Sashe 42
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ransa a mugun b'ace ya d'ago Kansa ya zuba mata idonsa,masu kwarjini,tuni tayi k'asa da kanta tana sharar hawaye
Yace"dukanin ku ke da ita Azimar babu zab'ina a ciki, ke kin kasance zab'in Mamana,ita ta kasance zab'in Waziri, duk zan aure ku ne ba dan inaso ba,sai dai n in cika umarnin magaba tana"
Shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa na fad'a miki ne saboda ki sani kuma ki shirya, saboda kin fi kowa sanin halina bani da munafurci kuma bana san hayaniya, da fitina,wanda na lura ke haka halin ki yake tada zaune tsaye, idan anjima zata zo nan domin ta kawo min ziyara zan tara Ku guri guda dake da ita,ku fahimci junanku, kar wata b'araka ta futo daga gare ki, nasan halinki, in xaki kwantar da hankalin ki ki kwantar domin ke da ita ba da ku kad'ai zan zauna ba,kin fi kowa sanin yaya tsarin masaraurmu yake"
Kuka mara sauti Halisa take,lallai tana cikin tsaka mai wuya, yanzu ta tabbatar da cewar Baba Waziri baya k'aunarta tunda har ya had'a "yar abokinsa aure da masoyin ta, ita da take burin taci lokacinta ita dashi kafin ya kawo wata,tasan ta more kuma sunsha soyyaya, yanzu ko auran a kayi tilas su raba kwana ita da Azima.
Tunda ya gama maganar shi,ya kishin gid'e kan kujerar ya lumshe idonsa Allah kad'ai yasan abunda yake damunwa, yana jin kukan Halisa yak'i k'arewa ya bud'e idonsa wanda suka d'an yi ja kad'an, yace" kin cika min kunne fa da gunjin kuka, kije ki tambayi Baba Waziri yadda a kai haka ta faru tunda na lura ke baki da kunya, har kina cewa an yaudare ku"
Yadda ya fad'i maganar da yanayin b'acin rai! yasa ta gane tayi kuskure domin Sarki! mutum ne wanda baya saurin nuna b'acin ransa da wuri, in ransa ya b'aci a yanayin maganar sa zaka gane, mik'ewa tayi ta nufi kujerar da yake zaune, ta rab'a jikinta a jikinta harda langwab'e kai, ta rik'e hannusa guda, d'aya, tayi k'asa da murya ta sosai tace" Allah ya huci zuciyar Habibi na, zuciya tana azabtuwa da so da k'aunar ka, shiyasa na rasa tunani na,lokacin da naji wannan maganar,ina kishin ka,mutuk'a bana k'aunar ko wace mace ta rab'eka sai ni,amma ina ganin burina bazai cika ba, Habibi nasan Azima ciki da waje,zata aure ka ne da wata manufa,a zuciyarta, gaskiya banso Azima zata kasance matarka ba, amma tunda haka Allah ya hukunta mama zan cigaba da tayaka addu'a"
Yanayin yadda tayi masa magana a nutse yasa yaji ta bashi tausayi, gyaran murya yayi gami da d'an gyara zaman sa,a nutse yace"ki koma inda kike mana, na hanaki irin wannan"
Muryar shi bata futa sosai yayi maganar,
Mik'ewa tsaye tayi tana gyara alkyabarta tace"tafiya ma zanyi,yanzu sai anjima zan shigo,da kamar k'arfe nawa zata zo"?
Tafad'a cikin sigar tambaya.
"Hud'u zuwa biyar na yamma"
"Shikkenan to"
Tafad'a a sab'ule jikinta babu kuzari ta futa daga falon
To,can gidansu Balaraba kuwa,babu wanda ya damu da rashin dawowar ta gida da wuri har wajan k'arfe tara da rabi na dare bata shigo gida ba, Iya hankalinta ya tashi ta futo ta nufi d'akin Sadiya matar Kawu suna maganar,can sai ga Sallau nan ya shigo fud'un-fud'un yana sab'a babbar riga, Iya ta tare shi cikin damuwa tace"Sallau har yanzu Balaraba bata shigo ba,babu ita babu yaran"
Da sauri ya kalli k'ofar d'akin nata, cikin mamaki yace"to ina ta tafi mutsiyaciyar yarinya,me shegen yawon tsiya,ai gwara in aurar da ita,kar ta jawo min masifa"
Lantana ce ta bankad'a labulen d'akinta ta futo da futular k'awai a hannunta, tace"wai zancan me nakeji ne"
"Wannan munafurkar ce bata shigo gida ba"
Lantana tace"Oho! dai a banza, duk inda ta shiga ta dawo,dole ace da mijin iya baba mune dai tilas d'inta, ehee"!!
