← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 80

Sashe 45

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mamaki jama'ar dake gurin suke kallon Waziri jin irin maganar da yake fad'a,maganar tasa tayi kama da ta masu tab'in hankali. Babu wanda ya saurare shi, a cikin su, suka cigaba da bin umarin me Martaba, da k'yar suka samu suka b'anb'are Moddibo daga jikin Sarki! suka nufi fada dashi, domin killace shi tunda dai dole yayi kwanan keso.
Waziri ne ya bi bayan su yana gyara alkyabar dake jikinsa, yace"Ban yadda a aje min gawar d'ana anan ba, domin inaso in kaishi kabarinsa da duk sassan jikinsa gaba d'aya, idan aka aje min gawar d'ana a wannan fada ban yafe ba,domin wannan fada bata alkairi bace,bata tattare da komai sai shirka,da tsafi gami da shanye jinin mutane"
Jin irin kalaman da Waziri yake fad'a ne yasa wad'anda suke d'auke da gawar Moddibo suka dakata, me Martaba kuwa cikin karfin hali yace"Kuje Ku cika umarnin da na Baku"
Aikuwa sai suka shige ciki sosai suka aje Moddibo gefe, suka futo gami da tsayawa bakin Kofa,suna jiran Umarni na gaba, me Martaba ya kallesu a nutse yace"Ku tsaya nan gurin ban yadda kowa ya shiga inda yake ba,yanzu zan futo zan shiga sallah"
Nan suka amsa suna godiya

Me Martaba ya wuce Waziri a gurin yana zare ido.

Waziri kuwa duk ya rasa abunda yake damunsa duk wannan maganganun da yayi, yayi ne kan ya b'ata wa me Martaba rai sai yaga ko a fuskarshi be nuna ba, ya fahimci yana cikin tashin hankali,kuma yasan bata komai bace face ta rasuwar gudan jininsa,.
Shi yanzu sam bai damu da rasuwar Moddibo ba,burinsa kawai yaga ya rusa sarautar Sarki Almustafah,ya kafa tasa
B'angaran sa ya koma fud'un-fud'un yana tafiya yana zancan zucci.

Bayan idar da sallar ne limami ya sanar da rasuwar Moddibo ta lasifi k'a inda jama'ar gari suka ji suka shiga cikin tsananin d'imuwa da jin mutuwar bawan Allah Moddibo, mutumin da bai dauki kansa a komai ba, yana rayuwa dai-dai da kowa Moddibo in ka ganshi baza ka taba cewa yana da alak'a da sarauta ba.

Hajiya Kattime tayi kuka tayi Ala wadai da turr! da halin mijinta,babu tamtama shine yasa zuciyar Moddibo ta buga ya mutu lokaci guda, duk da cewar ita musulmace muka ta yadda duk kanin me rai mamaci ne,mutuwar Moddibo tana alak'a da mahaifinsa Waziri,shine sila.

Humm Rayuwa kenan, me Martaba ne da Sarki! suka wanke Moddibo tsaf suka suturtashi, suka kuma kwana dashi, har garin Allah ya waye.

Mutane damk'am a harabar gidan sarautar suna jira a futo da gawar Moddibo domin su sallah ce shi, kowa da irin abunda alkairin da yake fada a kansa.

Har waye war gari Waziri bai futo ba, kuma duk irin karatun da ake cikin gidan yana ji, domin malamai ne suka taro suna ta sauke wa Moddibo al'ikur ani.

Me martaba ne ya bada Umarni a je a kira Waziri dole ya zo kan gawar danshi kafin a d'auke shi, sannan ya umarci Sarki! kan yaje ya futo da Balaraba, itama tazo kan gawar mijinta kafin a d'auke shi.

Gabansa ne ya fad'i domin kwata-kwata ya manta da Balaraba, nan take ya shiga wani yanayi da ya tuno da nauyin ta da Moddibo ya dora masa kafin rasuwar sa.

A nutse ya mike ya futa daga fadar, wani bawansa yana take masa baya, kai tsaye shashensa ya nufa.

