Sashe 17
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maddibo da ne ga wazirin Sarki,inda Waziri ya kasance kani ga Maimarta ba Sarki Almustapah,Uwarsu daya ubansu daya, Waziri yana da "yaya goma sha shida, bakwai mata sauran duk maza ne, matanshi hudu ko wacce tana da " yaya dashi, Waziri mutum ne shi mai bala'in san mulki sosai domin ji yakeyi tamkar ya kwace sarautar daga hannun dan uwanshi,kullum burinshi da kokarinshi yaya za'ayi taga sarautar ta dawo hannunshi, shida iyalinshi,shiyasa da yaga Maimartaba bai haifi da namiji ba,sai hankalinshi ya kwanta, yana jiran ranar da Maimartaba zai kwanta dama,ya gaje sarautar tunda shine namiji,cikin hukunci ubangiji Allah ya azurta Maimartaba da haihuwar Sarki!Almansor, in da ya zamo daya daya kwal cikin "yaya mata goma sha bakwai shi ya zama cikin na sha takwas, lokacin waziri kusan zaunce wa yayi,ya dinga shige sa fuce gurin ganin ya ga bayan Sarki!Almansor, Allah bai bashi iko ba,dan duk wani kulunboto da yake shiryawa sai ya koma kanshi ko kan iyalinshi,duk rabi" yayanshi maza sun zama "yan shaye-shaye in ka cire, Yusuf(Maddibo) duk ciki shine nutsatstse a cikinsu,shiyasa suka fi shiri da Sarki!Almansor kusan a tare suka yi makaranta komai iri daya suke sawa, duk inda daya yake dayan ma ba gurin, halayyarsu ce kawai bata zo daya ba,inda Sarki Almansor ya kasance mugun muskili wanda magana take masa wahala,sai ya kwana ya yini bai kula kowa ba har in dai ba kamawa tayi ba,shi kuwa Maddibo mugun saukin kai ne dashi gami da wasa da dariya, in ka ganshi sam baza kace yana da alaka da gidan sarauta ba,sabuda da kowa mu'amala yakeyi,babba da yaro,
Tsakaninsu basa boyewa juna sirri duk abunda ya dami daya daga cikinsu, tsakaninsu suke warware matsalar basa taba yadda maganar ta futa waje, shiyasa kai tsaye Maddibo shi ya fara kawowa maganar Balaraba,
Kiranshi da suna Sarki! da mutane keyi na gida da jama'ar gari ya samo a sali ne daga gurin mahaifinshi,shine take kiranshi da sunan tun yana yaro in yaga yana wata irin tafiya cike da kasaita, ko cin abuncin sa abin kallo ne,balle yadda yake magana, Yadda Maimartaba ya fuskanta abin a jininsa yake, shi kanshi yaron ya san ya fishi kasaita, shine dalilin da yasa yake kiranshi da sunan, mutanan gida suka kama hade da jama'ar gari
Halisa kuwa " yar kanwarsu ce wacce ta kasan ce autarsu wato Fulani Mariya maca ce mai mutukar kirki da sanin ya kamata sam bata kin talaka kullum cikin jawo jama'a take gidanta, tana can tana auran sarkin garin Wani gari jaja Amare, tun Halisa tana yarinya rikonta ya dawo hannun, me babban daki, wato Uwargidan Sarki, ta hada da "yayan ta ta rike kamar gaske, tun ta so warta take mutuwar son Sarki!Almansor, tun tanayi a boye har abu ya fito fili kowa ya fahimta,har maimartaba, nan kuwa Me babban daki ta tsaya kai da fata tace lallai dole ne a kulla wannan al'amarin domin dorewar zumunci, Maimarta ba ma ya nuna yaddarsa, a kan al'amarin, Shi kuma wanda ake domishi ya nuna bayaso da kyar dai mahaifiyarshi ta lallabashi ya dadda gudun bakin mutanan gari
*Wannan shine kadan daga cikin tarihin abunda ya faru a baya*
*Cigaban Labari*