Sallau yace"ai ko guduwa tayi bazan fasa abunda na shirya a kanta ba, sai na d'aura auranta da Iro"
Lanatana tace"kayi min dai-dai, da taje ta jawo mana abun fad'a"
Uwa! na daga cikin d'aki tana sako baki, bak'in ciki da b'acin rai yasa Matar Kawu komawa gurin ta, Iya ma d'akinta ta koma tana addu'ar Allah ya tsare mata su Balaraba duk inda suke.
Lantana Sallau Uwa su Shamsiiya baccin su sukai babu abunda ya dame su.
Sab'anin Iya da matar Kawu baccinsu rabi da rabi ne, saboda fargaba,
Asubar fari suka dunga jin bugu, a gigice Sallau ya diro daga gado,babu salati babu komai yaje ya zare sakata, yana hamma! Idonsa duk kwantsa abun k'yamk'yami! d'an aiken gidan me gari ne yazo, Sallau gabansa ya fad'i yace"lafiya dai ko"?
D'an aiken yace"me gari yace"kazo yanzu-yanzu me Martaba ya aiko yana neman ku"
Saura kad'an ya fad'i saboda razana da yayi,baki na rawa yace"me nayi ni Sallau"?
D'an aiken yace"Ai ba kai ka dai zakaje ba tare dashi zaku"
Ihu! ne kawai sallau ba kurma ba,ya shige gida cikin tashin hankali!
*Muje zuwa*
[02/08, 18:14] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*
_*MARUBUCIYAR*_
```Nana Khadija```
```Yaro Da kud'i```
```Gimbiya Balaraba```
_*ZAMANI WRITERS*_
_*ASSOCIATION🤝🏻*_
_*DEDIGATED*_
*_TO_*
```RAHAMA ALIYU```
```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM```
*🅿65*
Lantana ce ta futo daga d'aki hannunta rik'e da butar alola, taga Sallau ya shigo wurjajan, kafin tayi magana ya tare,ta yana cewa "Lantana masifa ta same ni ,yanzu aike ya same ni,cewar muzo ni da me gari wai me Martaba yana neman mu"
Sakin butar tayi tafadi a gurin saura kad'an zaninta ya fad'i k'asa saboda tsorata da tayi,salati take tana sallalami, cikin tsora tace"Allah yasa ba wani laifin kayi ba"
Yace"yanzu dai zanje in ji, d'aki ya shiga yana tashin Uwa,ya fad'a mata halin da ake ciki,ko a jikinta ta koma tai kwanciyar ta
Wani kud'addan yadi ya d'auko ya sanya a jikinsa,ya d'auki wata daud'add'iyar hula ya kwafa a kansa ya futo da sauri,har yanzu Lantana na tsaye a tsakar gida,jikinta duk yayi sanyi, tarasa abunyi,ta kalli Sallau lokacin da ya futo,tace"Nifa inajin wannan shegiyar yarinyar nan ce ta ka k'arar ka gurin Sarki kasan ba kunya ce da ita ba"
" Ai in itace ma,kanta ta kai domin a gaban me Martaba zan zayyane masa abubuwan da take na fajirci"
Lantana tace"Kayi min dai-dai kar ka rage komai duk ka fad'a masa zinace-zinacen da takeyi"
Haka Sallau ya futa Lantana tana k'ara yi masa hud'uba.
Lokacin da suka isa fadar Sarki Almustafa a cike take, me Martaba yana sauraron k'urafe-k'urafen mutanan sa, sai da fada tayi sauk'i sannan me Martaba ya waiwayo kansu, suka k'ara mik'a gaisuwa, Sallau duk ya sare! da al'amarin ganin yadda me Martaba yake yanke hukunci cikin adalci a bawa me gaskiya,gaskiyar sa, mara gaskiya a bashi rashin gaskiyar sa,sai gumi! yake sharcewa,
Cikin nutsuwa me Martaba, ya d'ora idonsa a kan me gari, Halilu, yace"Halilu ya al'amura da fama da jama'a"?
