← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 80

Sashe 31

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Walidi"
da sauri ya daga kai yana kallon inda yaji kiran
Balaraba ce tsaye k'ofar d'akinsu, hannu ta d'aga masa alamun yazo inda take, da sauri ya nufi inda take, " ya akayi Gimbiya"?
yafad'a yana murumshi,

"Nawa ne k'udin?

" Wane k'udin kike tambaya"?

"Na Uwa! mana,sai a biya ta ta sakar masa wuya"
tafad'a tana kallon inda suke tsaye, tana k'ara mamakin rashin mutumcin Uwa!

Wata mahaukaciyar dariya Walidi ya kwashe da ita, yace"kinga Gimbiya kar kishiga wannan cakwakiyar babu ruwanki sunfi kusa, tunda ki kaga yayi shiru to ya aikata ne"

"Ai ba cewa nayi zan shiga ba, a dai biya ta ta sake shi, tun misalin shida na safe suke abu d'aya yanzu har bakwai da rabi, yanzu kuma zaka ga yara sun fara shigowa siyan a wara, wannan ba mutumci ba ne"

Tab'e baki yayi yace"dubu biyar ne"

"Shikkenan zan futa yanzu, zanje banki zan ciro k'udi ka f'ada mata in nadawo zan bata magana ta wuce"

"Shikkenan Gimbiya, tunda kince zakiyi amma ni da dan tani ne da kin rabu dasu, ai gwara da tayi masa haka,gaba bazai kara aikata wa ba"

Lantana idonta a kansu, sai tab'e baki take tana cewa"munafukar banza da wofi kawai, kinibabbiya" kasa-kasa take maganar sabuda batason Walidi yaji

"Ke Uwa! sake shi za'a biya ki"
Walidi ya fad'a yana cije baki!

Hannu daya ta mik'a masa tace"bani in rik'e a hannuna tukkuna"

"Dallah! ki sake shi za'a baki an fad'a miki"
yafad'a kamar zai kai mata duka,
Sakin sa tayi ta matsa gefe tana huci!
tace"ina kud'in suke, kai ma zan iya tsine maka akan k'udin wallahi"

Dariya yake mata yace" Yo ke Uwa! ai ko kin tsine min tsiniwar ki baza ta kamani ba, sabuda kema, baki bi naki iyayen ba, duk abunda kai sai am maka,Hahahahahahaha!
Ya karashe maganar yana wata dariya kamar shashasha.

Ya cigaba da cewa, "Gimbiya zata bayar a baki an jima"

Jin yace Balaraba zata bayar a bata yasa ta kwantar da hankalin ta ta wuce d'aki tana huci!

Sallau kuwa tunda ya samu ta sakeshi sai ya sulale ya futa daga gidan kafin kowa ya ankara,haka ya futa baiyi sallah ba.

Shamsiyya da Mabaruka har a ka gama masifar suna bacci sai da Uwa! ta shiga d'akin tana kwashe sauran kud'in tanayi tana zage-zage sannan ne suka tashi, Shamsiyya tace"wai menene ina bacci ina jin hayaniya a gidan sama-sama, na d'auka ma mafarki nake"

Nan Uwa! ta kwashe komai ta fad'a musu, suka had'u da ita suna zagin Baban na su.

Balaraba kuwa wanka tayi a gurguje ta sanya doguwar riga ta atamfa, me kalar blue da yellow mayafi mai girma ta yafa ta sanya takalmi plate mai a don duwatsu, tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ta kuzo a gani ba, su Sadiya sun shirya tsaf cikin uniporm dinsu na makaranta, ta hada musu shayi mai kauri ta basu sannan ta dafa musu indomee cikin kula, tare suka futo ta kulle d'akin ta nufi d'akin Iya, tana kwance kan katifa, da alamar ta fara samun saukin jikin ta, suka gaisa cikin mutumci Balaraba tace"Iya jiki yayi sauk'i ko"

"Alhamdulilahi jiki yayi sauk'i Balaraba, Allah yayi miki albarka, ta cigaba da cewa, kin futo to Allah ya bada sa'a"

"Ameen Iya nagode, yanzu ba kasuwa zani ba,zanje in ciro kud'i a banki zan sa a fara neman min gidan haya, ko a bayan layi ne,domin bana so in yi nesa dake"

" Yanzu ashe baki bar wannan k'udirin naki ba, Balaraba"
Iya tafad'a cikin jimami

"Iya kiyi min addu'a kawai zaman gidan nan nagaji dashi wallahi,gwara in tafi in bar musu"

"Shikkenan Allah yasa haka shiyafi alkairi"

"Ameen sai nadawo"
Balaraba tafad'a tana k'okarin tafiya, ta jiyo mitar Lantana, ko waiwaya batai ba, ta futa daga gidan.

*****
Kwana yayi yana tunanin ta ina zai fara bunkican Asalin Balaraba, ga Moddibo yau yak'i kwana a shashen sa, ya gudu nasa sabuda tunda ya dawo nan yake kwana, dole gobe kafin ya futa,ya nemi Moddibo a kan al'amarin domin shi kam bai san ta inda zai fara ba, kwana yayi yana mafarkin da yasa bayi kullum, asubar fari ya tashi, yana had'a gumi, mafarkin yau yafi na kullum bashi tsoro, yau ganinshi yayi tare da yarinyar nan mai kama da budurwar Moddibo, yana tara da ita kamar matarsa, abunda bai tab'ayi ba kenan, tunda yake bai tab'a mafarkin wata "ya mace ba, ya san dai shi mutum ne mai yawan sha'awa shine dalilin da yasa ma yake yawaita azimi, domin tsare kanshi, kuma baya tab'a yadda ya keb'ance da mace ko wace iri ce mutukar ba muharramarsa bace, sosai ya ganshi a mafarkin tare da yarinyar suna mu'amula irin ta ma'aurata, jikinshi a mutukar sanyaye ya mik'e ya shiga toilet domin ya tsarkake jikinshi, dole sai yayi wanka, kamar yadda addini ya tanada, bayan ya gama ya d'aura alwala ya futo, jikinshi d'aure da wani k'aton towol mai kauri da tsane ruwa, wani k'arami ne a hannushi yana tsane kanshi dashi, farar jallabiya mai yankakken hannu ya saka ajikinshi had'e da gajeran wando, ya sanya hula irin ta larabawa, a kanshi sai ya zama tamkar wani balaraben kasar Saudia,kalar fatarshi ta futo sosai, ya zura wani farin takalmi ruffafe mai mutuk'ar kyau a kyawawan k'afafunshi, ya nufi massalaci cikin nutsuwa.

