Sashe 59
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tamkar wacce aka aikowa da mala'ikan d'aukar rai! Haka ta kicin-kicin da fuskarta, cikin yanayi irin na b'acin rai tace"Wannan ba hurumin ka ba, cewar maza nawa na kula ko nayi mu'amula dasu lokacin ina sana'ata, kai bari kaji wani abu da baka sani ba, yau kasan dashi, na Dade da sanin dama kanai min kallon "yar tasha me sai da abunci cikin kasuwa, babu irin maganganun da baka fad'uwa Moddibo ba,kan kar ya aure ni, kushe da hassada basa hana gamji toho nida Moddibo soyyaya ce ta tsakani da Allah, ina mutukar alfahari da sana'ata,kuma duk inda na shiga na futa naji ana zagin masu irin Sana'a ta sai inda karfina ya tsaya, saboda haka tun kafin magana tayi nisa mutukar kasan da wani k'uli a ranka a game da aure na, sai ka janye kawai babu Lallai babu dole a ciki"
Ta k'arashe maganar tana sauke ajiyar zuciya.
Fuzgo hannuta yayi tafad'a kansa, ya rungume ta tsam! K'irjinta ya dunga fat-fat! Shima nashi haka, muryar shi a tsark'e yace"Ni kike k'okarin zagi ko saboda kawai na tambaya ki, abunda nake da hakki akansa"
Da sauri ta fuzge jikinta tanai masa kallo na wani irin mutum mai baud'adan ra'ayi yasan yayi Abu ya nuna bai yi ba, babban abunda yake bata haushi dashi shine son ya tab'a mata jikinta.
"Sama-sama tace" Babu maganar zargi a magana ta,ai gaskiya ce tun yanzu naga take-taken ka, kayi hakuri idan na b'ata maka rai,da kalaimai na"
Tana gama maganar ta shige d'akin da suke kwana.
Kallonta yake babu k'iftawa har sai da ta shige dakin sannan ya d'auke kansa, yana sauke wata irin zazzafar ajiyar zuciya, kwata-kwata a "yan kwana kin nan, yana yawan jinta a cikin zuciyarsa, duk sanda ya tuna da cewar tayi mu'amula da maza ta shiga cikin kasuwa ta saida abunci,sai yaji wata irin kibiyar kishi ta soke, ranar sai ya yini yana kwance duk ransa a b'ace! Yana kishinta sosai da sosai.
Kasa daurewa yayi yasa yayi mata maganar.
***********
***********
***********
Lantana na bayan mota duk tayi tsuru-tsuru sai zare ido take, burinta kawai ta isa gidan ta ganta gata ga Balaraba sai ta fara gudanar da aikinta.
👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*
```MARUBUCIYAR```
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*
_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________
_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_
*🅿93*
Kai tsaye shashen Mama Fulani suka nufa,, bayan Buba yayi parking d'in mota suka futo cikin nutsuwa, Buba ya bud'ewa Lantana k'ofa ta futo daga cikin motar sai zare ido takeyi ganin wasu irin mutane manya-manya a shashen Mama Suna kaiwa suna kawowa kuwanne jikinsa sanye da kaya jajaye da k'aton ta wani, gefanta ya kalla taga wani tsaye hannusa rik'e da k'atuwar bulala sai zare ido yake ga idanunsa sunji kwalli rabad'au, saurin d'auke kanta tayi tana k'ara damke abunda yake hannunta.
Ganin suna ta zubewa k'asa suna gaidasu Shatima ne yasa ta shiga taitayinta, ta dunga bunsu a baya simi-simi har suka shiga falon a tare.
Lantana ta tsorata da ganin irin had'uwar falon Mama Fulani ko ina ta kalla sai taga kalarshi daban, ga kayan alatu na jin dad'i da more ta yuwa, wani irin mugun kamshi me dad'i yana shiga hancin ta.
Tun daga bakin Kofa ta zube tana gaida Mama.
