← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 80

Sashe 34

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jiki na kyarma! ya warce kamar zai had'a da hannusa, saura k'adan ya tsuguna sabuda tsabar godiya da rawar jiki, nan Sarki! ya wuce ya barshi yana sambatu daf, da zai futa daga lungun sukayi karo da Balaraba, fad'uwa ta kusa yi yayi saurin rik'o hannuta, yana kallonta ta cikim gilashin dake idonsa, kallon kallo sukeyi da ita, fuskarta a had'e ta fuzge hannunta tana hararasa, tare da zabga tsaki tayi gaba, ji yayi bazai iya jurewa ba yasa ya tarota ta hanyar fuzgota ta dawo gabanshi, ya rik'e mata kafad'u da duk hannuwan shi sannan ya mannata da bango fuskarsa daf da tata yace"wai ke dame kike tak'ama ne, mara kunya, dan ma kin samu zaki fad'i na taimake ki shine zakiyi min tsaki" a tsiwan ce tace"anyi maka d'i... bata karasa ba ya rik'e bakin da ya tsunsa biyu ya murd'e leb'ubunan fuskarshi babu walwala yace"wai me kike da suna"? Balaraba kome? d'azu kafin ki futa kin min tsak'i yanzu ma haka, daga kawai an miki tambaya, zakina wa mutane, tsaki, wai ke kina tak'ama da kyau,ko dame kike tak'ama ne"? yafad'a yana zura hannun shi ta bayanta in da ya shafo tudun mazaunan ta a hannunsa, cikin sigar duniyan ci, yace "ko da wannan kike tak'ama ne"?

Zabura! Balaraba tayi tana mutso-mutso, gashi har yanzu bai sakar mata baki ba, wani munafukin murmushi ya saki, yace" yarinya ko dame kike tak'ama bai dame ni ba, babu abunki wanda zai rud'ani kamar yadda yake rud'a wasu mazan, yanzu "yar uwarki tafad'a min wai inyi taka tsan-tsan dake, bata sani ba ni ko a k'afa aka d'aura min ke sai na kwance,na gudu"
yana gama fad'ar maganarshi ya sake tayi taga-taga zata fad'i sabuda rashin k'arfin jiki, shi kuma kamar walkiya ya b'ace daga gurin.

Kamar ta d'ora hannu aka haka takejin wani mugun d'aci a zuciyar ta, gabanta ne ya fad'i lokacin da ta tuno muryarsa sai taji kamar tasan mai irinta, tsugunawa tayi a gurin tana cusa fuskarta tsakanin k'afafunta tafashe da kuka wurjanjan! babban bak'in cikinta yadda wannan guy d'in ya samu nasara a kanta, gashi ta kasa gane fuskarsa duk da haske futula, tunda take a duniya babu namiji da ya tab'a kusantar ta kamar haka,sai shi har yayi nasarar tab'a mata jiki, bayan shi sai Sarki! ranar da suka zo tare da Moddibo, shima kuma bai yi a banza ba sai ta d'auki fansar abunda yayi mata, ta dad'e tana kuka a tsugune a gurun, daga bisani ta mik'e ta shiga gida, duk suna zaune a tsakar gida Sallau yana mayar musu da magana abunda ya faru, amma k'iri-k'iri yak'i futo da k'udin, tanaji Uwa! tana cewa"ai yadda Shamsiyya take f'adamin mutumin da yazo yayi mata, sabuda haka ko ya sake dawo wa ka had'ashi da ita kawai, amma me za'ayi da waccan mutsiyaciyar yarinyar, nan sukai ta zagin Balaraba, gami da mata mugun baki, duk tana jinsu a d'aki, abunda ya hanata kwana a gidan da ta kama haya shine, babu fenti babu shara, yanzu futar da tayi ma kenan, domin tasa yara su share mata gidan, tunda anyi fenti da yamma, haka ta kwanta tasa su Sadiya da Usuman a gaba tana kuka tunda take bata tab'a kukan maraici ba sai yau

*Comeent Vote and Share*
[21/07, 06:17] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^°
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®{REAL BINTU BATULA}👄*

