Sashe 21
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Comment*
*Vote and Share*
[06/07, 13:37] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
∆∆∆∆∆∆
_*GIMBIYA BALARABA*_
∆∆∆∆∆∆
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*MARUBCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```
_*Zamani Writes Association*_🤝🏻
```Bisimillahir-rahamanir-rahim```
*Real Bintu Batula👄*
*🅿39*
Hannu kawai ya dagawa Buba Dreba da sauri ya karaso gurin, Cikin nutsuwa ya mai da idonshi kan Maddibo yace"Ni zan wuce, naga alamar baka da ranar tafiya, ka kawoni gurin yarinyar mara tarbiyya tana neman ta zageni"
Cikin daga murya Balaraba tace,"to in na zageka me zaka yimin karkari kasa a daure ni to ka dade baka sa an daureni ba,kuma zakasan wanda ka tofawa miyau dinka,wallahi sai na rama kaji na rantse"
Cikin hayaniya take fadar maganar,hawaye yana kokarin zubo mata,
Babu zato taji wani sabon yawu a fuskarta ya kara tofa mata a karo na biyu, baice komai ba ya shige mota Buba Direba ya shiga ya kunna mota suka bace daga gurin.
Maddibo kamar ya dora hannu aka domin takaici da Sarki! ya kunsa masa, ya dauko shi domin yazo ya gyara masa lamarinsa gurin Balaraba, yazo ya bata daya goma bata gyaru ba,yanzu yaya zaiyi?
Cikin muguwar kunya gami da jin nauyi ya kalli Balaraba tana goge hawayen bak'in ciki,tana sane ta matse kukan batayi a gabansa ba,sabuda kar yaga gazawar ta, sai bayan ya tafi hawaye ya balle mata,kamar me tunda take a duniya babu mahalukin da ya taba yi mata tozarci irin na yau,dole ne ma sai ta rama wulakanci da mutumin nan yayi mata.
"Kiyi hakuri dan girman Allah,Balaraba, hakan ba halinshi bane, dana san abunda zai faru a tsakanin ku da ban gayyato shi ba,dama da yaya ya yarda zaizo din,kiyi hakuri dole zan dauki mataki akan haka,sabuda ke kanki kiba da daraja da mukami cikin zuciyata"
Fuskarta goge da hannuwanta duk biyun,fuskarta a hade tace" Ya kuke dashi,ma'ana menene alakar ka da gidan Sarki"?
Tsayuwa ya gyara sosai yana fuskantar ta, yace"Ni Sunana Yusuf kamar yadda kika sani, amma Mutan gida na kirana da Maddibo asali sunan kakanmu a gare ni shiyasa suke kirana da haka, Sarki Almustaph Wan mahaifina ne, Waziru Zayyanu"
Da sauri Balaraba ta dago kai tana kallonsa cikin mamaki!
Ya cigaba da cewa"Sarki! Almansor dan Uwana ne na jini kuma aminina abokina tare mukai karatu dashi tare muke rufewa mu kashe, amma halin kowan daga cikinmu daban yake da na dan uwansa, yana da saukin kai sosai in ka fuskance ki, amma bashi da hakuri ko kadan in ka tabashi, Mugun muskiline,sosai shiyasa nayi mamakin abunda ya hadaku haka kuke fadawa junanku bak'aken maganganu, da alama s kwai abunda ya taba hadaku a baya"
Shiru tayi na minti biyu ta kalleshi a nutse tace"kana kallonshi yayi min wulakanci har da tofa min miyau bakace komai ba, dama ka dauko shine domin yazo ya wulakantani ko, babu komai, Nagode"
Tana gama fadar maganarta ta kama hanya ta barshi tsaye a gurin,tafiya take kamar zata kifa jin zuciyarta take kamar zata kone sabuda tsabar turiri da take mata, da kyar ta kai kanta gidansu,
Maddibo ko binta da kallo yayi har ta bace masa, jikinsa a sanyaye ya futo da waya ya kira daya daga cikin Direbobin cikin gidan Maimartaba Sarki Almustaph ya fada masa unguwar da yake,yace yazo yanzu-yanzu ya dauke shi
Yana nan a tsaye a gurin, Sallau Direba ya karaso gurin Lokacin goma da rabi na dare,da sauri ya bude motar ya fito ya budewa Maddibo ya shiga suka bar unguwar,
Salihu Yana tukin mota yana mamakin me ya kawo Maddibo irin wannan unguwar, ya gaza hakuri ya yace"ranka shi dade nace Allah yasa lafiya, ko wani abune ya faru a unguwar ne"
"Lafiya kalau, nazo gurin wani abokina ne"
"Masha Allah Yallabai dafatan ka same shi lafiya"?