Cikin mamaki Mama Fulani tace"Bisimilah mana ki shigo daga ciki sai mu gaisa sosai"
Da k'yar Lantana ta mike ta isa kusa da Mama Fulani ta zauna a k'asa sai washe baki take.
Tana fad'in "Ranki shi Dade ashe ina da rabon ganin ki a duniyar nan, ashe jinina zai had'u da jininku,gaskiya nagode Allah nagode Muhammadu rasililahi"
Mama tayi murmushi kawai tana kallonsu Shahid nan yayi mata bayanin Lantana
Cike da farin ciki ta kalli Lantana tana fad'in "Gaskiya naji dad'in zuwanki sosai,dama nace aje a sanar daku halin da ake ciki,Gobe insha Allahu bayan d'aurin aure zan tura a d'auko sauran mutanan gida suma suzo ayi hidimar buki dasu"
"Lantana tace" Ai naji dad'in wannan abu ranki ya Dade nace Ashe da rabonmu muma zamuci arziki mu bar shi inda yake, haihuwa tayi mana rana"
Murmushi Mama tayi batace komai ba.
Su Shahid suka mike. Inda Shatima yake tambayar Sarki! Mama tace"Ya koma Shashen sa. Sallama sukai mata suka wuce Shashen Sarki!
Lantana ta dunga b'arin jiki sai zuba take tanaiwa Mama labari,tace"Ina angon namu yake ne yazo ya zab'a ko ni ko ita"
Mama bata iya surutu ba saboda ba d'abi'arta b'ace,gashi bata San wulakanta mutum sai ta dunga biyewa Lantana kawai domin karrama ta.
Jakadiya Shafa'atu ta shigo suka gaisa da Lantana, nan Mama take sanar da ita cewar kakar Balaraba CE,Jakadiya ta kara gaida Lantana cikin girmamawa, Mama tace, taje ta kira Balaraba dasu Sadiya su gaisa da kakarsu sannan Balaraba ta bata abunci, Sadiya da Usuman ne a gaba kafun Balaraba, da sauri suka ja tunga suka tsaya ganin Lantana a gurfane gaban Mama sai surutu take sai kace wata tsuhuwar redio, Sadiya ta juya da sauri zata koma suka ci karo da Balaraba tayi saurib tare ta tana tambayar ta menene"?
Bakinta na rawa tace"Yayarmu Lantance"
Da sauri ta kalli inda Sadiyar take nuna mata, Lantana ce, kuwa hankalinta na kan Mama basu ga futowar su ba, fad'uwar gaba taji, tana mamakin me ya kawo Lantana gidanan,, wata zuciyar tace mata kika sani ko Mama ce tasa aka d'auko ta.
Da kuzari a jikinta ta nufi inda suke, Binta sukayi a baya suna cike da tsoran abunda zai faru Usuman addu'a kawai yake a cikin zuciyarsa Allah yasa Lantana kar ta gudu dasu shikam yaji dad'in zaman gidan nan.
Lantana na hango Balaraba ta mike da sauri zaninta ya fad'i ta d'auka da sauri ta d'aura taje ta rungume Balaraba ta fashe da kuka tana fad'in "Ashe kina nan Balaraba, munyi neman duniya bamu ganki ba,Shima Sallau da k'yar ya koma gida ranar ashe alkairi ne a tartare dake Balaraba"
Wasu irin sambatu Lanatana ta dunga yi Mamaki ya kama Balaraba sai ta rik'e ta ta zaunar da ita tana fad'in ki zauna mana, don Allah ki nutsu sosai sai muyi maganar.
Ita dai Mama tana kallonsu cike da mamaki
Jiki narawa ta zauna tana hawo hannun Usuman yana fuzgewa yana komawa bayan Balaraba,
Tace"Zo nan Sadiya mu gaisa" k'in zuwa tayi yarinyar.
Fashewa da kuka Lantana tayi cike da munafurci da kitifi tace"kinga abunda nake fad'a miki ko Balaraba, dubi wai jina ne yake guduna duniya kenan"
Balaraba na jinta tasan dai makircin Lantana,, tace"Ki nutsu nu gaisa mana"
Jikinta na rawa ta hau gaida Balaraba, amsawa tayi kawai tana kunshe dariyarta ita Abunda Lantana take ya soma bata mamaki wallahi.
Mama kanta ta fuskanci rashin gaskiya gurin Lantana.
Da k"yar ta hillace ta suka nufi gurin cin abunci Lantana taka tunga ta tsayawa wai baza ta hau kan daining ba, haka ta had'a mata ta kai ta aje mata can wani k'ebabtaccan gurin Cin abunci take kamar wata jaka babu kamun Kai babu komai, Mama Fulani na daga gurin zaman ta tana kallon ikon Allah, Balaraba kuwa wata irin kunya ce ta kamata, a hankali tace "Lantana kici a nutse mana"
Ko saurarenta batayi ba,sai da ts cika Uwar hanjinta da kyau sannan ta tsame hannuta tana goge bakinta,,, Mik'ewa tayi ta koma falo kusa da Mama Fulani,,Tsaki Balaraba taja tana d'auke kanta,tanajin Lantana tana cewa Mama wai tana so ko bayan biki ta zata zauna anan"
Mama Fulani tace"Ai babu komai sai ta zauna d'in.
Mama Fulani dai shiru tayi musu ita da Jakadiya suke hira itama da tagaji sai tao shiru ta k'yaleta,, sai banbadanci takewa Fulani.
Mintu ashiri Mama ta kara a gurin ta mike tsaye tana musu sallama domin zataje ta kwanta, nan sukai mata sai da safe, ta shige d'akinta, Jakadiya ma sallama tayiwa Lantana ta mike ta nufi dakin kwananta.
Balaraba ta kalli Lantana da rai a b'ace tace" Ai sai ki tashi haka muje ki kwanta, wai don Allah meyasa kike haka ne"?
Lantana ta hau yak'e tana fad'in "Me na aikata " yar nan, baki San su irin wannan mutane dole sai kana musu banbad'anci ba"
Tsaki taja tana fad'in "To banda wannan masarautar ta masu hankali ce,don Allah ki dunga nutsuwa kar ki bani kunya gurin abokan zamana da mutanan gida"
Lantana tace"To naji zan kiyaye ai kina da damar da zaki fad'a min duk irin maganar da kike so, saboda Kinga zaki auri Sarki!
"Shiru kawai tayi mata tana surutai a cikin zuciyarta take fad'in ko wannan auren ya dama,ni a gurina sunan shi auran biyayya.
***********
***********
***********
*Komai yayi farko yana da k'arshe*
Cikin shiri sosai suka futo daga shashinsa gida ya cika ya tumbatsa baka jin komai sai busa da sarewa irin ta gidan sarauta, marok'a da magogo sai aikinsu suke, k'amshi suke ko ta ina Sarki yana cikin wata d'anyar Shadda gezner me mugun tsada anyi masa wani irin dinki babbar Riga da " yar ciki ita kanta hular dake kansa da da yankin shaddar aka had'a ta kafarshi sanye da wani takalmi rufaffe mai mugun kyau kalar kayan jikinsa sky blue yayi masifar kyau fysakarsa sai futar da annuri take, sajensa ya kwanta lif-lif a fuskarsa hannusa wani irin agogo ne, na zallahr azurfa, kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki da annushuwa, sai gaisawa yake da manyan mutane gwamnoni da "yan majslisa sanatoci da sauransu, " yan abokan arziki duk murna sukeyi da farin ciki.
Wata kujera ya nufa wacce a ka k'wata ta da shimfud'u na alfarma yana tafe su Shatima na take masa baya, zama yayi cike da k'asaita, wasu nayi dake tsaye suna jiran zuwansa suka hau yimasa firfita, Shahid da Shatima suka zauna gefe da gefan sa.
K'irari kawai kakeji da busa marok'a sun rud'e kowa da irin nashi rok'on kowa naso ace nashi yafi na d'an uwanshi.