Me gari Halilu yace"Alhamdulilahi Allah ya taimake ka"
"Masha Allahu"
me Martaba ya fad'a yace"kasan wancan yaron"?
Sallau da
Me gari Halilu su ka kalli inda me Martaba yake nuna was,
Walidi ne zaune cikin dugayen kaya kamar bashi ba,sai Moddibo dake gefan sa,a zaune,
Cike da furgici Sallau yace"Walidi me ya kawo ka nan"?
Wani dogari ya buga matsa tsawa,gami da cewa"gyara kintsi!! nan ba gurin shirme bane"
Shiru fada tayi,na minti biyar me Martaba ya kalli me gari Halilu a karo na biyu yace"ina sauraron ka"
Sunkuyar da kai k'asa me gari yayi yace"k'warai kuwa Allah yaja zamanin ka,nasan wancan yaron farin sani domin yana d'aya daga cikin matasan gari na, yanzu haka ma muna tare da mahaifin sa,Allah ya taimake ka"
Ya k'arashe maganar yana sunkyar da kansa cikin ladabi,
"Alhamdulilahi"
me Martaba ya fad'a ya cigaba da cewa, " yaron nan yazo min da magana wacce naji bata kwanta min ba,wato kuna so ku had'a aure babu sanin kowa,hatta yarinyar da kuke so kuywa aure bata sani ba,kuma bata amunce ba, shine nasa aka kira ku inji kan wane dalili zakuyi haka"?
Sallau yayi karaf! yace"Allah ya taimake ka wannan yarinyar da kake magana a kanta nine mahaifinta,saboda nine wan ubanta,nafi kowa sanin halinta muguwar karuwa ce,yawo take tana bin maza,ga shaye-shaye,kwanaki ma har ciki ta zubar,shine ni kuma nake tsoron kar Allah ya tambaye ni amanar da ya bani yasa kawai nace gwara inyi mata aure in huta, to sai a kayi sa'a kuma d'an uwanta wato yaron gurina Iro yace yana sonta zai aureta a haka duk da mugun halin nata, nayi murna da naji haka,shine banyi k'asa a gwiwa ba,naje na siyo alawa da goro, na kai gidan me gari domin a d'aura auran bata sani ba, Allah ya taimake ka yanzu zan can da nake maka ma, tunda ta samu labari,mun nemata mun rasa tunjiya bata kwana a gida"
Fada tayi shiru tana sauraron maganganun da Sallau yake, kowa yana jiran abunda me Martaba zai ce"
A nutse ya d'ora idonsa kan Walidi,yace"kaji abunda mahaifin ka yace a kan "yar uwarka"
Walidi ya gyara zama sosai yace"Allah ya baka nasara,a rayuwarka, duk abunda ma haifina ya fad'a ba gaskiya bane, gaskiyar magana Balaraba kintstsiyar yarinya ce me gurin zuciya, nan dai Walidi duk ya fayyacewa me Martaba abunda yake faruwa, ya cigaba da cewa,maganar cewar Balaraba ta gudu, an neme ta an rasa, hakane, Allah ya taimake ka,Balaraba ta hannun Moddibo, shine ya taimake ta ita da "yan uwanta guda biyu"
Kallo ya koma kan Yusuf Moddibo musamman Mahaifin sa Waziri Zaiyyanu
Me Martaba yace"hakane Moddibo"?
A nutse yace"k'warai kuwa Allah ya taimake ka,yarinyar tana hannuna kuma ina me farin cikin sanar dakai cewar itace yarinyar da na fad'a maka inaso in aura"
Cikin mamaki me Martaba yace"jeka d'auko min yarinyar,ka kawo min ita,yanzu zan sa a kira min d'an uwanka,Almansur,domin shi nasa yayi min bunkice a kanta,shi kuma muji ta bakinsa"
A nutse Moddibo ya mik'e ya na kai gaisuwa, ya futa daga fadar,
Sallau kuwa duk rigar jikinsa ta jik'e jagab! ganin reshe yana nema ya juye da mu jiya, babban abunda ya d'aga masa hankali shine ,jin da yayi wai Balaraba na gidanan,kuma wai wannan da yayi maganar shike san ta da aure ,lallai asirinsu ya tuno.
[03/08, 19:52] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation