← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 80

Sashe 8

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Tanko ya fada Bakinshi sai rawa yake yi Da Sauri ya Fita daga dakin ya tsaya kofar Dakin Lantana,Daga Waje yace"Lantana ki fito ,Suwaibah Allah ya karbi Abinshi, Burinki ya cika"
Yana gama Maganar Yayi waje Cikin Zafin Nama,Bakinshi dauke da Addu'oi Ga Suwaiba Matar Arziqi

Da Sauri Lantana ta bankada Labule,ta fito kamar gaske ta tsaya tsakar gidan Tafashe da ihu! "Wayyo Mun shiga Uku! Ihu! Take Sosai Sai kace Mahaukaciya ,Cikin Ziciyarta Sai murna take

Nan Makota suka dinga Shigowa Cikin tashin Hankali ,Masu kuka nayi masu salati nayi ,kar dai Lantana taji Labari

Malam Suka shi go dashi da Liman da Sauran dattawan Unguwa,

A ka sutturce Suwaiba a ka kai ta gidanta Na gaskiya, Sosai mutuwar ta ta ba zuqatan Mutane banda Lantana da yaran ta

Bakin ciki Kamar yakashe Lantana Lokacin da ta Fahimci Da Namiji Suwaibah ta haifa,suka riqa tsara yadda zasu kashe jinjirin ita dasu Sallau,Fahimtar Hakan yasa Malam Tanko ,daukar jinjirin Bayan kwana ba kwai ya Miqashi ga Gwaggo Shattu ,yace ya bata Amana

Gwaggo tace ta karba Allah ya tayata riqo ,A lokanci A kwai qan warta da take Shayarwa sai ta bata,Jaririn Wanda yaci Sunan Ayuba,da zumar in ta yayashi Sai ya dawo Hannuta,

Lantana taji ciwon Abinda Malam Tanko yayi ,nan ta Sanyashi a gaba ta rika cin mutumcinsa bai ce Mata komai ba

To A taikaice dai rikon Ayuba ya dawo Hannu Gwaggo Shatu yana da Shekara Uku ,Sharasa Bakwai a duniya Allah ya dauki Ran Malam Tanko Sakamakon Rashin Lafiya tafarar daya,

Ayuba ya shaqu da Mahaifinshi Sosai Shiyasa Yaji Dacin Mutuwarsa,inda Kiyyaya da tsana gami da tsangwama,ce Tsakaninsa da "Yan Uwansa don ko da a kazo rabon Gado Sallau da Lantana ,Cewa Sukayi Ayuba Bashi da gadon Ubansu Domin Ba Dan Halak! Bane ,Sai da Malam Liman ya tsaya tsayin Daka A kan Lamarin Sannan A ka fitarwa da Ayuba gadonsa a gidan Ubansa.
Duk Rayuwarshi gidan Liman yake yin ta ,inda ya kasance *Yaro* mai zafin Nema,a wancan lokacin duk Abinda ya ta6a sai ya zama kudi.

Sallau ya sakoshi a gaba Da bakin ciki da hassada ,duk inda yasan yana zuwa Nemansa sai ya je ya batashi.
[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: 🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀

*✍🏻Writting by*
_Binta Umar_
*MAMAN ABDUL WAHABU*

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_🤝🏻

*🅿18*

_Bissimillahi_

A lokacin Sallau yayi Aure inda ya Auri "Yar yayar Lantana Mai Suna Fatsima suna kiranta da (Uwa!) Yarinya ce Mara kunya inda bata ganin girman kowa ,babba da Yaro ,Har Mahaifiyarta fito Na fito take da ita,Bata da Aiki sai yawon tallace Tallace to har a kayi Auran Uwa Na fita kofar gida ta dasa kasko Na suyar Awara gefe ga gyada nan cikin Faratin A quq-qulle a leda marau da tubes! Haka take Tara matasa ai ta shirme ,idan har kan dillanci tazo nan ma tana tabawa
A takaice ita ce take ciyar da Sallau domin shi ya zauna zuciyarsa A mace yaqi ya fita ya nema ,Gwara Maman shi ya kan fita yayi buge bugensa ya samu Na kashewa,ita ko Lantana Kasuwanni take bi tana tallan zogale da kuli ,Da wannan suke Samun Abinda zasu kai bakinsu.