" Alhmdulilahi"
Maddibo ya fada yana jin zuciyarsa babu dadi,Sarki!
ya cuce shi, yanzu yaya zai yi ya shawon kan Balaraba,
Yana zaune a ka tafaran Falonshi shi kadai kwal, in banda karar AC babu abunda kakeji, yana zaune a wata kujera me cin mutum daya daga shi sai wando 3Quetar kafarshi daya kan daya kana kallon irin zaman da yayi kasan na masu mulki ne, Sigari yake zuka yana lumshe ido,zuciyarsa in banda zafi da turiri babu abunda take,jira kawai yake Maddibo ya shigo suyi ko wacce-wacce,domin yana ji yana gani bazai bari ya auri yarinya kamar wannan mara tarbiya ba babu yadda za'ayi ta shigo ta bata musu zuri'a.
*Comment*
*Vote and Share*
[07/07, 12:38] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
∆∆∆∆∆∆
_*GIMBIYA BALARABA*_
∆∆∆∆∆∆
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*MARUBCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```
_*Zamani Writes Association*_🤝🏻
_*DEDICATED*_
_*TO*_
```{RAHAMA ALIYU}```
*®REAL BINTU BATULA👄*
*🅿40*
```Bisimillahir-rahamanir-rahim```
Maddibo ne ya shigo falon cikin sallama,amma kana kallon fuskarsa kasan yana cikin bacin rai, kujerar dake fuskantar sa ya zauna sosai ya murtuke fuskarsa, yace" yace "Yanzu abunda kayi mun ka kyauta kenan, haka mukayi da kai ? a kan zakaje ka bata min lamarina a gurin yarinyar nan"
Hannu ya daga masa a fusace! ya mike zaune sosai ya gyara zamansa, yana kashe guntuwar tabar dake hannunshi cikin wani karamin plete wanda ke aje kan wani karamin teble dake gabanshi, a ya mutse yace "me nayi maka, zaka zo kana min wani shan kunu,ni ban yi magana ba,kai ne zakayi magana, haka kawai ina zama kazo ka dauke ni la kaini an ci mun mutunci, wannan bayi ba ne"
Ya karashe maganar yana huci!
Kasa Maddibo yayi da muryar shi ganin yadda Sarki! ya ke hayaniya, yasan halin bakar zuciyarsa yanzu sai ayi batacciya shi dashi,shiyasa ya kwantar da kai, dama kuma (Annabi muhammadu slw) yafada cewa idan mutum biyu na fada,to daya yayi saurin saukar da zuciyarsa gudun abunda zai je ya dawo,idan duk zucoyoyi biyu suka dauki zafi a lokaci guda,to shedan zai samu abunda yakeso,a kansu, Allah kasa mu dace
"Yanzu a matsayin ka na namiji mai hankali a kanta ya kamata ka biye mata duk abunda tayi, wannan ni kawai ka ciwa mutumci wallahi"
"Ok " Ok wato ni ba kaga abunda tayi min ba,yariya karama tana nema ta zageni, abunda babu wanda ya taba yimin shi a rayuwa ta ita tayi min sabuda samun gurin kazo ka nai min wata maganar banza, Ok zan dauki mataki akanta mai tsauri wallahi sai inga yadda za'ayi ka aureta"
"Duk abunda zakace sai dai kace" auran yarinyar nan kamar nayi nagama,kuma duk abunda tayi maka kai ne ka jawo tayi maka, me ye ruwanka da sana'arta da har zaka dunga kiranta da "yar towo-towo wannan ai cin fuska ne, kuma a sanina da kai nasan wannan dabi'ar ba taka bace,kawai ka ara ka yafa ne"
A harzuke! Yace"an kira ta da "yar towo-towo din karya akai mata ne, in tayi wasa ma da " yar tasha za'a kira ta watarana"
Zare ido! Maddibo yayi cikin mamaki yace"wai me yake damunka ne, kai me yarinyar nan tayi maka da zafi haka"?