_*MARUBUCIYAR*_
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
```{RAHAMA ALIYU}```

_ZAMANI WRITES_
_ASSOCIATION_🤝🏻

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

*🅿55*

Da wuri ta tashi tayi shirye-shiryen ta, tsaf ta shiryasu Usuman cikin kayan makaranta, ta had'a musu shayi, suka sha, itama ta had'a tasha, tana zaune gefan katifa, wayarta tafara k'ara tana dubawa taga Moddibo ne, sai ta kusa katsewa ta d'auka, ajiyar zuciya taji yana saukewa,sai ya bata tausayi , sallama tayi cikin muryar ta mai dad'in sauraro, yace"Gimbiya kin tashi lafiya"?

"Lafiya k'alau, kai fa"?
" Nima k'alau na tashi, jiya nai ta kiran wayar ki tun safe a kashe, gashi baki futo kasuwa ba"

Cikin nutsuwa tace"wallahi kuwa na kashe ne sabuda ina da uziri,nagode sosai"

" Wane uziri ne wannan, da alama kina cikin damuwa"
yafad'a da cikin tausayin ta gami da so da k'auna

A jiyar zuciya ta sauke, tace" yanzu zan fito zan kira sai muhad'u domin maganar ta wuce a fad'eta a waya"

"Ok toum in sha Allahu yanzu zan futo sai mu had'u, amma kicire damuwar komai a ranka kinji ko"

K'walla da take k'okarin zubo mata take k'okarin mayarwa tace" nagode Yusuf sai mun had'u"
kashe wayar tayi ta aje gefan katifa, ta cigaba da kurb'ar ruwan shayin ta, sha takeyi kawai amma zuciyarta babu dad'i,, tana jiyo hayaniyar mutan gidan a tsakar gida,, Uwa sai cinikin awara take babu abunda ya dameta

A nutse ta futo daga d'aki nta ta jawo k'ofar gami da sanya mata kwad'o, Lantana na tsaye bakin k'ofar futa hannunta rik'e da wani k'aramin buhu da alama kasuwa zata shiga, wani kallon banza ta watsawa Balaraba, ta ci gaba da magana da Uwa! dake zaune a kujera "yar tsugono tana faman soyawa a wara, gaishe su tayi, suka k'i amsa wa, tace" Matar Kawu Ina antashi lafiya"?
Sadiya dake sunkuye tana wanki bakin rijiya tace"lafiya lou Balaraba,kin futo"?
"Eh matar Kawu"
Balaraba tafad'a tana k'okarin barin gurin.

"Allah ya bada sa'a"
Matar Kawu tafad'a ta cigaba da wankin ta.

"Ameen" Balaraba tafad'a ta nufi kofar d'akin Iya.

Iya jiki yayi sauk'i suka gaisa a gurguje, ta aje mata kular abuncin su Sadiya tayi mata sallama ta futa.

Ashiru yana cikin Napep yana jiran futowar ta, dan haka tana shiga suka gaisa, cikin mutumci yaja Napep din suka bar Unguwar.

Daf da zasu shiga kasuwar wayar ta tayi kara, tana dubawa taga Modibbo ne, d'aga wa tayi tace" Ina titin jark'asa yanzu, zan tsaya dai-dai masu sai da lemo da a yaba sai kasame ni a nan"

"Ok gani nan zuwa"
Moddibo ya fad'a gami da kashe wayar.

Futa tayi daga Napep d'in ta sallami Ashiru,

Nik'ab d'inta ta futo dashi ta sakaye fuskar ta,sabuda zurga-zurgar jama'a duk da safiya ce, ko minti goma batayi ba, taga wata mota mai kyau tayi parking a gabanta, d'auke kai tayi domin tasan ba motar Moddibo bace, futowa yayi yana murmushi, yace"Gimbiya wannan shan k'amshin naki yana burge ni, gaskiya dole maza su dunga jin shakkar ki"
jin muryarsa yasa ta waigo da murmushi a fuskarta tace"barka da zuwa"
"Barka kadai Gimbiya,shigo mota mana" yafad'a yana bud'e mata k'ofar motar, tunda take bata tab'a shiga motarsa ba sai yau, sabuda haka a nutse ta shiga, ya mayar da murfin ya rufe, ya zagaya ya bud'e ya shiga shima,

"Maddibo ya kalleta a nutse yace" wannan nik'ab d'in yayi miki kyau Gimbiyata"

K'okarin cirewa take, tace"kaga ni ko ala dole nake sashi sabuda kallon da ake damuna dashi"

"Nima kinyi min gata"
yafad'a da murmushi a fuskarsa,ya cigaba da cewa"da zaki dinga sawa daga nan har lokacin auran mu"

Kallonsa take cikin nutsuwa tace"Yusuf da gaske kana sona"?

"Kwarai kuwa"
yafad'a cikin shauk'i yau gashi ga ita

Idanun ta ne ya fara tara ruwa tace"zaka iya aure na dani da k'anne na biyu wato Usuman da Sadiya"?

Cikin tausayi yace"kwarai kuwa, duk abunda kike so ina so balle Usuman da Sadiya Gimbiya ki kwantar da hankali, in sha Allahu zan rik'e ko da amana"

Hawaye ne ya fara zuba a fuskarta, taso ta danne kukan amma yak'i dannuwa, tace"Nagode sosai, inaji a rayuwata bani da mai k'aunata kamar ka, na auna ka sosai na lura tsakani da Allah kakeso na, ba wani abu nawa ne yake burgeka ba,shiyasa na yanke shawarar tsayar dakai a matsayin mijina kuma Uban "yayana, sabuda haka in ka shirya kawai ka futo muyi aure in huta da bala'in da nake ciki"

Shima kamar zai yi kukan yake rarrashin Gimbyar tasa duk hankalinsa ya tashi, yace"kinyi magana a kan gab'a Gimibiya, dama ke kad'ai nake jira ki amunce min naj dad'i insha Allahu zaki futq daga halin da kike ciki zan aure ki domin kyawun halinki,ba dan kyau da wani abu naki ba, ni ina sonki tsakani da Allah" ya karasa maganar jikinsa na kyarma, ji yake kamar ya yaye mata damuwar dake damunta.

Rarrashin ta yake har sai da ya ga damuwar da take ciki ta ragu, domin har dariya tai masa,sai suka cigaba da hirarsu cikin so da k'auna, yace"yau baza ki shiga kasuwa bane"? girgiza kao tayi tace"yau bazan shigaba,zan koma gida ne, domin a kwai sauran aiki da nabari, zan tare a sabon gidan da nakama haya" gabanshi ne ya fad'i yace"kamar yaya kin kama haya? haya wace iri"?

Sunkuyar da kai tayi tace"har gida mana"

Cikin mamaki yace" Gimbaya kin kama hayar gida, kikace min maganar babu dad'in ji, ke baki san yanzu sai ki zama abin kwantacce ba, ne, kamar ki budurwa kina zaman kanki,gaskiya ban amunce ba"
ya k'arashe maganar da b'acin rai a fuskarsa.

" Yanzu ya kakeso ayi ne"
tafad'a da damuwa a ranta, domin bata son tona asirin gidansu"

Sassauta murya yayi yace"ki bar maganar kama hayar gida kiyi hakuri ki koma gidanku ki cigaba da zama kamar yau ne komai zai huce"

"Shikkenan, zan bi maganar ka"
tafad'a cikin tausayawa kanta"

" Yawwa nagode Gimbiyata, yafad'a fuskarsa d'auke da murmushi najin dad'i

Wayarsa ce tayi k'ara yana dubawa yaga Sarki! ne, Balaraba ya kalla fuskarsa d'auke da murmushi yace"ga mutumin ki fa"

"Wanene"?
tafad'a cikin rashin sani

" Sarki ne"!

Shan kunu! tayi ta d'auke kanta, murmushi yayi kawai ya girgiza kai tana ji yana masa magana yana amsawa sama-sama, da alama wani abun yake tambayarsa, yana gama wayar ya kalleta yace" muje in kanki gida, yana can yana jirana yanzu"

" A ya mutse tace"gashi ni kuma bangaji da ganin ka ba, sai yaya kenan"?

Agogon hannunsa ya kalla da murmushi a fuskarsa yace"Kiyi hakuri in kin bani dama zan shigo da daddare mu k'ara gaisawa, yanzu muhimin abu ne yasa ya kirani"

Tab'e baki tayi tace" wannam d'an rainin hankalin wallahi na tsane shi"

Cikin mamaki yake kallon ta fuskarsa ta janza da yanayin damuwa yace"har kike rantsewa Gimbiya yanzu d'an uwan nawa kika tsana"?
Chapter 34 · 0% Book details