← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 80

Sashe 30

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu abunda yake damun Iya illa zazzab'i na maleria nan me chamis din ya had'a mata magani yace"dole za'ai mata allura ta kwana uku, Balaraba duk ta biya kud'in me chamis din yace"Iya kinci abunci in ce ko"?
"Eh to ba sosai naci ba"
Iya tafad'a da kyar! yace "babu damuwa dama illar guda d'aya ce ayi miki allura bakici abunci ba, tunda kinci ko yaya ne shikkenan, nan ya had'a allura yayi mata, suka kamo hanya suka tawo gida,gurin wani mai balango da gurasa suka tsaya Balaraba ta sai mata gurasa da balangu,suka wuce gida, suna shiga soran gidan suka dinga jin hayaniya tana tashi a gidan, Iya tace" wannan masifa ta gidan nan Allah kayi mana maganinta,
"Humm Iya ki kyalesu suyi su gama insha Allahu na kusa barin gidan sai kowa ya huta tunda nice basa buk'ata, duk kuma wanda ya zalunce ni Allah zai saka min"
Balaraba tafada lokacin da suke shiga gidan, kayanta tafara cin karo dasu a watse a tsakar gida wasu a gurin rijiya wasu a kusa da shara, Cikin mamaki ta tsaya tana binsu da kallo, dawowar Mabaruka kenan daga talla, tana tsaye ita da Shamsiyya tana wassafa mata abunda ya faru, tsalle ta buga tayo kan Balaraba tace"Allah nagode maka,kullum mu ake kira karuwai, yau gashi yau Allah ya nuna mana karuwa a gidanmu,,zatayi zina da d'an gida, Huuuuuuuuu!!! tir dake da halinki shegiya karuwa"
tak'arashe maganar cikin ihu! dama hanya take nema wacce zata ci mutumcin Balaraba sabuda mak'ure ta da tayi a bango kwanaki,
kayanta dake watse tabi tana tumurmusawa da k'afafunta, babu abunda Balaraba tace, takama hannun Iya ta shigar da ita d'akinta,sannan ta futo su Sadiya na biye da bayanta, suka shiga d'aki, zama tayi gefan katifa ta zabga tagumi hannu bibbuyu, tunani take yaya zatayi da rayuwar ta da ta k'annenta, sai yanzu tafara jin rad'adi a kafarta, kallon k'afar tayi taga ta kara tasawa alamun k'ona, ita ba wannan ne abund ya dame ta ba yadda za'ayi su futa daga wannan jarabar itada "yan uwanta, shawarar da ta yanke kawai shine ta nemi gidan haya su bar gidan, shine mafuta duk wanda zai yi zargin ta, ya dad'e bai yi ba,dama kuma a cikin zargin mutane take, kullum, tun tana jiyo motsin da hayaniyar su Lantana ta a tsakar gida, taji shiru da alama kowa ya shiga d'akinshi, buta ta dauka ta futo tsakar gidan domin ta daura alwala, suka ci karo da Sallau ya shigo gidan afujajan, gabanta ne ya fad'i sai tafara karanta innalillahi a zuciyar ta, tsayawa yayi yace" yawwa dama d'azu gajiya nayi na futa sabuda abokai na suna jirana a waje gashi baki dawo ba, sabuda haka yanzu me ake ciki, ki kawo kud'in da nace ki bayar domin za a sai wa Iro magani yanzu"

"Kawu ina takkadun gida da shago na wanda Maimartaba da yaron shi ya bani gurin saukata"?

Gabanshi ne ya fad'i sosai sabuda tun lokacin da ya karb'i takaddun daga hannunta yaje ya sanya su a caca lokaci guda a ka cinye shi cikin inda-inda yace" wannan maganar ki aje ta gefe guda domin bazan baki a hannun ki ba, sunan na adana miki"

"Kawu kaje na bar maka su, kayi hakuri ni a yanzu bani da wani k'udi da zan baka, wallahi"
tafad'a tana k'okarin shiga band'aki sabuda tasan tunda ta ganshi ya shigo afujajan tasan daga gurin caca yake, watakila an cinye shi ne ya tawo yana neman kud'i ruwa a jallo,tasan ko ta bashi k'udin gurin caca zai koma baba wani magani da zai sai wa Iro, tana jinshi yana zaginta ta shigewar ta band'aki, bayan ya gama zage-zagen nasa d'akin Lantana ya nufa sai kace zararre, cikin ikon Allah duk ya taddasu suna bacci, nan ya tsallake su ya shige k'uryar d'akin ya fara laluben inda, Uwa! take ajiyar kud'i Allah ya bashi sa'a ya ga wani k'aton banki, batare da b'ata lokaci ba ya fasa shi ya kud'i ne a ciki kimanin dubu bakwai, ya lissafa dubu biyar ya bar sauran dubu biyu, a watse a gurin ya tsallake yayi ficewar sa daga gidan.

*Muje zuwa*

```Shin Balaraba in ta bar gidan ina zata koma?```

```Idan Uwa! ta wayi gari taga bankin ta a fashe wace irin masifa ce zata biyo baya```?

```Ta yaya Sarki! zai fara bunkican Asalin Balaraba```?

``` Menene a zuciyar Sarki!dangane da Balaraba```?

```Maddibo ne mijin Balaraba ko Sarki!?```

*Duk wannan amsoshin suna gaba, ku cigaba da bina domin ganin wace irin waina za'a toya*

*Comment*
*Vote and Share*
[16/07, 21:17] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^°
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®{REAL BINTU BATULA}👄*

_*MARUBUCIYAR*_
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
```{RAHAMA ALIYU}```

_ZAMANI WRITES_
_ASSOCIATION_🤝🏻

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

*🅿51*

Bayan ta idar da sallahr tayi addu'oin ta kamar yadda ta saba, Usuman ne ya farka daga bacci ya fara kuka, " Yaya yunwa nakeji, abunda yaron ya fad'a, Sadiya ta hau tashi daga bacci,sam ta manta bata basu abunci ba suka kwanta bacci, Sadiya ta mik'e zaune tana mutsike ido, Balaraba tace"tashi kuci abunci,kinga Usuman ya tashi yana kuka,maza jeki dakin Iya ki dauko kular abuncin ku,da sauri Sadiya ta mike, ta nufi d'akin Iya, