← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 80

Sashe 68

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

```MARUBUCIYAR```

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_

_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

*🅿104*

Mama ta kalli Shafa'atu tace"Ki d'auki wannan kayan tsubbu kije ki k'ona su can bayan gida, ubangiji Allah ka rabamu da sharrin zuciya"

Jakadiya tayi bisimillah ta d'auki ledar dake aje gaban Mama ta futa daga d'akin domin taje ta aiwatar da aikin da aka sata.

Madabo tayi musu wani kallon banza tace"Ya kamata Ku zo a mai daku gida domin zama daku annoba ne,wallahi Fulani ki barni da halina kawai amma na tsani mutum me asiri wallahi"

Murmushi Fulani tayi tace"Na san halin ki ciki da bai don me yasa bakya shiri da Kulu ai saboda halin ta ne"

Madobo tace"Wallahi kuwa ai Kulu tayi nisa sai addu'a"

Mama tace"Ita kad'ai ce magani"

Shiru falon yayi, kunyar duniya ta ishi su Lantana sun kasa d'ago kai su kalli mutane,,Balaraba ma kanta na k'asa tana sak'e-sak'e, k'amshin turaran sa ne ya gauraye falon,, da sallama ya shigo cikin yanayin tafiyar sa ya zauna kusa da mamansa.

Kwarjinsa da haibar sa ya cika falon, Lantana duk dadewar ta a gidan bata tab'a ganin shi ba sai yanzu, bakinta na rawa tace"Ranka ya Dade ya barka da yamma"

A nutse ya galli gefan da take ya amsa Cikin yanayin muryar shi.

Mama tace"Kakar Balaraba ce nasan baka gane ko wacece ba"

Mai da ganinsa yayi kan Lantana wacce tayi muzu-muzu a zaune tana tsoran kar Mama ta fada masa halin da ake ciki,, minti biyu yana kallonta yaji sam matar bata kwanta masa,, a hankali ya Dora idonsa kan Uwa! Ta zaune sai gumi take cikin zuciyarta take cewa dama wannan ne Sarki! Almansur din? Lallai Allah yayi hallita a gurin,, ina Shamsiyya ina shi,, a ya zama dole ta sanar da Shamsiyya cewar ta daina wahalar da kanta ko mutuwa zatayi ta san Sarki ya fi k'arfin ta,, Ya mutse fuska yayi ganin wata koriyar kwanta a idon Uwa! Abun k'yamk'yami yace"Ita kuma wannan fa"?

A hankali Mama tace"Matar Kawun ta ce, sunanta Uwa!" Tunda yaji haka ya d'auke kansa zuciyarsa tana tashi tunda ya kalli fuskar Uwa! Babu kyawun gani,, gai sawa sukayi da Madabo cikin mutum ci da girmama juna,, ya gaida mahaifiyar shi a mutumce, falon yayi shiru kowa da abunda yake sak'awa a zuciyarsa

Tunda ya zauna a gurin yake so su had'a ido da ita,, Allah bai bashi iko ba, itama gane hakan ne yasa taki d'ago kanta sai kara sunkuyar da kanta take.

Mama ta kalle shi tana fad'in "Dama yanzu nake cewa a kira min kai zamu zauna da kai da iyalin ka"

Shiru yayi yana d'an Sosa kai as'usuel.

