← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 80

Sashe 44

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsananin b'acin rai! Waziri Zayyanu ya shiga b'angaran sa,sai a kayi sa'a duk "yayan shi maza na zaune a falo suna hira, nan suka ga shigowar mahaifin su hankalin sa a tashe, Khalifa ne yace" Allah yasa lafiya dai na ganka kana faman gumi!
Zama yayi cikin kujera yana cire rawanin dake nannad'e a kansa,yace"je ka kira min mahaifiyar ka"
Tafiya yayi kiranta, ya kalli sauran yaransa da kumfar baki yace" in dai nine na haife ku daga yau na rabaku da Moddibo har abada babu ni babu shi hakanan kuma babu ku babu shi"
Cikin rashin fahimta Ishak yace"ban fahimci me kake nufi ba Baba"

Zuwan mahaifiyar tasu ne ya dakatar da maganar da yake tazo ta zauna kusa da mijin nata,tana kallon fuskarsa tasan lallai yau an tab'oshi"
"Lafiya ranka ya dad'e"?
Ta fad'a cikin sigar tambaya.

Waziri yace" zaki ce min baki san abunda yake faruwa bane? kun had'a kai da d'anki kun munafurce ni, yaje ya d'auko yarinya da suka gama lalacewa da ita a waje ya kawo wa wannan mak'iyin nawa ya d'aura masa aure da ita"

"Duk maganar da kakeyi ban fahimce ka ba,domin kuwa ni ban San abunda yake faruwa ba"

Girgiza kai yayi kawai ya umarci d'aya daga cikin yaran dake zaune a gurin yaje ya kira Moddibo.

Hankalin kowa ya tashi a gurin saboda sun san halin mahaifin nasu bai iya b'acin rai ba.

Mintuna goma tsakani Moddibo suka shigo tare da Ishak d'an uwansa

Ko zama Waziri Zayyanu bai bari yayi ba,yace"Umarni na ne ni ne nasa a kira ka, saboda dalilai masu k'arfi,yanzu-yanzu nake so ka furta cewar ka saki wannan yarinyar da kasa aka d'aura maka aure da ita,idan kuma kak'i ni yanzu zan saki taka Uwar,saboda haka zab'i ya rage naka."

*Muje zuwa*

*Comment Vote and Share*
[05/08, 20:08] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

_*MARUBUCIYAR*_
```Nana Khadija```
```Yaro Da kud'i```
```Gimbiya Balaraba```

_*ZAMANI WRITERS*_
_*ASSOCIATION🤝🏻*_
________________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_
________________________

_*DIDEGATED*_
_*TO*_
```RAHAMA ALIYU```

_BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_

*🅿68*

Dukaninsu sun furgita da jin furucin da mahaifin nasu yayi, ita kanta mahaifiyar tasu ta girgiza da furucin da mijin nata yayi,kuma tafi kowa sanin halinsa zai iya aikata duk abunda ya fad'a.

Modibbo ya shiga, tsaka me wuya bai tab'a tsammanin hukuncin da mahaifin nasa zai yanke ba kenan,iya tunanin sa yana ganin zaiyi fushi dashi daga baya ya sakko shi kuma sai ya nemi afuwar sa, tabbas Uwa-Uwa ce, babu ta yadda za'ayi ta sanadiyar sa ya rushe auran da aka d'aurashi sama da shekara talatin da wani abu,dole duk son da yake wa Balaraba ya rabu da ita ko da hakan zai yi sanadiyar rasa rayuwarsa, a kan mahaifiyar sa babu abunda ba zai iya ba.
Khalifa ne mara kunya sosai ya cikinsu yace"Mu baza ka jawo mana b'acin rai!ba a cikin gida saboda haka kabi umarnin da a ka baka, idan ba haka ba zamu b'ata maka rai kuma zamu hana matar taka daka aura jin dad'in duniya,a kan mahaifiyar mu,babu abunda baza muyi ba"
Jin furcin da Khalifa yayi yasa Waziri umartar sa da yaje ya d'auko takarda sa biro, aikuwa da sauri ya tafi, ita kuwa Hajiya Kattime tana zaune tana kallon ikon Allah bakinta ya mutu, takasa fahimtar komai, a wannan badak'alar da take faruwa.

Khalifa ya dawo hannusa rik'e da farar takarda da biro ya zo ya mik'awa Moddibo, guda d'aya, d'ayar kuma yaje ya kai wa mahaifin nasu ganin Waziri ya d'ora biro jikin takkada yasa Moddibo saurin dakatar dashi, da hannu jikinshi na kyarma! yayin da gumi yake zuba a jikinsa, ya d'ora biyu jikin farar takarda yayi rubutu kayi biyu,kamar haka.

_Ni Yusuf Moddibo na saki matata Balaraba Ayuba Tanko saki d'aya kacal, kan wani dalili guda d'aya, ina fatan Allah ya had'amu da ita a aljanar Firdausi_

Yana gama rubutuwa ya ninke takadar, zuciyarsa tana wani bugawa fatt!!fatt!fatt! Waziri Zaiyyanu ya mik'a masa hannu yana nufin ya bashi takardar, a hankali ya karasa inda yake zaune ya mik'a masa, bud'e takardar yayi ya karanta ya mayar ya ninke ta ya aje ta gefe,wani takarda ya kara cirowa ya mik'awa Moddibo cikin bada Umarni yace"Saki uku zaka rubuta mata,saboda nasan halin wancan mutsiyacin zai iya turasasa ka ka mayar da ita,don haka ban yarda da saki d'aya ba"
Cikin tsantsar b'acin rai Hajiya Kattime tace"Wannan abunda kake tsantsar jahilci ne da son kai, Allah da kansa shi ya hallici saki,kuma ya umarci da ayi shi,amma kuma baya son ayi din,saboda haka tunda ka tursashi ya rubuta saki d'aya saboda son zuciyar ka to ka kyaleshi haka, ba lallai sai an saki mace saki uku ba take sakuwa,saki d'aya ma ya hallata"
Cikin tsawa Waziri yace"Zakayi abunda na saka ko sai ka gama jin hudubar da mahaifiyar taka take maka"
Ganin Moddibo ya tsaya yayi shiru da takarda a hannu yasa Waziri ya d'ora biron dake hannusa a jikin takarda ya fara rubutu.

Moddibo ya rik'e hannunsa jikinsa zafi rad'au! muryasa a shak'e yace"Baba Waziri ka gafarce ni, idan nayi maka,laifi, ni Yusuf Moddibo na saki Matata Balaraba saki uku"
"Innalilahi wa inna ilaihi rajiun"
Shine abunda Kattime take fad'a zuciyarta kamar tayi bunduga tarasa wane irin bakar zuciya ne da mijin nata.
Mik'a masa takardar yayi a karo na uku yace"rubuta min da hannun ka"
Ganin babu abunda yayi saura yasa Moddibo ya rubuta ya mik'a masa, ya bud'e ya karanta tsaf, cikin bada Umarni yace"Ka tafi da kanka kaje ka kaiwa wanda ya d'aura maka auran" Moddibo ya karb'i takardar ya kama hanya, yana tafiya yana had'a hanya jiri yana kwasar sa,Allah yasa bangaran babu ma'aikata sosai, sai da ya futa harabar gidan sarautar sannan ya dai-dai ta nutsuwar shi,amma duk da haka duk Wanda ya kalleshi a lokacin yasan yana cikin tsananin damuwa, haka ya isa fada, lokacin ana shirye-shirye kiran sallaar magariba
me Martaba ya futo kenan domin shiga gida suka ci karo da Moddibo, yana kallonsa ya gane da akwai matsala, kafin yace komai Moddibo ya mik'a masa takardar hannunsa, da sauri maga takarda ya karb'a ya bud'e ya fara karantawa kamar haka.

_Ni Yusuf Waziri Zayyanu na saki matata Balaraba Ayuba Tanko saki uku,saboda wani dalili,ina rokon Allah ya had'amu da ita a aljanar Firdausi_