To shiyasa daga Lantana Har Sallau! Suka taso Ayuba a gaba da kyashi gami da hassada,Wanda hausawa sukance (Hassada ga mai rabo taki ce)

Ayuba ya shaku da "Yar Uwarshi Atika ,domin duk wani Sirrin shi tasani ita da Gwaggo Shatu marikiyar shi ,

Haka ya cigaba da Rayuwa ,tare da Kiyyaya da tsangwama gurin "Yan Uwanshi,Amma duk da Haka shi bai fasa Zumunci da su ba,

Hafsatu ita ce Ayuba ya Amince da tazama Uwar "Yayanshi, Domin ya yaba da tarbiyar ta gami da nutsuwa da kamun kai,"Yar Makotan Su Atika ce Yayarshi Ita ma haifinta ya rasu,to haka dai Malam Liman ya tsaya Masa tsayin daka ganin Tabbatuwar Auran

Nan ta tare gidansu ,Bangaran shi Na gado,Uwa da Lantana suka ce dawa Allah ya hadasu,suka sanya ta a gaba Babu irin Muguntar da basai Mata,yarinyar duk ta kwar zane,kullum cikin Aikin Awarar Uwa take tamkar ita take Auranta,inda Allah ya tai maketa ma ,Lantana,bata yini a gida Sai Yamma take dawowa daga zarar ta dawo ,zatai ta kwala Mata kira tana zagi! Tai ta sanya ta Aikin Wahala ,ko da ta Samu ciki basu bar ta ta huta ba, Kullum idan Ayuba ya shi go gidan yaga irin wahalar da take sha,sai bakin ciki ya kamashi gashi bashi da Bakin Magana,Lantana ta tsigale shi, Kullum in sun shiga daki yai ta Rarrashin ta yace"tayi hakuri Shima ba yason Wannan Wahalar da take sha Da yana da Hali da sai ya kama mata Haya ko daki guda ne,to Babu Hali domin duk wasu hanyoyin Samunsa Sallau ya shiga ya fita ,ya rabashi dasu da Asiri da kuma Ziga ga Mutane ,cewar kar Wanda ta hada hurda dashi domin ko ba Dan gari ba ne,Zai cuce su ya gudu

To Lokacin A kwai qarancin Ilimi gami da Wayewa Sai Jama'a suka dinga gudun Ayuba,
Tunda ga Lokacin ya dai na sana'a sai dai ya fita tayi buge bugensa ya dawo gida

A lokacin Uwa! Tana da Yara Biyu Namiji da Mace'Iro da Shamsiyya, To iro tun yana shekara Uku ya iya yawon Talla kusfa kusfa,haka zata kasa masa a faran ti tun Safe ,ba bu Maganar zuwa makaranta
Haka ake Zaman doya da Manja a gidan Domin Maman ma ya yi Aure shima Matarshi Na gidan , Mai suna Halima inda ta kasance mace mai sauqi hali gami da Hankali ,kwata kwata bata kaunar Abinda Su Lantana sukewa Hafsatu Matar Ayuba ,sai ta riqa Jan ta a jiki tana tausar ta,nan ko Uwa!! Tace dawa Allah ya hada su ,shiga fita Dari sai ta Zubda musu Ha baici ta dauki gaba da Halima ,duk dai a kan tana kula Hafsatu,ita ko Lantana dama Macace mai mugun kwadayi kasan cewar Maman duk ya fisu Samu yasa bata son Laifin sa ko Na Matarshi shiyasa ta kyale ta take Kula Hafsatun Dan kar ta dai Na bata Abinci da kayan dadi in Maman ya siyo Domin ,shi kwata kwata ya Manta da wata Lantana ta Matarshi yake,in Anyi Magana yace ai tana fita Nema taci da Kan ta,shima yanzu Nauyi yayi masa yawa.

