← Book details Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 41

PART 2⃣

Hatsabibin Boka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

32
By gentle
lady💃🏽


Yasaukarda ajiyar zuciya yana kallon khadija yace akwai bukatar inga dad Dan dawuri nakeso ayi auren nan

Khadija tace kaiya muktar inkashirya mubamu shiryaba ai """yagyara zama wanne shiri kenan??? Ninadauke maku komai.

Tace munji Amman saimun shirya wlh yace waishirin me zakuyi kayan sakawane dakuma shirye shiryen buki cikin sati kungama komai

Tace mudai ah ah kuma so akeyi ayitareda na yayansu"" muktar yace tonidai karkiyimun tsiya idan akanemeki shawara kice sati biyu kinji Kanwata duk shirinda zakuyi aikun isah gamashi
..
Tace to yace kokefa inasu sapna banji duriyarsu ba"""??? Tace sunanan kuwa Bari nasa akawosu takwalawa Zaraha u kirah ta amsa tazo dasauri Khadija tace daukomasa sapna tace to tagaidashi sannan takoma daki

Yace Yar raino akasamo maki?? Tace um um daga Niger nazoda itah kaiyagyada daidai fitowarta taduka tabashi sannan takoma yace wai yanmatana tagirma sosai inasu anwar din Zahara u ce tasake fitowa tareda su anwar""

Yadorasu akan cinyarsa"" sai kallonsu " yakeyi Suna burgeshi jiyakeyi kamar yahadesu"" inama yayansane""" yanatayi masu wasa" khadija tana kallonsu saida akasoma kiran azahar yatashi"yamika matasu yayi alwala yawuce masallaci

Takira Zahara u tadaukesu tashiga kitchen tadorah girki"" sannan tahau sama dakin lubabatu" tashiga" labila tana kwance tarungume filo saijuyi take tana murmushi"'" tanaganin khadija tarufe fuskarta da tafin hannunta""

Duka khadija ta danamata abaya tasaki Yar kara

Tace haba sahiba menene haka daxafi wlh"" khadija tace ainasani dankiji zafin nadakeki banda iskanci Yayana yana tambayarki kinwani rugowa daki me kike nufi???

Murmushi tayi tace wlh kunyarsa nakeji sahiba mezance to??? Khadija tace ra ayinki zakifada akansa mana"" tace wanne ra ayi aikema kinsan inasonsa""

Khadija tace wa badai niba yaushe kikai danie kinasonsa"" labila tace kesahiba aibasai nafadaba daga fuskata dayanayina zaki gano tatashi zaune tana fuskantar khadija tace batun yauba nake fama dasoyayyar sa sainaga kamar shibana cikin tsarin matanda yakeso

Shiyasa banason zama guri inhar yana nan dankar xuciyata takarasa makancewa Amman sonda nakeyiwa ya mukty bazai faduba

Khadija tasaki murmushi tadafata tace nasan haka dagake harshi ainagano take takenku idanu kawai nazuba maku karshe saigashi yafito fili yasanar danie kinga kitashi kiyi wanka kishirya kafin yadawo sallah

Labila taturo idanu tace tome zanyimasa kina nufin akwai maganar dazamuyi????

Sosai sahiba akwai bukatar Ku tattauna ku fuskanci juna"" labila tace nidai ah ah"

Aikuwa baki isaba aini bahakan nayiwa dad ba 😕danhaka bazakiyiwa yayanaba"" tamike taja hanunta yauzan maidawa kurah aniyarta nima zanyimaki kwalliya kamar yanda kikamun

Babu yanda labila batayiba Amman saida khadija tasata gaba tashiga wanka itakuma tayi alwala tayi sallah

Takoma tadibo abincinta data Dora tana fitowa yanashigowa da sallama"" cikin fara a ta amsa harkadawo ya muktar

Yace ah wlh yana samun wajen zama yakirata tazo tazauna Murya kasa kasa yace yazanyi naganta inason nawuce

Khadija tace yanzun kuwa zan izomaka keyarta" tamike harzata wuce yace kidaiyi mata ahankali karki wahalarmun da itah

Tana dariya tawuce tashi yayi yafita saman kujerun dasuke harabar waje yazauna yana jiranta""

Khadija koda taje labila tashirya Amman tarasa kayanda zatasaka "saida khadija tazabomata wasu kayan kantine Riga da siket sunhadu sosai tasaka tasa farararen takalma da farin hijab"

Khadija tariko hannunta sukafito taduba bataganshiba tace nasan yafita saiki karasa Amman bari nabawa Zahara u abunsha takaimaku