Tsaki! yayi ya koma ya kwanta cikin kujera yana lumshe ido zuciyarsa sai zafi take
Maddibo yace"dan Allah kafada min meye alakar ka da yarinyar nan Balaraba naga alama kun san juna,ganin yadda kuka shaida juna da wuri"
Minti biyar bece komai ba,farlon yayi tsit! bakajin komai sai karar AC kadan-kadan,
Cikin Ginshera yace"Babu wani abu da ya hadani da ita, hasali ma ban taba ganinta ba,sai ranar saukar su, wacce sukayi ta wattanin baya da suka wuce, wannan shine ganina da ita na farko, tun daga ranar ban kara dora idona a kanta ba sai yau"
Cikin mamaki Maddibo yace"kana nufin kace min itace yarinyar da kake fada min dazu muna mota"
"Kwarai kuwa"
yafada idanunshi a lumshe, ya cigaba da cewa"tun ganina da ita na farko naji na tsaneta sabuda dabi'ointa na lura yarinyar tana da girman kai sosai, kai kanka kasan halina bana shiri mutum mai girman kai da nuna shi wani ne"
Girgiza kai Maddibo yayi yana cigaba da sauraronsa
Ya cigaba da cewa"babban abunda ya burgeni da ita shine, lokacin da aka kirata cikin jama'a a lokacin bukin saukar alkur'anin nasu, ta bude taro da addu'a, lokacin ta bani sha'awa sosai jin tana futar da kira'a sosai, hakan yasa, Maimartaba yayi mata kyauta nima nayi mata tawa"
Shiru yayi yana jan numfashi tsawon minti biyu baice komai ba, yana dan girgiza kansa, yaja tsaki kadan ya bude idonsa sosai wanda suke lumshe yace"inda na kara tabbar da cewar yarinyar nan bata da kirki,lokacin da zata karbi kyautar daga hannuna, in kaga irin kallon da tayi min irin na wulakanci sai ka rike baki,kwata-kwata kanta na wani gefe bataso ta kalli fuskata, ina nan da hotonan in kana bukata zan dauko maka kagani kai ma zakayi mamaki"
Shiru Maddibo yayi kawai yana sauraronsa
Shi kuma ya cigaba da cewa"a lokacin abun ya bani mamaki, ganin lokacin dana futo daga gida itace ta farko gurin mikewa domin ta ganni, kamar yadda jama'a suke yi amma yanzu gata a gabana tana dauke kai, kawai na shareta amma abunda tayi mun ya bani mamaki, sosai, naje na zauna, Shahid ya nuna min irin hotonan da yayi mana ni da ita, a lokacin na kara ganin, wukantacan kallon da ta din ga yi min,shi kuma Shahid cewa yake wai mun dace da ita sabuda yana ganin kamar "yar wani ce a garim nan kuma yarinyar tana da kyau sabuda haka kawai in shi ga,raina ya baci sosai da maganar da yayi min, wannan shine dalilin batawar mu dashi,domin da muka shiga gida, ya dame ni da zancan ta, fada mukayi dashi sosai, shine dalilin da yasa kaga baka ganshi ba kwana biyu, to wannan shine,abunda ya hadani da ita, sabuda haka,naji bana kaunarta kai kasan halina,in naki mutum to nakishi har abada wallahi"
A nutse Maddibo yace"ni dai yanzu hakuri nake baka, maganar nan ta wuce kai kayi laifi,itama tayi laifi, sabuda haka sai ayi hakuri a yafi juna,amma gaskiya banji dadin tofa mata miyau da kayi ba"
"Ok yanzu hakuri kakeso inje in bata kome"?
A'a ni bance ba,kawai ka kiyaye ko da nan gaba zaku hadu,tunda dai kasan babu abunda zai hanani auranta,sai dai idan mutuwa nayi"