← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 80

Sashe 53

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance suka ganshi kamar me bacci, idonsa a rufe, Sarki! Ya zauna gefansa yana tattab'a jikinsa, sanyi k'alau d'aga hannunsa yayi yaga ya koma ya kwanta yaraf!! Shi ba yaro bane yasan mecece mutuwa, Mama Fulani ta zube gurin a sume.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

```MARUBUCIYAR```

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_

_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

*🅿84*

Cikin damuwa da tashin hankali Sarki! Ya futa daga d'akin, Jakadiya Shafa'atu na tsaye a falon tana gyare-gyare taga futowarsa,a gigice, tace"Allah ya taimake ka lafiya"?

Sarki! Yace"Babu lafiya Jakadija, Allah yayi wa me Martaba rasuwa, Mama ta suma a d'aki,innalallahi wa'ina ilahi raji'un"

Futa yayi bai san Inda yake saka k'afar sa, lokacin gari ya soma haske, kai tsaye masalaci ya nufa domin ya shaidawa liman abunda yake faruwa.

Jakadiya Shafa'atu kuwa kasa shiga d'akin tayi, saboda tsoro da sauri ta nufi b'angaran Waziri domin ta kirawo Hajiya Kattime.

Lokacin da liman ya sanar da rasuwar me Martaba mutane da dama sai suka dunga k'aryatawa kafin kace kwabo kowa ya futo daga shashinsa,har Waziri,,, ya nufi shashen Mama Fulani domin ya tabbatar. Babu Wanda ya hanashi shiga,saboda me Martaba bashi da wani d'an uwa shak'ik'i kamarsa,duk da sun san cewar babu jituwa a tsakaninsu kwana biyu.

Tsallake Mama Fulani yayi ya nufi gawar me Martaba,yana dubawa, hamdala yayi a fili yace"Taka ta k'are Mustafah sai mun had'u, acan,
Lillab'e gawar yayi ya futo yana share hawaye kamar gaske,nan ya k'ara tabbatar wa da jama'a cewar me Martaba ya amsa kiran ubangijinsa.

Da k'yar Mama Fulani ta farfad'o ana tai mata fiffita, duk bata cikin hayyacin ta, Hajiya Kattime ta rungume ta a jikinta.
Balaraba a gefenta tana share mata hawaye Mama takasa cewa komai, tunda ta farfad'o bakinta sai motsi yake,babu abunda take fad'a sai Kalmar innalillahi wa'inna ilahi raji'un"

Balaraba hawaye kawai yake sharewa tana addu'a Allah ya yaye musu wannan masifa da ta tun karo su,gani take kamar k'arya ne me Martaba bai mutu ba, sai data an futo dashi cikin suttura za'a kaishi makomarsa sannan ta gasgata,fad'uwa tayi a gurin ta suma,Mama Fulani kuwa rirrik'eta akayi domin itama saura kad'an ta fad'i da k'yar! ta samu tayi masa addu'a wasu hawaye masu zafi suna zubo mata, Waziri ya tasa gawar a gaba yana kuka kamar wani k'aramin yaro. Sarki! Kuwa wani mugun haushinsa yake ji,ganin yadda ya babba ke gaban gawar, ya hana mutane suyi masa addu'a, sai da aka sauke alk'urini me girma sannan aka sallaci gawar me Martaba ya samu jama'a sama da k'asa ko ina,haka aka d'auke shi aka kaishi makwancinsa na gaskiya.

***
B'angaran Hajiya Kulu da yaranta kuwa duniya sabuwa suka bud'e sun cika suna ciye-ciye da kalle-kalle tamkar ba mahaifinsu ne ya rasu ba, babu abunda ya dame su,Naja'atu ce me cewa,lokacin su yayi,za tayi facaka da kud'i, son ranta

Sarki! Kuwa wani irin zazzab'i ne yake damunsa tun bayan dawowarsu daga mak'abarta,daurewa kawai yakeyi ya zauna yana karb'ar gaisuwa gurin "yan uwa da mutan gari,suna kokawa da rashin da akayi, kowa sha'awa yakeyi Almansor ya maye gurbin mahaifinsa,hatta da su Galadima ma burinsu kenan,Governor da yazo gurin gaisuwar a bunda ya fad'a kenan,Waziri yayi tsagal yace" Ba haka al'adar sarautarmu yake ba,nine k'anin me mutuwa nine zan gaje shi,kafin "Yayanmu saboda haka tunda ina raye,ban mutuba ni zan zauna kan kujerar mulki" Governor yace"Wannan ba sarin mulkin k'asa bane, nine shugaba,dole nine zan zab'i sarkin gari na, saboda haka baza mubi tsarinka ba,Dan kar kace ba'ayi maka adalci ba,za muyi k'uri'a bayan sadakar uku wanda ya fi jama'a shine zai zauna kujerar mulki"

Waziri ya baza babbar rigarsa cikin bak'in ciki da b'acin rai yace"Lallai kam kun jawo masifa,domin rashin zaman lafiya zai tabbatar a masarautar nan, tunda iyayenmu da kakanimu suke mulki basu tab'a wata k'uri'a ba sai yanzu, mu baza'a rusa mana tsarinmu ba"
Yana gama fad'in maganganunsa ya mik'e ya futa daga fadar,ranshi a b'ace, yana ganin wannan Governor zai kawo masa matsala fa, yayin da buk'atarsa ta kusa cika

Sunyi mamakin abunda Waziri yayi,zahiri ya nuna mulki yake so,Sam mutuwar d'an uwansa ba itace a gabansa, wannan ya k'ara bawa Sarki! K'warin gwiwa da son sha'awar mulki abunda bai dame shi ba,a da yana so yanzu su fafata da Waziri, Allah yaba mai rabo sa'a.

Sai bayan sallahr isha'i Sarki! Ya shiga gida kai tsaye shashen Mamansa ya nufa,yana tafiya cikin sanyi jiki, ji yake duk duniyar tayi masa zafi, Lallai d'an adamu ba abakin komai yake ba,dubi irin hukuncin ubangiji,wata guda yayi rashin mutane biyu da bazai tab'a mantawa dasu ba a tarin rayuwarsa.

Balaraba da Mama Fulani da tare da Madabo,da Halisa,da Azima da wasu mata biyu, sai jakadiya Shafa'atu wacce take kusa da Mama Fulani tana b'are mata lemon zak'i,domin ta kasa cin komai, wani irin d'aci take ji a bakinta, da k'yar ta dunga shan lemon har tasha guda uku.

Da sallama ya shigo, falon Suka fara rige-rigen gaishe shi,da yi masa gaisuwa,amsawa yayi sama-sama ya shige turakar mahaifinsa.

Ko da ya shiga kwanciya yayi kan gadon me Martaba,ya d'auki rigarsa da ya rasu da ita a jikinsa,ya rungume ta,k'am wasu zafafan hawaye suka fara zubo masa.

Shikkenan Moddibo ya tafi me Martaba ya tafi,sun barshi shi kad'ai hakika duniya abar tsoro ce,hakama abun jikinta

Kuka Sarki! Yake sosai,kukan da bai tab'a yin irinsa ba, hak'ika yanzu yana buk'atar me rarrashinsa domin ji yake zuciyarsa zata iyayin bunduga, shi musulmi ne, dole ya yarda da mutawa da rayuwa yasan mutuwar wannan mutane biyu, babu wani mahaluki da ya isa ya tare ta sai,Allah domin shine ya hallice su, amma ya karb'i abunsa, shima kuma na hakane, yanzu kawai addu'arshi itace Allah ya sanya masa dauriya da jarumunta a zuciyarsa.

Kamar a mafarki yaji muryarta a kansa,tana kiran sunan sa.

Bud'e idonsa yayi dukansu ya sauke a kanta

Wani irin yarrrr taji lokacin da suka had'a ido ganin yadda k'war idonsa ta koma wata kala,tayi jazur kamar Jan gauta.

Wani irin tausayinsa ne ya tsirga mata,itama sai taji hawaye yana k'okarin zubo mata,daurewa tayi kawai,a zuciyarta tace"Maraici babu k'arya a cikinsa,komai girma komai dukiyarka, ka rasa iyaye kayi babban rashi,yanzu zai fara jin irin ciwon da take ji a zuciyarta na rashin iyaye.

Lumshe idonsa yayi yana jin tamkar ya kamo ta ya rungume a jikinsa ko ya samu sassaucin abunda yake ji a zuciyarsa,hak'ik'anin gaskiya yanzu Wanda zai rarrashe shi yake nema.

Cikin taushin Murya tace"Ka tashi inji Mama kaci abunci,tace inyi k'okari in baka kaci kafin ka kwanta"

Yana jinta yayi shiru abunsa, wani sanyi irin na zazzab'i yana k'ara ziyartarsa.
Ta kure jikinsa yake yana neman bargo domin ya lullub'e jikinsa.

Duk tana kallon abunda yake yi, muryar ta na rawa tace"Don Allah ka tashi kaci abunci kaji ko, bana son abunda zai damu Mama,ina tausaya mata da halin da take ciki,kar ka k'ara sanya mata wata damuwar tunda kasan rashin cin abuncin ka zai d'aga mata hankali, ba kai kad'ai kayi rashi ba,har damu,ni ina ganin kamar ni akayiwa mutawar ma"
Ta k'arshe maganar tana goge hawaye da suka zubo mata.

Yana lullub'e cikin bargo yace"A k'oshe nake,ko na tashi babu abunda zan iya ci, kiyi tafiyar ki kawai nagode"

Girgiza kai tayi kamar zatayi kuka ta zauna gefan gadon ba tare da wani tunani ba ta kama bargon tana k'okarin cirewa daga jikinsa, bargon ya rik'e ya had'a da hannunta, yana girgiza kai,alamar ta sakar masa

Girgiza kanta tayi itama kamar yadda yayi mata, komawa yayi ya kwanta kawai ya rufe idonsa,

Kallonsa tayi taga yadda kwarmin idonsa suka zurma ciki sai girman k'war idon,sai kace Wanda yayi wata yana lalura, ba tasan sanda hawaye ya fara zuba daga idonta ba,wannan tausayi ta rasa daga ina yake zuwa, babu komai a zuciyarta face tsagwaron tausayin Sarki!Almansor.

Sheshshek'ar kukanta yaji yasa ya bud'e idonsa da Sauri, yana kallonta,tayi saurin kauda kanta,tana k'okarin mik'ewa daga kusa dashi, ya ruk'ota da Sauri ya rungumeta tsam-tsam yana wata zafaffafiyar ajiyar zuciya!
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