Labila tawuce kamar wacce kwai yafashewa aciki tafiyarda takeyi saita bada wata ma anar daban kamar tafiyar yanga takeyi""
Tunda tatunkaro wajen yafara tasbihi ga Allah yakasa dauke idonsa akanta harta zauna fuskarta tana kallon kasa "tace inawuni yaja ajiyar zuciya yana fuskantarta yace lafiya qalau yagidan

Cen kasan makoshi ta amsa saikuma shiru yabiyo baya nayan dakiku muktar yakatse shirun tahanyar magana

Labila yakirah sunanta ta amsa batareda tadagoba"" yacigaba zansake gabatarda kaina awajenki magana tagaskiya maganar aure takawoni ba wasaba

Nadade ina jinyar sonki acikin zuciyata saiyau nasamu damar saukeshi Amman banji tabakinkiba shinnayi maki??? Shiru tayi """ yace eh ko ah ah yakamata ki amsamun tambayar nan

Dankarki cutarda kanki alkawarinda kuka daukarwa kanku kumanta dashi kifadamun ra ayinki nasan kumata kunada naku ra ayin tayiyu banacikin jerin mazajenda kikeso ki aurah

Naga mata wata zatace tafison fari wata baki wata maitsayi wata guntu wata maidogon hanci watakuma tafison mai gutsurarren hanci wata siriri watakuma tafison maikiba toke wanne kikeso aciki???

Cikin jinkunya tace Wanda yatara dukkanin abunda kakedasu"" bakinsa harkunne yace kenan ankarbi kokon barana???

Tace tunkafin makaroka akabaka"" yanxu shaidamaka nekawai akayi muktar baisan sanda yafurta alhamdulillah ba jiyakeyi kamar ana shawagi dashi saiwani kallo yake jifan labila dashi maikashe jiki

Zahara u ce tayimasu sallama ta ajemasu kayansha sannan takoma cikin gida "" labila haryanzun kunyar muktar takeji sunfara fira jefi Jefi Amman yawan maganar duk muktar keyi Dan batacewa komai

**-***---**---**---***-

Tafe suke cikin mota suna tafiya Wanda yake daya mazaunin yayi shiru yabuga tagumie daganinshi abun duniya yadameshi

Bayan motar wata matashiyar yarinyace zaune alamu sun nuna tana dauke dakaramin ciki danyadan taso yakara mata kyau farace Amman basosaiba

Mazaunin driver kuwa wani kyakkyawan saurayine mai kamada muktar yanayinsu iri dayane saidai shi yanada dan duhu sosai Sabanin muktar dayake fari

Amman dakagansu babu makawa zakace sunhada jini daya suna shiga garin kano dattijon dayabuga tagumi shiyasomayiwa maitukin kwatance

Harsuka kai unguwar saidai gabadaya komai yabace masa sukatsaya yafito yayita yandube dube Amman baigane komaiba

Matashinne yafito yace Abba idan bazaka ganeba muyi tambaya mana yasunan maigidan"??? Dattijon yayi shiru daga bisanie yace malam garba sunansa"

Inajin nan ne kawai sanadin gine gine da akai dahanyoyi wajen yabace mun" saurayin yace bari natambaya gawani cen zaishiga gida"

Dasauri yakarasa wajensa yana masa sallama hafis yawaigo yana kallonsa aransa yace wannan kamar muktar??? Saurayin yabashi hannu suka gaisa yace Dan Allah tambaya mukeyi

Hafiz yace Allah yasa nasani"" saurayi yanisa yace gidan wani malam garba"" Hafiz yayi shiru daga bisani yace akwai masu suna malam garba dayawa a unguwar nan saidai kafadamun sana arsa

Yace gaskiya bansan sana arsaba Amman yanada yaro muktar Hafiz yace haka kam naga kunyi kamada muktar sosai kamafi yanayi da Khadija""

Saurayin yayi murmushi yace yayanane ai nisunana faruq wancen mahaifin mune yayi nuni da dattijonda yake kishingide jikin mota yana jiransa

Hafiz yace Allah sarki kunbaro gidan baya kadan" faruq yace kozakadan taimaka kakaimu gidan??? Yace aibadamuwa bari nadauko mota Dan akwai Yar tafiya kadan wannan gidanane

Faruq yayita godiya Hafiz yace bakomai ai yashiga gidan yadauko motarsa yashiga gaba faruq yaja tashi yabi bayanshi


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 25 · 0% Book details