Balaraba kuwa tun lokacin da Moddibo ya kaisu daki ya ajesu, ta shiga cikin wani yanayi me wahalar fad'a motsi kad'an tayi zataji gabanta na faduwa,lokacin da Moddibo ya zo futa kiran sa tayi ta sanya kuka, tace"Yusuf a rayuwata bani da babban masoyi sama dakai da me Martaba, tabbas yanzu na kara tabbatar da soyyayar da kake min ta gaskiya, Yusuf na baka amanar kaina, saboda kazama jigo na rayuwa ta, ina rokan Allah ya amintar da ruhimu tare"
Hawaye ya share mata,yana wani murmushi Wanda ya kara masa kyau,ya kama duk hannuwanta ya rik'e a nasa cikin taushin murya yace" Gimbiya baki da matsala dani insha Allahu karshen kukan ki ya k'are a duniya,fatana dake kawai ki rik'e amana ta,kuma ki tayani addu'a zanje in nemi yafiyar mahaifina, saboda na lura da halin da ya shiga lokacin daurin auran mu"

Wani hawayen ya kuma zubo mata,ba tare data goge ba tace"Yusuf inajin wani abu a zuciyarta a game da wannan al'amari, don Allah ka nemi afuwa gurin Baba Waziri, kan dukkanin abunda yazo maka dashi"

Damk'e hannunta yayi sosai cikin nasa, da murmushi a fuskarsa yace" Insha Allahu komai zai zo da sauki, yanzu abunda zakiyi shine, kici abunci ki bawa su Sadiya suci su kwanta, ke kuma sai kiyi alwala kiyi sallah raka'a biyu ta nafila domin ki nema mana zab'i na Allah, yanzu zanje in dawo muyi hira me dad'i irin ta Ango da Amarya"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta.Ya mik'e tsaye da murmushi a fuskarsa,ya kamo fuskarta ya manna mata kiss, rufe ido Balaraba tayi cikin jin kunya, fuskar ya saki, ya nufi hanyar futa yana waiwayenta, har ya bud'e kofa zai futa,ya tsaya yace"Gimbiya sai na dawo"
Bud'e ido tayi da sauri tana kallon kofar futa ko rigarsa bata gani ba,ya fuce.

Jiki a sanyaye ta mik'e ta nufi toilet ta dauro alwala tazo ta shimfid'a dadduma ta tada sallah kamar yadda Moddibo ya umarce ta.

Sosai ta yi addu'oi tana kuka tana rokan Allah, bacci ne ya ci k'arfinta nan kan daddumar ta b'ingire bacci me nauyi ya d'auke ta,ba tare da taci komai ba,hakanan su Sadiya basu ci komai ba suma bacci ya kwashe su,

Humm baccin asara kenan baccin da Balaraba bata tab'a irinsa ba, ko sallahr asubah ba tayi ba, a tak'aice dai Balaraba bata da labarin rasuwar Moddibo domin bata tashi farkawa ba sai k'arfe bakwai da kwata na safe.
[08/08, 04:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

_*MARUBUCIYAR*_
```Nana Khadija```
```Yaro Da kud'i```
```Gimbiya Balaraba```

_*ZAMANI WRITERS*_
_*ASSOCIATION🤝🏻*_
________________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_
________________________

_*DIDEGATED*_
_*TO*_
```RAHAMA ALIYU```

_*BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM*_

*🅿70*
Bugun k'ofar Sarki! ne ya tashe ta,ta mik'e zaune jikinta duk a mace,da k'yar ta mik'e tsaye ta nufi, K'ofa domin bud'ewa duk a tunaninta ko Moddobo ne, tayi mamakin baccin da ya kwashe ta,me cike da tarin mafarkai marasa kyau.Bud'e kofar tayi tana koma wa ciki ba tare da ta kalli me shigowa ba, shiga yayi d'akin sosai yana bin su da kallo daga ita har su Sadiya

Sai da ta zauna gefen gado tana kallon sa, gabanta ne ya fad'i lokacin da suka had'a ido da Sarki! Mutum me fararan idanu taga k'wayar idonsa ta rine tayi jajazur!
K'asa tayi da kanta,gabanta na dukan uku-uku! A nutse yace"Kinyi sallah"

Cikin wani irin yanayi ta kalleshi tana girgiza kai.
Alamun batai ba.

Ajiyar zuciya ya sauke k'asa-k'asa yace" Kiyi sallama ki sauko k'asa ki same ni, ina jiran ki"

Cikin k'arfin hali tace"Ina Moddibo"?
Yana k'okarin futa daga d'akin yace"Yana k'asa,zaki sauko ki same shi"
Futa yayi ba tare da ya saurari abunda zata ce ba.

Mamaki take me ya kawo shi d'akin ina Moddibo yake?,shine ya kamata ya shigo gurin ta ba Sarki! ba,bayan haka kuma taga kamar a kwai alamun rashin nutsuwa a tattare da Sarki!
Sauri-sauri tayi alwala ta futo ta tada sallah.Bayan ta idar tai addu'oi yanda ya sauwak'a ta mik'e har zata futa ta dawo tana duba su Usuman dake ta faman bacci, Ajiyar zuciya tayi ta tashi Sadiya domin tayi sallah,sai da taga Sadiya ta shiga toilet sannan ta futa daga d'akin.

Yana tsaye tsakiyar falon hannunshi goye a bayansa hankalinsa na sama ita kawai yake jira ta sauko, had'a ido sukayi a karo na biyu lokacin da take saukowa dukkaninsu suka d'auke kai,sai kace wasu surukai, bai jira sun jera ba, ya kama hanya zai futa, ita kuma sai ta tsaya a tana kallon sa,yace tazo kasa ta same shi zai futa kuma ina Moddibo yake?
Mutumin dake take masa baya ne yace"Allah ya kara miki lafiya, ai bayansa zaki ni, me Martaba ne yake neman ki"
Jin abunda yace yasa fad'uwar gabanta ya tsananta, babu kuzari tabi bayansa, kanta a k'asa
Tayi mamaki da ta dunga ganin mutane a harabar gidan kuma kowa ta kalli fuskarsa babu walwala gashi wasu daga ciki sai kallonta da k'yar dai suka isa fada, Sarki!ya tub'e takalmin sa ya shiga,ita kam tsayuwa tayi bakin Kofa sai da akai mata iso sannan,ita babban abunda ya d'aga mata hankali shine dandazon mutanan da ta gani shiya furgitata.
Me Martaba ne kad'ai cikin fadar sai gawar Moddibo dake cikin makara a killace, Balaraba na sanya k'afarta ciki taci karo da makara, fad'uwa ta kusa yi saboda tsorata da tayi,bango ta dafa da hannunta miyau din bakinta ya bushe tass!tamkar ba'a tab'a hallitarsa ba,a bakinta har wani shak'ewa take, zubewa tayi bakin k'ofa, tana shashsheka,shikkenan mafarkin da tayi kan Moddibo ya tabbata babu tamtama wannan Moddibo ne cikin makara,kamar yadda ta ganshi jiya cikin baccin ta, kamar zautacciya ta k'arasa kusa da Moddibo da rarrafe,ta sanya hannu ta d'aga mayafin da aka lullub'e masa fuska dashi, Silalewa tayi ta fad'i a gurin ta suma.

Da sauri Sarki!ya mik'e yaje ya janye makarar,cikin tashin hankali yake tunanin yaya zai da ita

Me Martaba,ne ya mik'o masa ruwa irin na gora,ragowa ne wanda ya sha ya rage yana aje a gefe, jikinshi na kyarma!ya karb'a ya gumtsa a bakinsa ya fesa mata a fuska, ta bud'e idonta zumbur zata mik'e a gigice!Sarki!ya dafe,hannunta dake rawa,karr!-karr! muryasa bata futa sosai ya kalli mahaifin nasa yace"Allah ya taimake ka, ya kamata a futa da Moddibo domin wannan kwata-kwata babu abunda zata iya yi masa na addu'a tunda bata cikin hayyacin ta,ina ganin zan shiga da ita gida gurin Mama dole sai tasa ido a kanta zata iya futa bata sani ba"

Me Martaba yace"Wannan shawarar taka itace shawara, kai ta cikin gida, idan ka shiga kai kiro min Hajiya Kattime da Mahaifiyar ka, su futo suyi bankwana da Yusufu domin za'akaishi gidansa na gaskiya"
Chapter 45 · 0% Book details