← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 80

Sashe 40

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kicin-kicin da fuska Balaraba tayi tace"ka gafarce ni Yusuf, ko maganar da zanyi maka zata b'ata maka rai, gaskiya kayi masa magana jiya cikin dare ya shigo d'akin nan, gaskiya ni ban yadda ba"

Wani iri yaji a zuciyar sa, jin abunda tace"me ya kawo Sarki! d'akin, ya san halin d'an uwanshi ba mane min mata bane,kuma bazai ci amanarsa ba, Sadiya tayi Sauri tace"A'a Yayarmu ya ganni a wajan d'akine shine ya bani magani nasha ya rakoni na kwanta yace kuma in daina futowa cikin dare"

Moddibo yace"yanzu naji,zance, kiyi hakuri Gimbiya babu abunda zai faru sai alkairi ba halin Sarki! bane abunda kike nufi"

d'an tab'e baki tayi kawai tayi shiru yace"Ku tashi mu sauka k'asa Ku gaisa sai Ku karya"
M'ikewa sukayi duka suka nufi k'ofa.

Karo sukaci dashi zai hau saman shima, ratse masa sukayi a baranda har ya k'arasa hawowa Mariya baiwarsa ce take bayansa da'alama gyare-gyare zatai masa Wanda takeyi kusan kullum duk safiya, murmushi ya sakarwa Sadiya, sam ! baki kalli inda Balaraba take tsaye ba, ciki-ciki tace"Ina kwana"?
yaci albarkacin Yusuf Moddibo.
A dak'ile ya amsa, ya mik'awa Sadiya hannu, yarinya mai sauk'in kai da wayewa sai ta sanya hannuta cikin nasa tana yar dariya tace" Magajin Sarki ina kwana"?
Cikin mamaki yake kallonta sai kuma ya kalli Moddibo cikin tuhuma yasan shine zai fad'a mata wannan sunan, saboda ba kowa ne ya ke kiransa dashi ba,

Murmushi Moddibo yayi, shi kuma ya tab'e baki kawai yaja hannun Sadiya suka nufi d'akinsa, Sakin baki Balaraba tayi kawai tana kallon ikon Allah, shi kuma yana sane ya sakarwa yarinyar fuska duk Dan ya muzgunawa zuciyarta, saboda yana bala'in jin ciwon zargin da take masa a kan yarinyar,baya ga haka ma, yarinyar ta kwanta masa,tana da hankali da nutsuwa ba kamar yayar ta ba.