```MARUBUCIYAR```

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_

_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_

_________________________

🕺🏼🕺🏼🕺🏼
*NAMIJIN DUNIYA*
🙆🏿🙆🏿🙆🏿

*Story & writing*

*By*
*Aunty Mamie*

_________________________

_Ina masoya wannan novel d'in, Aunty Mamie na gaida ku, kuma tana muku fatan alkairi, gaba d'ayan Ku, wannan novel d'in mai suna Namijin duniya ya koma na kud'i dan haka duk me buk'atar ci gaba da karanta shi sai ya tuntub'i wannan numbar_
08166526167
_________________________

*🅿85*

K'okarin k'wace kanta take daga jikinsa, ya rik'e ta tsam a k'irjinsa,sai sauke ajiyar zuciya yake,zuwa can taji d'igar wani abu me d'umi a bayanta, hannuta tasa ta shafo,taji ruwa, Wannan ya tabbatar mata da cewar hawaye ne, tunda take dashi bata tab'a ganin kukunsa ba sai yau, itama zuciyarta sai ta karye,babban mutum kamar Sarki! yana kuka lallai tashin hankalin ya kai inda ya kai.

Sunfi minti biyar rungume da juna, sai da taji jikinsa yayi sanyi sannan ta zare jikinta daga nasa,tana kallon fuskarsa, lumshe idonsa yake amma ba bacci yake ba, tana kallon yadda yake cije bakinsa,kamar wanda yaji ciwo me zafi. Jikinta a sanyaye ta futa daga d'akin.

Tana zama Mama Fulani tace"Ina fatan kin bashi abunci yaci ya k'oshi"?

Balaraba bata iya k'arya ba,dan haka kawai sai ta girgiza kai alamar A'a.

Tace"Mama nayi-nayi ya tashi yaci yace a k'oshe yake Wallahi"

Mama Fulani tace"Nasan dama abunda zai ce kenan, sam baya son cin abunci, tun safe a ce mutum babu abunci a cikinka, sai damuwa Allah ya kyauta"

Balaraba dai Shiru tayi tana tunanin abunda ya faru tsakaninta dashi.

Halisa ce ta mik'e da sauri tana kallon Mama Fulani tace"Bari inje in gwada bashi ko zai ci"

Mama tace"Aikuwa da kin kyauta"

Madabo tayi murmushi, tace"Ai dama ko wace mace da irin hikimar ta,da kin sani tun farko ita kika tura ba waccan ba, ita har yaushe ma suka shak'u da shi"

Mama ta gane magana Madabo ta fad'a mata, tabbas Madabo baza ta canza halinta ba, na fad'ar maganganu da habaici.
Chapter 53 · 0% Book details