Gimbiya Halisa ta futo daga wani daki dake cikin falon tw cire alkyabar jikinta yanzu tana cikin wata muguwar shadda wacce akai mata mugun aiki mai bala'in kyau (sirfani) abunka da siririya sai dinki yak'i zama a jikinta sosai, duk cikin kayan lefansu take Balaraba na da irinta Azima ma haka.

Mama ta kalli su Lantana da suka muzanta tace"Yanzu sai Ku shirya a mai daku gida ko"

Lantana kamar ta kurma ihu shikkenan, taga samu taga dashi,inama ace Balaraba ta ce ta zauna mata

Jakadiya Shafa'atu CE ta dawo ta zauna Cikin nutsuwa,, Mama tace"Jakadiya kar ki gaji a had'a musu tsaraba zasu wuce gida"

Jakadiya ta mike tana fadin"An gama Uwar dakina"

Balaraba ta mike a nutse ta nufi dakin da take, duk wani Abu da tasan nata ne naci da na sawa ta had'a su guri guda ta futi dasu da k'yar,, zama tayi kujerar da ta tashi tace"Gashinan Ku raba Wannan nawa ne babu yawa,, Ku gaishe min da Iya matar Kawu"

Lantana godiya kawai take yau ta k'ara tabbatar da cewa Ubangiji mak'agin baiwa ne me yin yadda yake so da kowa wai tana raye a duniya Balaraba tayi aure kuma ta dauri Sarki! Lallai idan kace tukunyar wani baza ta tafasa ba to taka ma ko dumi baza tayi ba, tabbas taga ishara ta gane duniya ba komai bace, yanzu dole ta kwantar da kai suci su sha ta dalilin Balaraba..

*******
*******
*******

Shamsiyya tsugene a bakin kofar zauren Arrama ta buga-buga an ki budewa, wata zuciyar tace watak'ila yana ciki yana aiki shine ta tsuguna tana jiran ya gama,, wasa take da wani kara a hannunta taji zuciyarta tana wani irin tashi, da sauri ta mike taje bakin kwata ta dunga yunk'urin amai,, aikuwa kafin kice me sai ga wani amai Kore fatau tana kyalashi,, mutane suka fara taruwa a kanta suna tausayin ta,,wata mata tazo ta kamata ta mikar da ita suka samu dakali suka zauna, da k'yar ta dawo hayyacin ta sai haki take, matar tace"Yarinya daga ina kike haka ai gwara ki koma gida ki je ki huta"

Shamsiyya ta ya mutse fuskarta har yanzu tana jin tashin zuciya tace"Nazo gurin Arrama ne, tun d'azu nake bugu bai bude ba nace ko aiki yake ne"

Matar ta girgiza kai cikin takaici wato ire-ire "yan Matan da suke zuwa gurin Arrama ne, wannan wai duniya INA zaki damu bin malamai babu yara babu manya babu zawawara babu Matan aure da " yan mata, tace"Ai sai da kiyi hakuri jiya-jiyanan aka kama shi yanzu yana hannun hukuma saboda jiya wata buduwar yarinya tazo Ita da uwarta gurin nan cika yayi da d'an Adam tazo tana kuka yayi mata ciki wata uku shine sukaje suka d'auko "yan sanda a ka kamashi, to d'azu da safe labari ya same mu cewar ya kufce daga hannun " yan sandar ya gudu"

Shamsiyya ta d'ora hannu aka tana fad'in"Na shiga uku na lalace, Arrama me yasa zakayi min haka,, kace Saura kad'an aikina ya kammala shine zaka gudu baka k'arasa mun ba"
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