*Muje zuwa*

*Comment*
*Vote and Share*
[17/07, 21:39] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®{REAL BINTU BATULA}👄*

_*MARUBUCIYAR*_
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
```{RAHAMA ALIYU}```

_ZAMANI WRITES_
_ASSOCIATION_🤝🏻

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

*🅿52*

Tare suka futo daga massalaci da Maimartaba, cikin nutsuwa suke tafiya tamkar wasu abokai yayin da wasu fadawa suke take musu, baya Waziri da Shamaki ne a bayansu, Shamaki ya kalli Waziri cikin sigar munafuci yace"Allah ya taimake ka, wai yaya kasake har haka tafaru? tuntuni tane fad'a maka wannan shak'uwar dake tsakanin Maimarta ba da yaron nan tayi yawa,kamata yayi ka d'auki mata, a matsayin ka na k'ani gare shi, ka lura da kyau, sam baya baka kulawa kamar yadda yake kula da d'anshi, ko wani abu ne ya faru, in ka lura Maimarta ba baya zartar da wani hukunci sai yasa anyi masa kiransa, kuma duk gaku a zaune a fada, kai da Ciroma da Galadima baku da amfani, nine Shamakin Maimarta ba,nafi kowa sanin shi, tunda kusan kullum tare muke yini a fada, kwanciya bacci ne kawai yake rabamu da shi, ina mai tabbatar maka da cewar in bakai da gaske ba, sai dai kaga wannan Yaro wata rana yana mulkar ka, Allah shi taimakake kayi tunani kan maganar da nafad'a maka"
Shamaki ya k'arasa maganar yana sunkuyar da kai, cikin munafurci

Ajiyar zuciya Waziri yayi yana kallon Maimarta ba tare da Sarki! suna tafiya a nutse hatta da tafiyar su iri daya ce sai dai kasaitar Sarki! har tafi ta mahaifin nashi,

"Akwai abunda nake shiyarwa,domin
Ni kaina wannan abu yana damuna Shamaki, tare nake so mu had'a baki da Ciroma amma yak'i bani goyan baya a kan k'udirina kansu,to amma yanzu na samo mafuta, kwananan buk'ata zata biya kan Yaron shiyasa duk wata giggiwa da yake nake d'aga masa k'afa sabuda nasa ta lokaci kad'ance, zai shafe a duniya kamar ba'ata b'ayin sa ba a doran duniya"
Waziri ya k'arasha maganar yana kallon su ganin yadda hadimai suke zubewa k'asa suna kwasar gaisuwa,wasu tun daga nesa in sun hangosu suke zubewa k'asa kansu a sunkuye, had'e da daga hannu, alamun girmamawa har sai Maimarta ba ya shige suke mike wa tsaye, wannan abu yana mugun b'atawa Waziri rai, shima suna gaishe suna bashi girma a matsayinsa na Waziri,amma baya gani, yafi son suyi masa gaisuwa wacce tafi ta Maimartaba da d'anshi Sarki!

Maganar da suke tattauna tsakanin Maimarta ba da Sarki! yana sanar dashi cewar zai fara bunkice da ya umarce shi, amma yana neman alfarmar ya barshi ya futa da Normal kaya,domin yin basaja, kuma bayaso a had'ashi da kowane bawa, in ba Direba ba, wato mai janshi a mota

Maimarta ba,yace"wannan tunanin naka yayi kyau sosai sabuda idanun jama'a wani ma in ya lura ga daga inda yasa ake bunkicen zai iya fad'in k'arya a kan yarinyar, dan haka duk in da ka tsara kaje kayi, Allah ya kiyaye hanya"

Sarki! yaji Dad'in amuncewar da Maimarta ba yayi, domin a k'aidar masarautar su, basa futa da Tufafi dole sai na sarauta in kagansu da Normal tufafi to a cikin gida suke.

Tare suka shiga b'angaran Mama Fulani domin yau Maimarta ba a gurin ta yake, ta k'ofar baya ya shiga, shi kuma Sarki! ya shiga ta k'ofar da kowa yake shiga,

Tana zaune kan wata katuwar daddamu, ja mai adon fulawa, gefan tumtum ne manya-manya guda uku, gabanta kuwa shak'e da kayan marmari, tana sanye da wata lifaya mai tsananin kyau da tsad'a hannuta rik'e davwani k'aramin carbi mai kyau sai kyalli yake, tayi kyau har tagaji Mama Fulani kenan mace mai karamci da karramawa, mace mai kaunar talakawa da nakassau, Jakadiya Shafa'atu ce zaune a gabanta,da mufuci a hannuta duk da safiya ce amma fiffita take mata, cikin sakin fuska tace"Shafa'atu wai ke bakya gajiya ne"?

" Yaya za'ayi in gaji da hidima da uwar d'akina"
Jakadiya Shafa'atu tafad'a tana sunkyar da kai,
Chapter 31 · 0% Book details