← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 80

Sashe 22

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan kuma abunda ya shafe ka ne, wannan yarinyar bana fata in sake ganinta,har abada kai ma ina me baka shawara ka janye maganar auranta,zai fi maka alkairi,kanemi yariyar arziki domin samawa " yayan ka Uwa ta gari"

Cikin Sanyi murya Maddibo yace"Addu'a kawai zaka taya ni dashi a kanta, amma maganar gaskiya Allah ya jarrabe ni da kaunar ta, kuma kai ne kake mata kallon mara tarbiya Balaraba yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata, abunda yasa ake mata kallon mara tarbiya dalilin sana'ar ta ne kawai"

"Ok me yasa baza ka hanata talla a cikin kasuwa, in dai da gaske kana sonta,sai ka hanata fita kawai ka killace ta guri guda,kai kanka kasan al'adar cikin gidan nan, abu mawuyaci ne su yarda ka aure ta"

"Ko kowa yaki yarda da al'amarin Maimar taba zai lamunce min,sabuda kasan halinshi da saukin kai, mutukar a kayi buncike a kanta, a gano babu wani aibu, a tattare da ita, ba zai hana kulluwar al'amarin ba"

"Ok Allah ya bada sa'a"
Abunda yace kenan, ya koma ya kwanta cikin kujera

Shiru falo yayi kowa yana sake-sake cikin zuciyarsa,daga bisani Maddibo ya mike ya nufi wani bedroom dake falon domin ya yi wanka yayi shirin bacci

Shi kuwa Sarki! da alama a falon zai kwana domin dai bashi da alamar tashi ya shiga bed din yana kwance yana dacin rai, tunani kawai yakeyi kan Balaraba, wane irin mataki zai dauka a kanta, domin duk abunda yayi mata bai wuce ba sai yaga karshen rashin kunyar ta, sai dai wannan ya zama dalilin batawarsu da Maddibo

*Comment*
*Vote anda Share*
[07/07, 22:32] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®REAL BINTU BATULA👄*

*MARUBUCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```

_*Zamani Writes Association*_🤝🏻

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
```{ RAHAMA ALIYU}```

*🅿41*

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

Har karfe biyu na dare yana zaune a falo yana kallace-kallace,Maddibo ko tuntuni yayi bacci babu abunda ya dame shi, wani film yake kalla tashar Sky Moveis, sai da yaga karshen film din sannan ya mike a nutse ya kashe kayan kallon ya nufi bedroom din nasa, kai tsaye toilet ya shiga yayi wanka gami da dauro al'wala, ya futo a nutse ya shirya, jikinshi, ya fesa turare sannan ya shimfida dadduma ya tada sallahr nafila kamar yadda ya saba,duk daran duniya, yana nan zaune kan abun sallah har aka fara kiran sallahr asubahi, ya mike tsaye hannushi rike da carbi ya sanya wani takalmi mai uban kyau,jikinshi duk wani gashi-gashi kana kallon takalmin kasan irin na masu mulki ne, futa yayi daga dakin nasa ya nufi kofa, har yq bude zai futa,sai ya tuna da Maddibo ya koma da baya, ya bude bedroom din da yaga ya shiga jiya, Maddibo na kwance bacci yake sosai,
Kiran sunanshi yayi"Maddibo"
Bude ido yayi dake bashi da nauyin bacci

"Ka tashi kayi sallah ni na tafi massalaci, sai kafito"

Bai tsaya ya saurari abunda Maddibo zai ce ba kawai ya fuce daga dakin

Yana futa suka ci karo da Maimarta ba ya futo tare suka jera har zuwa massalacin,

Bayan an idar da sallah suka gaisa, jama'a kowa yana so su gaisa da Maimarta ba, da yake in an idar da Sallah ya kan zauna a massalanci su gaisa da Jama'a ko kuma in da akwai daurin aure ko radin suna duk nan za'a gabatar kafin ya koma gida ya futo fada

Sarki ya na zaune kusa dashi Waziri yazo suka gaisa da dan uwanshi, da alama akwai maganar da yake so yayi, ganin haka yasa mutane suka fara futa da dai-dai da dai-dai, gurin ya rage daga Maimarta ba,sai Waziri da Sarki! Sai Maddibo dake gefe guda yana lazimi

Kanshi a kasa yace"Allah shi taimake, dama akwai maganar da nake so muyi da kai, tuntuni wallahi sai yau, nace,ko zamuyi maganar kawai a huta Allah shi taimake ka"

Maimarta ba,yana zaune hannushi rike da wani carbi mai kyau sai kalli yake,lazimi yake, kallon kanin nasa yake, yana nazarinsa sabuda yafi kowa sanin waye Waziri, duk da girmansa sam bai san abunda ya dace ba gashi bai iya yanke hukunci ba,shiyasa ko wani abu a kakawo gaban fada,ba ya wakiltashi a kai, gwara ya wakilta Sarki!sabuda yana yin abu cikin hikima da adalci,

Gyaran murya yayi yana nuna masa carbi,alamar ya daka ta tukkuna, ya cika carbin

Tsit!gurin yayi har sai da ya kammala, sannan ya dago kanshi cikin nutsuwa yace"Wace irin magana ce, wannan wacce ka boye ta ka kasa fada gashi kullum muna zama a fada, da tuni an warware ta"

"Allah shi gafarta maka, ai wannan maganar bata shafi fada, ba ta shafi cikin gida ne,"

Girgiza kai Maimarta ba yayi tsawon minti biyu bece komai ba,daga bisani ya kalli Waziri yace"ka sameni a shashen Fulani sai mu tattauna maganar, Allaj ya warware mana"

"To" To Masha Allah, Allah ya kara nisan kwana ai magana ce ta alkairi nasan kuma kai ma zakaji dadin ta"

Murmushi Maimarta ba yayi ya mika masa hannu suka musabaha, yace"ai tunda naga kana farin ciki nasan maganar ta shafe ka"

"Kwarai kuwa"
Waziri yafada shima yana murmushi, amma fa ta ciki na ciki

Sarki! ne ya matso sosai kusa da mahaifin nasa, kanshi a kasa yace"barka da asubah"
Hannunshi Maimarta ba ya riko fuskarshi a sake yace"kai kayi min laifi, kwana biyu baka zuwa fada,bazan karbi gaisuwar ka b

Sosa kai yayi na sabo,yayi kasa da kanshi yana murmushi yace"tuba nake ranka shi dade, tunda mukaje can gwarzo na dawo bana jin dadi jikina,wallahi"

"Me yasa baka kawo uzirin ka ba"

Shiru yayi sai faman sosa kai yake

Waziri Zayyanu yace"wannan sharme ne, mu me yasa muke futowa fada, kullum kuma ai tare mukaje can Garzon ko ba haka ba ne, wannan yana nuna mana cewar sam baza ka iya wakiltar jama'a ba.
Cikin fada ya karashe maganar,

A nutse Sarki ya dago kai yana kallonshi,ya wani hade fuska sam ba ya so yana shiga lamarin shi,shi kuma yaki ya gane,
Ganin yadda Sarki! ya hade fuska ne yasa Waziri saurin sunkyar da kansa, sabuda wani irin kwarjini da Allah yayi masa,

Wannan abun da Waziri yayi masa yasa ya fasa gaida shi,kawai ya dauke kanshi,jira kawai yake Maimarta ba ya mike shima ya samu damar tafiya,
Maddibo ne ya karaso kusa da Maimarta ba ya gai dashi, ya gaida Mahaifin shi Waziri Zayyanu,

Maimarta ba ya mike cikin nutsuwa, suma suka mike suka biyo bayanshi lokacin gari ya soma washe wa, Wasu fadawa ne guda Uku tsaye bakin massalacin sune suka rufa musu baya,har sai da Maimar taba,ya shiga Shashenshi,sannan kowa yayi nasa ban garan,

Sai wajejen Goma da wani abu sannan Waziri ya samu Maimar taba,bangaran Fulani, nan suka zauna a ke bantaccan falo wanda yake zama domin sirri irin wannan,

Gyara zama yayi sosai yace"ranka ya dade magana ce daga Sarkin garin Yalwa, kasan tare mukayi karatu dashi,sosai har yanzu alakar mu dashi tanan, to shine yake neman wata alfarma a gare ka, wato ya naso ya hada jini da kai, wai yarinyar shi Azima tana son Auran Almansor,, shine ya aiko min da sako, a kan hakan, Allah shi tai makeka kaji abunda yake tafe dani"
Waziri ya kare maganar yana sauke ajiyar zuciya
Kanshi a kasa yana sauraron abunda Maimar taba zai ce

Minti biyu a tsakani, Maimarta ba yace"wannan ba hurumi na ba ne,domin bazan iya tilas ta Sarki! ya je ya nemi auran yarinyar nan ba, abunda zakayi kawai ka nemi shi kafada masa zan can, sannan yarinyar tazo ya gan ta in yaga tayi masa shikkenan,ni dan addu'a ne, sai a hada da Halisa kawai"

*Comment*
*Vote and Share*
[08/07, 13:24] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®REAL BINTU BATULA👄*

*MARUBUCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```

_*Zamani Writes Association*_🤝🏻

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
```{ RAHAMA ALIYU}```

*🅿42*

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

Shiru Waziri Zayyanu yayi na minti biyu kana ya dago kanshi yana kallon Maimartaba yace"Allah shi taimake ka ina ganin yaron nan zai bamu kunya domin kasan halinshi da baudaddan ra'ayi, ina ganin kai ne zaka tilas tashi ya amunce da buk'atar mu,domin lokacin maganar Halisa ma haka muka dinga dauki ba dadi a kansa, Zai iya bujerewa bukatar mu, Azo a samu matsala game da dan gartakarmu da Sarkin Yalwa, Maimar taba Sarki Alkassim"

Cikin Mamaki Maimarta ba yake kallon Waziri jin abunda yace, gyaran murya yayi a nutse yace"maganar in tilas ta Sarki! ya nemi auran yarinyar da kake magana sam! bata taso ba, domin babu wanda zai zauna masa da ita,sai shi,idan na tilas tashi yaje ya dauko yarinyar mutane, yazo yayi mata rikon sakainar kashi,in ce me? ko kai kace me, abunda nakeso ka fahimta shine, ba wai ina biye wa yaron da duk abunda yake so ba, ina neman zaman lafiya da kwanciyar hankali, ko yau Sarki! yace yana so ya auri mace hudu ni mai daura masa aure ne,sabuda nasan da amuncewar sa kuma ba kowa ne zai zauna masa da suba sai shi, sabuda haka ka aika ai maka kiranshi,sai ka zube masa maganar in ya amunce shikkenan nima na amunce, Allah ya tabbatar da alkairi"
Ya karashe maganar yana duba wani karamin littafin husunul-musul wanda yake karantawa shi kullum da safe,

Jikin Waziri Sanyi kalau ya dago kansa yana kallon Maimartaba yayi tunanin zai samu nasara gurinshi sai yaga sab'anin haka, a gurinshi, jiki a sanyaye yace"duk yadda kace haka za'ayi Allah shi taimake ka zan sanya a kira min shi yanzu kafin mu zauna a fada"

Cikin sakin fuska Maimarta ba ya mika masa hannu sukai musabaha yace"masha Allah, ina sauraron ka duk yadda kukayi dashi sai ka same ni a shashenan domin tattauna maganar"

"Insha Allahu, A tashi lafiya"
Waziri yafada kanshi a kasa ya futa daga dakin.
Chapter 22 · 0% Book details