluwarda kakemuñ???

Dankulanin dakakeyi inàjin sanyi araina kadaina saigahawaye sharr kamar anbude fanfo kaleed yakuramata ido yanaji kamar yajawota jikinsa ya rarràsheta

Amman babu halinyin hakan danzai iyah shiga wani yanayin dakyar ya iyah furtamata Kalmar sorry

Tadago jajayen idanuwanta takafeshi dasu tace menaji kafada ya kaleed hakurifa?? Atunaninka Kalmar hakuri zata iyah tasiri azuciyata??? Inazargin anyama bakasoma soyayya dawataba???


Ninakasa fitarda miji saboda soyyyarda nakeyi maka duk danasan kayimun nisa dankoda babu maxa aduniya bazaka taba aurenaba

Kaleed yace injiwaye yafada maki??? Karkiyi mamaki nangaba zamu iyah zama miji damata

Murmushin yake tayi tace hakan zai iyah faruwa ammanfa ashirmen tunani ko mafarki Dan babu inda natabajin Yaya ya auri kanwarsa

Kaleed yace inamai tabbatar maki za afara akanmu kisa wannan aranki watarana zansake tambayarki yakika ganie tabbas saimunzama miji damata wannan alkawarine yayi maganar yanatada motarsa

Baki sake take kallonsa danganie takeyi kamar yazare a ina yatabaganin wannan kwamachalar uwadaya ubadaya

Saikace wadansu jahilai aiwannan ko ajahiliya dakyar idan anyi hakan"" nikam nace anyikam tunda harma zamanin jahiliya DA zai iyah yingadon uwarsa idan mahaifinsa yarasu yadauki matar wacce tahaifeshi acikin gadon abunda akabarmasa

Lokacinda mata basuda wani yanchi saikuma shima yacigaba dakwanciya da itah zuwan musuluncine yahana wannan akayiwa mata gata Allahu Akbar

Allah mai iko Hakika musulunci bakaramar gata yayiwa mataba gashi yanzun saida kudi ake daukarmu

Tunda sukahau hanya baisake cewa komaiba saidai jefi jefi yakandan juyo yakalleta danyasan tana nan tana saka maganarsa acikin zuciyarta


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 5 · 0% Book details