Sashe 29
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yace"in ka isa ka k'ara shiga hurimin Balaraba, sai dai Uwarka ta haifi wani, ya karasa maganar yana cije baki!
Ihu! Uwa! take kurmawa tana tsinewa Walidi, Iro ta kallah wanda yake kwance bai san in da hankalin shi yake ba, jini ne kawai yake futa ta hancinsa da bakins, da gudu ta karasa gurin da Lantana take tsaye, tace"Lantana a gabanki za'ayi kisan kai, sabuda ke butulo ce wato kin manta alkairin da yaron nan yake miki,kullum ya dawo daga tafiya kin dinga k'arb'e masa kud'adan sa, babun abunda zance dake sai dai ince Allah ya isa tsakanina dake Lantana" tana gama fad'ar haka ta shige cikin gidan da gudu domin ta d'ebo ruwa wanda zata zubawa Iro da alama suma yayi
Tana barin gurin Lantana tace"Yo ni me zan tsinana miki, kaji masharanciyar mace, ko zatai min sharri, yashe nake ganin Iro ma balle ya bani kud'i o ni Lantana Allah ya had'ani da suruka wacce bata k'auna ta"
Banza Walidi yayi mata,hankalin sa na kan Balaraba yana tausar ta, kawai sai saukar mai soyayye yaji a k'afafun shi ya waiwaya a zabure! Shamsiyya a tsaye a bakin k'ofar shigowa hannuta rik'e da abunda take tsamo a wara, sai muzurai! take sam! bashi taso mai ya sama ba Balaraba tayi niyyar watsa wa sai ya sauka a k'afarshi.
*Muje zuwa*
*Comment*
*Vote and Share*
[15/07, 22:39] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^°
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®{REAL BINTU BATULA}👄*
_*MARUBUCIYAR*_
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```
_*DEDIGATED*_
_*TO*_
```{RAHAMA ALIYU}```
_ZAMANI WRITES_
_ASSOCIATION_🤝🏻
```Bisimillahir-rahamanir-rashim```
*🅿50*
Da sauri Balaraba ta sunkuya tana duba k'afarta guda wacce soyyayan mai yayi nasarar zuba lokaci guda ya tsun kafarta suka tashi, sabuda nan mai ya zuba Walidi kuwa ko ta kan kafarshi bai yi ba, yayi kan Shamsiyya, da wani mahaukacin duka, da gudu tayi cikin gidan, domin tasan zai iya ji mata ciwo,
Duk suna tsaye a tsakar gidan ta shigo a guje ta nufi d'akinsu ta kulle kof'a tana zagin Walidi tace"dan Uwarka, ka manta ranar da ka k'onani akanta, wallahi naso ita man ya sama shegiya mai sufar aljanu"
K'wafa Walidi yayi kawai yace"sai dai in baza ki kara futowa ba amma billahillazi sai na k'one miki wannan bak'ar fuskar taki,wacce ta gaji da bilitin" d'akin Balaraba ya nufa yana k'okarin bude mata,
Lokacin da ta shigo cikin gidan kai tsaye d'akin Iya ta nufa, duk mutan gidan babu mai kula da ita, gwara ma matar Kawu wato Sadiya,ita kuma, bata zama,kusan kullum tana hanyar gidansu, tana jinyar mahaifiyar ta, Iya na kwance kan wata ya mutsetstsiyar kafita jikinta a rufe,da zani sai rarar d'ari take, Sadiya da Usuman suna zaune sun zabga uban tagumi, suna tsoran su futa Lantana ta dakesu domin haka take musu kullum shiyasa in suka dawo daga makaranta, har indai yayarsu bata dawo ba, to sai suyi zamansu gurin Iya, jikinsu yayi sanyi da rashin lafiyar Iya.
Shiga tayi d'akin cikin sallama Sadiya ta amsa, tace" Yayarmu sannu da zuwa"
"Sannu Sadiya, kuna zaune ku kad'ai Iya bacci take ne"?
" Yanzu ta tashi taje tayi alwala ko sallah batai ba ta koma ta kwanta"
Sadiya tafad'a tana kallon yayar tata.
" Yayarmu kin dawo lafiya"?
Usuman yafada, hankalinshi na kan ta
"Lafiya lou Usuman, kayi karatu a makaranta ko"?
" Eh nayi yau ma an karb'i haddar da aka bamu"
"To ka dage da karatu ni kuma nayi maka alk'awarin zan siya maka keken hawa"
Murna yake sosai ya mik'e ya karaso inda take ya rik'e hannunta yace"nagode Yaya Allah ya biya miki bukatun ki"
"Ameen" Balaraba tace ta mayar da hankalin ta kan Iya, tace"Iya sannu da jiki"
Kai kawai Iya ta iya d'agawa "Bari in d'auko miki hijab muje Chamis kinji"
D'aga kai ta kuma yi a karo na biyu.
da taimakon Balaraba Iya ta mike tasa mata hijab d'in ta rok'ota suka futo, Su Sadiya nan suka zauna jiran dawowar su
Kasancewar Walidi ya futa daga gidan yasa Lantana yi musu wani kallo shek'ek'e tace"munafurcin banza da wofi, zaki lanjare kice baki da lafiya, duk kuje ku gama munafurcin naku ku dawo ku same ni nice dai Lantana ban can zaba
Babu wanda ya kulata cikinsu Uwa! lokacin tana band'aki, sai ita kad'ai a zaune a tsakar gidan, suna futa suka ci karo da Sallau ya dawo,tun daga bakin lungu a kasanar dashi abunda ya faru a gidan, cikin tashin hankali ya shigo gidan,
Yaji dad'in ganin ta a sabuda haka sai ya ja tsaya yana surfa mata ashar yace"bantab'a sanin ke "yar daba bace sai yau, duk ikirarin da mutane suke a kan " yayana cewa suna harkar Daba! a she ba haka bane, duk abunda ya faru d'azu ina da labarin sa, to bari kiji wani abu da baki sani ba, duk k'iyayyar da kike wa Iro shine dai mijin ki ko kink'i ko kinso sabuda haka dole ne zakije har d'akinshi ki bashi,hakuri idan kuma kink'i sai dai kije ki nemi wasu iyayan bamu ba, domin ni nan da kika ganni sharri na yafi kala dubu,wallahi duk inda kika shiga,sai naje na b'ata miki suna"
Ya karashe maganar a zafafe!
Da kyar! Iya ta bud'e baki tace" haba Sallau bai kamata kafad'i wannan maganar ba,kamata yayi kabi ba'asi kafin ka yanke hukunci, me Iro yayi mata har ta d'auki mataki a kanshi, ni duk da akwance nake a d'aki bana jin dad'i hakan bai hanani na jiyo abunda yake faruwa ba, da Iro da Balaraba duk naka ne, in dai adalci ake"
"Ke Iya rufe min baki, bana son hauka, me zai yi mata kuwa? wanda har zata d'auki wuka ta cire masa d'an yatsa, wallahi sai kin biya kud'in magani yanzu-yanzu, domin yana can Chamis za'ai masa d'inki, duk abunda ya faru shi Iro da kanshi yaje ya fad'a min komai, ni sam banga wani laifi a nan ba, dan yayi yunkurin tab'a jikin ki sabuda shine mijinki, dama kuma addini ya hallata cewar namiji zai iya tab'a jikin matar da zai aura kafin auren domin ya san wace iri ce matar gudun abunda zai je ya dawo, sabuda haka bayan kin biya kud'in maganin shi zakije ki bashi hakuri har shagonshi, kamar yadda na fad'a a farko"
Cikin mamaki Balaraba take kallonshi, jin abubuwan da yake fad'a bata tab'a yadda Kawu Sallau mugun jahili ne ba irin yau, a wace mazahabar a ka yadda namiji ya kusanci mace kafin auransu, itakam bata tab'a jin wannan k'aulin ba,
Iya tace"to kayi hakuri mu dawo sai mu yi maganar in sha Allahu zata bi umarnin ka kamar yadda kake so"
Kaucewa yayi ya basu hanya yace"kuje ku dawo ku taddani ina nan ina jiran ku"
Suna futa shi kuma ya shige gidan yana zage-zage kamar wani mahaukaci, Lantana ta mik'e zaune tana taya shi zage-zage tace"ashe kaji abunda ya faru ko?
"E naji ai shi Iron yaje ya fad'amin, duk abunda ya faru,kuma ina shigowa unguwar ake ta tarata ana fad'amin"
"Hummm! kagani ai sai ka d'auki mataki akan ta in ba haka ba kuwa sai dai kazo ka tarar ta kashe mu,a gidan dan yarinyar ta zama abunda ta zama, a duniyar nan"
Nan Sallau ya zauna kusa da mahaifiyar tashi suna k'ara maimaita maganar,
Uwa!ce ta futo daga band'aki hannunta rik'e da buta, aje butar da sauri ganin d'akin Balaraba a bud'e tun dazu Walidi ya bud'e mata, lokacin da zata shigo,gidan sam ta manta bata kulle ba suka futa, kai tsaye d'akin ta nufa, Lantana ta mik'e da sauri tabi bayanta, shima Sallau d'in mikewa yayi ya rufa musu baya,
Bunkice suke mata sosai a cikin d'akin sunyi mata filla-filla da kayan sawar ta sun jefo waje, Lantana tace" yawwa Uwa! d'aga katifar nan ko anan take b'oye k'udi ki kwasa maganin dukan d'anki da tayi, aikuwa kafin Lantana ta rufe baki, Sallau ya d'aga katifar da sauri, babu komai k'asan katifar, ya mayar da ita ya aje, dama Balaraba bata wani ajiyar k'udi duk in ta samu na b'ukata ne shiyasa basa taruwa, mafi a kasari ma tafi ajiya cikin jakarta,kuma tana jikinta a rataye, haka suka k'araci bunkucen su basu ga komai ba, suka futo suna ta zagin ta,kamar mahaukata