Da asubah Maddibo yasa drevar ya futa dashi suka shiga kasuwar sha tambaya,can gefan titi yasa drevar yayi parking din motar, yana kwance cikin motar yana kallon masu shigowa cikin kasuwar duk da cewa safiya ce,
Wajan karfe takwas da rabi ya hangi Napep din Ashiru Balaraba na kokarin fitowa daga ciki yau tana cikin wata irin doguwar riga baka " yar saudia rigar taji adon duwatsu sosai da sosai tayi nan nade kanta da veil kafarta sanye da wani takalmi mai tsayi mai igiyoyi,sai ta kara tsayi sosai takalmin shima baki ne sosai kafarta tayi kyau a cikin talakmin hannuta rike da wayarta da wata "yar karamar pose ta tsaya suna magana da Ashiru
Maddibo kuwa suma ne kawai bai yi ba lokacin da ya hangi fitowar ta sai ajiyar zuciya yake saukewa, yana wa Allah tasbihi cikin zuciyarsa yace" tabbas Allah ya aje baiwarsa gaskiya yarinyar ta hadu sosai, dole maza su rika rikice wa a kanta, in da take burgeshi , kamun kai da rashin kwadayi gami da dogaro da kai shiyasa duk abunda a ka fada masa a kan ta yake kauda kai,sabuda yana ganin babu mahalukin da ya isa ya hanashi auranta,
Ya na can yana tunani Ashiru yaja Napep dinshi ya na kokarin hawa titi,can ya hangoshi, da sauri ya bawa drevar Umarnin bin bayanshi duk in da ya nufa.
*Muje zuwa*
[30/06, 04:10] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
∆∆∆∆∆∆
_*GIMBIYA BALARABA*_
∆∆∆∆∆∆
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*Na*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*MARUBUCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```
Zamani Writes Association🤝🏻
```Bisimillahir rahamanir rahim```
*🅿34*
Sosai Ashiru yake gudu a kan kwalta,kasancewar babu cinkoso sosai na ababan hawa, sauri yake shima ya isa gurin aikinsu, kawai sai yaga katuwar mota ta tari gabanshi, sai ya rage gudu, ya fara tafiya a hankali gabanshi yana faduwa!
Cikin sauri drevar dake jan Maddibo ya yi parking din motar gefan titi ya fito,yana dagawa Ashiru hannu.
Ashiru ya tsayar da Napep dinshi ya fito daga ciki duk hankalinshi a tashe,ganin mutum sanye da wasu manyan kaya ja da baki kanshi nade da wani katon abu,yana gani ya fahimci daga gidan sarauta ne,
Hannu ya bashi suka gaisa yace"Yallabai ne yake son yin magana da kai"
Jiki na rawa Ashiru ya bi bayan dravar suka karasa inda yayi parking din motar, Maddibo ya mika masa hannu fuskarsa a sake yace"barka da asubah"
Cikin dari-dari Ashiru ya mika masa hannu sukayi musabaha da juna,kana yace"barka dai yallabai,fatan katashi lafiya"
"Lafiya kalau Abokina"
Maddibo yafada fuskarshi dauke da murmushi ya cigaba da cewa"in baza ka damu ba inaso in nemi alfarma a gurinka"
Jiki na kyarma Ashiru yace"babu damuwa Yallabai"
"Masha Allah, Menene alakar ka da Balaraba"?
Cikin rawar baki yace" babu wata alaka a tsakaninmu kawai ina kaita bakin kasuwa kullum"
"Ok shiga muje ka nuna min gidan su"
Maddibo yafada babu wata damuwa a tare dashi.
Ashiru duk ya rude yace"Yallabai Allah dai yasa ba wani abun tayi muku ba,sabuda na fahimci bata kaunar Sarki!Almansor, in wani abu tayi muku, ku gafarce ta dan Allah, Balaraba marainiya ce bata da uwa babu uba,kusan itace take daukar nauyin gidansu"
Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke, wani irin tausayin Balaraba yana ratsa zuciyarsa.
Yace"Babu laifin da tayi mana, alkairi ne zai kai ni gidansu,ka kwantar da hankalin ka"
Da kyar Ashiru ya je ya gyara parking a gefan titi kana ya sanya key ya kulle Napep din nasa, ya shiga motar suka kama hanya har unguwarsu Balaraba.
Sosai Maddibo yayi mamakin irin unguwar da Balaraban shi take rayuwa, wani irin lukuna masu dauke da dagwalan katoci ku ina kwata tabi hanya abun babu kyawun gani, hankalinshi bai kara tashi ba ma sai da yaga lokwan su Balaraba,mai tattare da tarkacan, kayan gwan-gwan ko ina gasu nan wasu a daure a buhun-huna wasu kuma a washe a hanya, in ban da wari babu abunda yake tashi a gurin,
Kasa shiga ciki yayi sosai ya tsaya daga baya, Ashiru yace"Yallabai ga gidan can, in da waccan budurwar take soya a wara to nan ne gidansu"
Yara ne suka fara taruwa a gurin suna kallon Maddibo,wasu na rugawa gida da gudu suna fada cewa ga Sarki yazo, ai tuni Yara suka cika gurin,kasancewar Safiya ce wasu duk sun fito domin tafiya makaranta, da sauri ya juya, ya bar gurin drvar shi ya bi bayanshi yana baza babbar riga, Ashiru ma ya mara musu baya,cikin zuciyarshi yana mamakin abunda yasa wannan mutumin yake neman gidansu Balaraba,
Maddibo ya shiga mota hankalinshi a tashe yana tunanin yadda za'ayi Sarki! ya iya shigowa wannan unguwar, shida yake da mutukar tsabta da mugun kyam-kyami! Wani lokacin in yaga abunda kyam-kyami, tsigar jikinshi ta dinga tashi kenan kuma kwana yake tsartar da yawu,ko ya yini bai ci abunci ba, yasan halinshi, sai dai kawai ya daukoshi suzo ba tare da yafada masa yadda yanayin gurin yake ba, kuma dole zuwan dare zasuyi, shawarar da ya yanke kenan cikin zuciyarsa.
Misalin karfe takwas shaura na dare, Maddibo na Shashen Sarki yana fama dashi ya tashi ya shirya, su tafi kar dare yayi, sai da ya gama yan garshi sannan ya mike ya shiga bedroom dinshi yayi wanka, ya fito a nutse ya tsaya gaban tafkeken dressing miroow dinshi wanda yake dauke da wasu mayuka masu tsada hade da manya-manya turarrika masu bala'in kamshi, da tsada.
Mai ya dauka yana shafawa a lafiyayyir fatarshi, sai sheki takeyi ko fatar wata macan albarka, Sarki!yana da kyau na ban mamaki ba lokaci guda kake ganin kyawunshi ba, sai ka yi kamar minti biyar kana kallonshi,a san nan ne zaka rinka ganin zallar kyawunshi yana bayyana wanda har kaji baka san ka dauke idanka da kanshi, Wata irin fata ce dashi chacolet, ga ta a murje ga wani lafiyyan gashi da yabi jikinshi ya kwanta baki sidik dashi, hatta da ya tsun kafar a kwai su a kwance,hakanan gefe da gefan fuskarshi, nan ma yabi ya kwanta, an yi masa wani irin gyaran fuska wanda yafito masa da dogan hancinsa hade da karamin bakinshi,kasan habarshi gashin yafi yawa ya barshi yayi tsayi kadan, hakan yayi masa mugun kyau, Sarki!Bashi da fara'a sosai, haka in baka sanshi ba zakayi zaton yana da girman kai, gami da wulakanci sabuda,dabi'ar shi, amma in kayi mu'amala dashi sau daya zaka gane mutum ne shi mai mutukar kirki gami da saukin hali, baya son rai ni ko kadan, shiyasa basa shiri da Halisa sabuda ya fuskan ci halinta,
Sarki!yana da wani abu da ya boye yake aikatawa babu wanda ya sani daga shi sai Ubangijinsa, cikin zuciyarsa baya son wannan abu da yakeyi, shiyasa kullum cikin rokan Allah yakeyi da ya sa ya dai na.