*Allah ka azirtamu da "Yaya masu Albarka ,duk Dan da zai zame mana fitina a rayuwarmu Allah kar ka bamu,Allah ka sa mufi qarfin zuciyoyinmu*

*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
08089965176
[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: 🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀
*🐾GIMBIYA BALARABA🐾*
🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀

*✍🏻Writing by*
_Binta Umar_
*MAMAN ABDUL WAHABU*

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_🤝🏻

*🅿19*

_Bissimillahi_

Cikin Hafsatu ya isa Haihuwa , Halima Matar ,Maman ce ta tsaya Mata a gidan Lokacin Gwaggo Shatu babu Lafiya Abinka da jikin girma, Iya" Atika ita ce ta karbi Haihuwar ,su Lokacin Domin Lantana ta tafi tallanta Hakanan Uwa! Na waje tana Soyar Awara Tamkar ba matan Aure ba
Cikin ikon Allah ta haifi diyar ta Mace Sak! Mahaifinta Kamar an tsaga kara dashi Fara tas!! Ga hanci har baka, Ayuba ya ruqa Murna ,A take yayi wa jaririya huduba da Sunan Mahaifiyarshi, wato Suwaibah ,sai ya ke ce Mata Balaraba kasancewar An haifeta ranar Laraba

Ko da Lantana ta dawo taga jaririya tace ,Haushi Kamar ya kashe ta ganin Baiwa da kyau da Allah yayi mata ga Hafsatu Lafiya lau,ita San samun ta Hafsatun ta mutu kamar yadda Suwaibah ma ta Mutu , A ranar kwana tayi tana zage-zage Kamar ba tsohuwa ba,

Ita ko Uwa!! Tsabar kyashi bai bar ta ba ma ballan ta ta shi go ta ga Abinda Hafsatu ta Haifa ,ta dai tura Iro gulma! Domin yaje ya gano mata ,Aiko Yaron ya dawo Yana Fada mata kyawun "Yar jinjinyar ,Bakin ciki kamar ya kasheta,ta waiwaya ta kalli Yarinyar ta Shamsiyya,a zaune ,duqun duqun!! Daga ita sai karamin ,Wando ga Wani Uban zarni! Da take yi,Yarinyar Baqa ce Sosai gashi Mummuna Dan Har Iro yafi ta kyau tunda shi ya Dan dauko kammanin Mahaifinshi,ito ko Shamsiyya Kamarsu daya da Uwarta!

Nan taci Alwashin Sake Haihuwa ,Domin tana Zaune Wata baza tazo tafi ta "Yaya a gidan Ba, kuma in sha Allah ita ma sai ta haifi Fari ,sabida Sallau yana da Haske dai-dai gwargwado

*Ni ko nace kuji ni da Uwa! Da tsabar jahilci don Allah*🤣

Har a kayi Suna Uwa! Da Lantana basu leqa sun ga Abinda a ka Haifa ba,Balle Sallau" Wanda ya tsiri gaba! Da Ayuba babu gaira babu dalili ganin yadda yayi komai Na Haihuwa ,Hatta hakika, biyu ya yankawa Maijego,shine yake Bakin ciki ,yana tunanin a ina ya samu kudin da yayi wannan Hidimar
****
Kafin Hafsatu tayi Ar'ba'in Uwa! Ta samu Ciki sai tun qaho take tana hora hanci ita zata haihu ,Shiga Dari fita Dari sai ta yadda Habaici tamkar Wacce bata taba Haihuwa ba ,Ita ko Hafsatu bata ce Mata komai ,in tagama Ai kace Aikacen ta ,sai ta tafi bangaran ,Suyi zamansu Har Magari ba

*Balaraba* ta saba da Halima Sosai in Kusan Kullum tana Hannunta ,in ko bata gurinta tana can gidan ,Iya Atika, Haka jama'a suke Kaunar ta daga An fita da ita kowa son ta dauke ta yake,Sabida farin jinin ta, Uwa! Ko babu shiri ta bazama, Gurin Malamai a kan Yarinyar ,Wai a Sanya Mata Bakin jini a ida nun Jama'a kuma a saka Ta ta fandare ta zama ga gararriya, Malamin nata yaga Tsubbu bace Tsubbacan Sa ya yi Mata Baya nin Yadda zata yi da kayan Aikin da ya bata Mutukar ta kuskure to babu Makawa "Yayanta zasu Lalace domin Aikin kansu Zai kuma,

Haka ta dawo gida tana Haki ga tsohon Ciki a jikinta, Sai da ta bari dare yayi Sosai kowa ya shige dakinshi ,sannan ta Fito ta daga Manyan dutsinan da suke girgi dashi ta tona Gurin da Wuqa yayi zurfi Sosai ,sannan ta saka Wasu Manya Manyan Layu! Guda biyu ,tayi Sauri ta Mayar da kasar gurin ta Binne ,sannan ta Dora dotsen a kai.
Chapter 8 · 0% Book details