*Innalilahi wa innailaihi raji'un*
Kalmar da me Martaba yake ta maimai tawa kenan, kafin su ankara Moddibo ya zube a gurin yana wani irin murk'ususu, jini na fita ta baki ta hanci, ya rik'e cikinsa tamau! bakinsa na motsi,kalamar shahada kawai yake
Sarki! ne ya futo daga b'angaransa ya na d'aure da alwala,sai ya hango abunda yake faruwa saboda haka cikin sauri da sassarfa ya k'arasa gurin,lokaci mutane har sun taro, hankali a tashe ya tsuguna ya d'ora gwiwarsa a k'asa ya d'auki kan Moddibo ya d'ora a cinyarsa, cikin damuwa ya sanya gefen rigar shi yana goge masa jinin dake futa daga bakinsa, Moddibo ya rik'e hannunsa tamau!! wani hawaye yana zuba ta gefen fuskarsa, muryarsa bata futa sosai yace"Allah yayi bazan yi tsayin kwana ba, a duniya balle in rayu da yarinyar da zuciyata take mutukar so, d'an uwana ne kai ko na mutu kai na amunce da ka maye gurbi na gurin Balaraba, ka bata hakuri,ga tanan na bar maka amana son Balaraba wani b'angare ne na zuciyata na tabbata ko na rayu a duniyar nan to da soyayyarta zan mutu, Sarki! na baka amanar Balaraba"
Ya k'arashe maganar yana wata irin shak'uwa!
Cikin tashin hankali da damuwa me Martaba ya bada Umarni a dauko mota domin a tafi asibiti,Moddibo najin abunda ake sama-sama girgiza kai kawai yake domin shi yasan halin da yake ciki,,hannun me Martaba yake taso ya kama,ganin haka yasa Sarki!kamo hannun me Martaba ya had'a dana Moddibo, me Martaba ya rik'e hannun sosai yana kalmatussha hada, nan take Moddibo ya fara fad'a shima. "La'ilahaillallahu Muhammadur rasulullahi,sallalahu alaihi wassalam" Da wannan kalmar Moddibo ya cika, dai-dai lokacin da ake k'wala kiran sallahr magariba.
[07/08, 13:48] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

_*MARUBUCIYAR*_
```Nana Khadija```
```Yaro Da kud'i```
```Gimbiya Balaraba```

_*ZAMANI WRITERS*_
_*ASSOCIATION🤝🏻*_
________________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_
________________________

_*DIDEGATED*_
_*TO*_
```RAHAMA ALIYU```

_BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_

*🅿69*

Wata irin ajiyar zuciya Sarki! ya saki lokacin da ya ji jikin Moddibo ya shika a jikinsa, sai yayi zaman dirshan a gurin had'e da rungume gawar yana wani irin kukan zuci idanunsa sunyi jajawur!kalmar innalilahi wa'ina ilaihi raji'un kawai yake maimaita wa cikin zuciyarsa.

Kafin kace kwabo mutuwar Moddibo ta watsu a cikin gidan,mutane kowa na futowa daga b'angaran sa cikin tashin hankali, lokacin da labarin ya iski Waziri bai yadda ba,sai da ya tura Khalifa domin yaje ya gani gaske ne,aikuwa Khalifa ya dawo cikin tashin hankali,ya tabbatarwa da Mahaifin nasu hakane.

Waziri ya shiga cikin tsananin rud'u da tashin hankali,a gigice ya futo kafarsa babu takalmi ya nufi fada,zuciyarsa na yi masa sak'e-sak'en cewa Sarki Almustafah shine ya kashe masa d'ansa saboda wani dalili nasa.

Lokacin da ya isa,gurin ana ta k'okarin cire gawar Moddibo daga jikin Sarki! Abun ya gagara domin ya rik'e shi tam! wasu hawaye na zubo masa masu tsananin rad'ad'i, cikin zuciyarsa yake cewa shikkenan na rasa d'an kuwa nagari shikkenan narasa amini me share min waye, me yasa mutuwa zata d'auki Moddibo ta barshi,shi a duniya shima tabbas bashi da wani amfani a cikinta.

me Martaba ne yake ta rarrashin sa kan ya sake shi a d'auke shi daga gurin,gashi lokacin sallah yayi,amma tamkar da dutse yake magana,kwata-kwata Sarki! baya fahimtar abunda yake cewa.

Waziri ne ya k'araso gurin idanunsa a kan gawar Moddibo,kurrr!! Yake kallonsa kamar wani zautacce yace"K'arya ne, babu wani munafurci da ban sani ba,a gidan nan duk wani abu a dake shirya min ni da "yayana nasan shi, saboda haka, ni sai nabi kadin jinin d'ana Yusuf Moddibo"
Chapter 44 · 0% Book details