```MARUBUCIYAR```

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_

_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

*🅿105*

Yara suka fara taruwa a kanta sai kurma ihu! Take, da sauri wannan matar ta d'ora ta a hanyar gida tana tafe tana kuka kamar shashasha sai surutai take.

**********************
Mota a ka kawo su har k'ofar gida cike da kayan arziki, yaran unguwa suka yi dafifi suna shafa motar suna tsalle har yanzu sun kasa sabawa.

Yara matasa suka kwashe kayan da suka zo dashi suna shiga gadan dasu,, suka bi bayan su duk jikinsu a sanyaye,, Buba direba yaja motar sa ya tafiyar sa,, suna k'okarin shiga gidan ana k'okarin futo da Sallau a rirrike jikinsa yayi tsanani, Lantana ta rafka salati gami da fashewa da kuka tana fad'in "Ina zaku kai shi"?

Walidi Yace" Asibiti za a kaishi domin jikinsa yayi tsanani, nan ta bisu a baya tana kuka, Uwa! Kuwa gida ta shige tana matsar hawaye, Sadiya da Iya na tsaye tsakar gida cike da tausayin Sallau Uwa ta shigo gidan, kallo suka bita dashi ganin tana matsar hawaye domin sun d'auka ko ganin jikin Sallau ya rikice yasa ta kuka, zauna tayi a tsakar gidan tana kukan nadama.

Ko minti goma ba'ayi ba sai ga Shamsiyya ta shigo gidan tana kurma ihu, ta zube gaban mahaifiyar ta tana fad'in"Shikkenan Uwa! Aiki ya lalace "yan sanda sun kama Arrama jiya da yamma"

"Don Allah ni yi min shiru da zancan wani Arrama in zaki hak'ura ki hak'ura ki zauna inda Allah ya aje ki, ni kam. na dawo daga rakiyar wannan duniyar me cike da rud'u"
Uwa! Ta fada tana sharb'e hawaye

Shamsiyya ta d'ago kai tana kallonta cikin mamaki tace"Ban gane abunda kike nifi ba kina nufin in rabu da maganar aure na da Sarki! Ko me"?

"E abunda nake nufi kenan, Domin babu yadda za'ayi ya aure ki yana da Balaraba"

Shamsiyya ta fashe da kuka tana fad'in "Uwa kar muyi haka dake kinji, kece fa kika yi mana alk'wari cewa ko da zakiyi yawo tsirara sai in da k'arfin ki ya k'are zaki tsaya min gurin ganin buk'ata ta ta biya"

"Ke ni ki k'yaleni don Allah inji da masifar da nake ciki, ubanki ya sake ni saki uku, ga masifar Ku ta same ni, Nazo a banza zan koma a wofi ni yanzu waye zai aure ni" ta k'arashe maganar tana rusa ihu!

Shamsiyya ta dafa kirji tana fad'in "Baban bamu ne ya sake ni yau she haka ta faru"?

Nan Uwa ta kwashe duk abunda ya faru ta fada mata har da zuwan su gidan Sarki! Shamsiyya ta kwanta tana rusa ihu! Babu kamar wacce uwarta ta mutu

***********************

Suna zaune gaban Mama Fulani duk su ukun sai shi da ya zama cikon na hud'un,, yana hakimce kan kujera.
Mama tace "Salati goma da Annabi" Duk suka amsa da "Sallalahu alaihi wasalam"Minti goma tsakani tayi addu'a ta shafa suka shafa suma,, ta kalli Sarki a nutse tace" Babban abunda yasa na tara ku anan shine, in ja muku kunne gami da nasiha, mussaman kai" tafad'a tana nuna shi da hannu, kansa ya sunkuyar kasa, ta cigaba da cewa"Allah ya d'ora maka wani babban nauyi a kanka na mataye har uku, dukaninsu suna da hakki a kanka babu wacce tafi kowa a gurin ka sai wacce tafi kyautata maka a cikinsu, don haka ina mai gargadin ka da ka rike amanar su ka bawa ko wacce hakkin su,da ya rataya a kan ka"
Yace"Insha Allah Mamana kar ki damu"

"Ku kuma na dawo kanku"
Tafad'a tana kallonsu duk su ukun, ta cigaba da cewa"Ku yi kokari Ku kula da mijin Ku Ku fahimci me yake so da Wanda ba ya so, yi nayi bari na bari Ku yi k'okarin zama lafiya da juna domin Ku kwantar masa da hankali gurin ganin ya rik'e amanar Ku, da jagorancin mutanan gari da ya hau kansa, ni Wannan kawai zakuyi min Ku faranta min, insha Allahu , kuma idan wani sab'ani ya shiga tsakanin ku dashi, ba fata nake ba,, zama ya gaji haka zo mu zauna zo mu sab'a haka duniyar take, to sai Ku same ni Ku sanar dani insha Allahu komai zai zo da sauk'i"
Chapter 68 · 0% Book details