*Comments Vote and Share*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

_*MARUBUCIYAR*_
```Nana Khadija```
```Yaro Da kud'i```
```Gimbiya Balaraba```

_*ZAMANI WRITERS*_
_*ASSOCIATION🤝🏻*_

_*DEDIGATED*_
*_TO_*
```RAHAMA ALIYU```

```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM```

*🅿62*

K'asa suka sauka zuciyarta tana mata sak'e-sak'e kan zak'ewar da taga mutumin nata yayi kan Sadiya,sam bata yadda dashi ba, ganin yadda yake wa mutane wani irin kallo, kullum ido a lumshe kamar munafuki.

Ko da suka sauka k'asa hadimai ne su wajan biyar maza biyu mata biyu suna aikin gyara falon,kowa da inda yake gyarawa, jikinsu sanye da wasu kaya iri d'aya masu kamar Uniform, wani k'amshi ne mai dad'i ya cika hancinta, wani ku-ku ne ya futo daga kchin hannusa dauke da wani tank'asheshan faranti cike da abubuwan ci, Balaraba tayi saurin kauda kanta domin bata so tayi k'auyanci irin na jiya, hannun Usuman ta kama suka ni bayan Moddibo,inda ya nufi
Wani k'ebantaccan guri a falon, yace da Usuman ya zauna, yaron ya zauna cikin wata k'aramar kujera mai taushi, zama tayi itama tana bin gurin da kallo gaskiya k'ayatuwar gurin ya burgeta sosai dagani gurin hutawa ne,

D'aya daga cikin hadiman dake aiki a gurin ne ya k'araso ya zube gaban Moddibo yace"ranka ya dad'e a kwai abunda za'ayi ne"?

A nutse Moddibo yace"ka kawo abun kari na mutum hud'u"

Cikin bin umarni ya mik'e daga gurin.

Cikin nutsuwa ta kalli Moddibo tace"ya kamata fa ka kira Sadiya haka"

" Yanzu zai sauko ai wanka ya hau yayi"
Shiru tayi kawai tana d'an ya mutse fuskar ta, tace"tsarin gurin nan ya burgeni Yusuf ina so abu White coulor" Murmushi yayi yace"lallai tsarin ku d'aya da mutum min in kin lura ai duk adon falon nasa white ne"
Shiru tayi tana da tasanin fad'ar maganar, minti biyu tsakani yace"zan shirya miki falon ki da wannan colour"

"Nagode"
Abunda tace kenan,tayi shiru kanta a kasa tana wasa da hannuta

Tsura mata ido yayi,kurum yana kallo, ta d'ago kai tana kallonsa suka sakarwa juna murmushi, tace"wannan kallon fa,Yusuf"?

Da murmushi a fuskar sa yace"kallon soyyaya ne Gimbiya zuciyata tana fad'a min akwai wani babban al'amari da zai faru a tsakanina dake"

Itama Murmushin take,tace"babban al'amari ai bai wuce na aure na da kai ba, dama ina so in tambaye ka a wace matsaya muka tsaya,nifa zama anan kamar a kan k'aya nake"

" Karki damu insha Allahu yanxu in na tashi daga nan gurin me Martaba zan wuce, za'ayi komai a gama cikin kwanciyar hankali"

Ajiyar zuciya ta sauke,ya cigaba da cewa"maganar gurin sai da abuncin ki ki bar wa su Hauwa'u su cigaba da samu a ciki, in sha Allahu xaki fara business in munyi aure"

Cikin murna da farin ciki take masa godiya,a bisa karamcin sa a gareta, tanaji a yanzu bata da babban masoyi kamar sa, zata dunga k'okarin danne damuwar ta duk Dan ta kwantr masa da hankali, Salmanu ne, ya k'araso gurin hannunsa d'auke da wani faranti me fad'i ya aje a tsakiyar su, Moddibo yace"jeka abunka kaji" godiya Salmanu yayi ya bar gurin, Sauri-sauri yake ya gama abunda yake yaje ya fesawa abokinshi Dauda labari,shi Dauda yana b'angaran uwar gidan Sarki wato, Kulu,mai d'akin kudu, kenan Mama Kulu kenan,

A nutse suke karyawa ita dashi, kana ganinsu kasan masoyan asali ne,Wanda suka yarda da Kansu, Usuman na gefe yana karyawa shima.

Cikin nutsuwa yake sakkowa daga sama step by step hannunsa na rik'e dana Sadiya, yana sanye da wasu kaya na alfarma, masu tafe da wata alkyabba, kafarshi sanye da wani takalim me gidan ya tsa, babu nad'i a Kansa, duk da cewar shigar dake jikinsa ta nad'in ce amma bai yi ba, cewarshi ya gaji da kayan nauyi, sumarshi ya gyara,sosai da gemunshi, sai sheki yake,d'an k'aramin bakinsa mai d'auke da siraran lips Wanda suka d'an yi duhu kad'an, yayi Kyau kwantaccan gashi ya kewaye shi, as'usul idanunshi a lumshe kamar ko da yaushe,sai k'amshi yake zubawa, yana sakkowa masu hidima a gurin suna zubewa suna kwasar gaisuwa, ko wanne munafurci fall a abakinsa saboda ganinsa da k'aramar yarinya "yar shekara goma, cikin yanayin tafiyarsa ya nufi, daining teble d'insa Wanda yake cike da abubuwan ci, dai-dai inda suke zaune yazo ya gifta Balaraba taji gabanta yana fad'uwa duk da cewar ba ta kalli fuskarsa ba,gefansa ta kalla, Yanayin kwarjinsa da yadda yake tafiya cikin k'asaita ya furgitata ko ba'afad'a an San d'an mulki ne shi saboda abun a jinsa yake, jin kamshin turaran sa yasa Moddibo saurin waiwayo wa sai yaga yana k'okarin zama kan kujerar daining d'in, ga Sadiya ta zauna itama, ku-ku shi na tsaye gefe,yana jira ya dai-dai ta zamansa yafara had'a masa,abin kari.
Mik'ewa yayi ya bar Balaraba a gurin ya nufi inda Sarki! yake zaune, sukai yi magana sama-sama,batajin abunda suke cewa, saboda a kwai tazara a tsaksninsu can ta hango,Sadiya ta zage sai kwasar girki take, babu wani kamun kai sosai yarinyar ta bata haushi, Moddibo ne ya k'araso inda take,tayi saurin kauda kanta saboda wani lokacin shima haushinsa takeji in taga yana wa Sarki!rawar jiki.
"Gimbiya zanje in gaisa da mutan gida,zuwa yamma zan shigo sai muk'arasa maganar mu, don Allah ki cire fargar ba komai a ranki"

A sake tace"shikkenan sai ka dawo a gaishe min dasu"

"Zasuji insha Allahu"
Yafad'a yana k'okarin barin gurin.

Bayan futar Moddibo daga falo,sai yayi shiru saboda duk masu hidima a gurin sun gama sun futa,sai sautin AC ne kawai yake tashi, Usuman can gefe yake yana ta "yan wasaninsa, sai taji zaman gurin ya gundure ta, taja tsaki ya kai sau biyat r in ta d'aga kai ta hango Sadiya,na cin abunci ta sake sosai dashi tana masa hira har da dariya.

Sam! tak'i yarda su had'a ido dashi, a sace take k'are masa kallo yana cin abunci cikin nutsuwa, gashi fuskarsa a sake,yana sauraron hirar da Sadiya take masa,cikin zuciyar ta take ayyana irin dukan da zata yiwa Sadiya.

Taku! tafaraji k'was!k'was!k'was! irin na mace, takun takalmin ya d'auki hankalin ta har shi uban gayyar, da yake can inda yake zaune saitin k'ofar shigowa ne, shiyasa ya ga wacce ta shigo Gimbiya Halisa ce, Balaraba na zaune can wata kusuwar wa shiyasa bata ganta ba,

Halisa tana tare da wasu bayi guda biyu suna take mata baya, wanda suka tsaya bakin k'ofar shigowa, can inda ta hange shi zaune ta nufa fuskarta babu walwala,ganinshi zaune da wata,daga can nesa tana yiwa Sadiya kallon wata k'atuwar budurwa, shiyasa ta sha kunu,sosai tana tunanin me ya kawo mace har falonsa duk da tasan halinsa ba ya Neman mata.

Giftawar ta Balaraba ta hanga,ta bita da kallo daga sama har k'asa, tana ganin yanayin shigarta ta gane," yar sarauta ce.
Sarki! kuwa d'auke kansa yayi daga kanta har ta k'araso gurin ta tsaya gami da d'ora hannuta kan kujerar da Sadiya take zaune tana mata wani kallo irin na raini tace"Habibi wannan yarinyar a ina ka samo ta,naga sam ba jinsin mu bace"

Banza yayi mata,kawai ya cigaba da cinsa abuncin sa a tsana ke,

K'ara maimata maganar tayi,ya d'ago kansa cikin jin haushin ta yace"ban sani ba, ki kauce daga kan mutane tunda ke baki da ladabi da sanin ya kamata"

Ganin ya hasala! yasa ta fara yak'e tace" tunda na shigo na ganka zaune da mace a guri guda naji hankalina ya tashi shiyasa na rasa nutsuwa ta, sai da na k'araso kuma naga ashe ma yarinya ce,amma dai duk da haka hankalina bai kwanta da ita ba,yarinya sai kace,me dubi yadda take k'walo ido kamar mayya"
Karaf! a kunnen Balaraba,dama taji abunda Halisa tace a farko Dan gane da Sadiya.

Ranta a b'ace ta futo daga inda take,ta tsaya a gurin tana kallon su, a cunkushe ta bud'e baki tayi magana, tace"ke! Sadiya baro gurin nan, kinji ko"
Duk hankalinsu ya koma kanta har shi,uban tafiyar, ganin fuskar yayar ta a murtuke ya fad'ar mata da gaba,sai ta fara yunk'urin mik'ewa tsaye domin ta cika umarnin ta, yayi saurin dafe hannun yarinyar ya hanata tafiya, ido ya zubawa Balarabar dake tsaye can gefe tana cika tana batsewa, ganin Sadiya tak'i tasowa yasa ta k'ara buga mata tsawa,a karo na biyu.
A nutse ya d'an daga muryarsa yace"tak'i zuwa d'in in kin isa kizo ki jata,da k'arfi mugani"

*Comments Vote and Share*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

_*MARUBUCIYAR*_
```Nana Khadija```
```Yaro Da kud'i```
```Gimbiya Balaraba```

_*ZAMANI WRITERS*_
_*ASSOCIATION🤝🏻*_

_*DEDIGATED*_
*_TO_*
```RAHAMA ALIYU```

```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM```

*🅿63*
Chapter 40 · 0% Book details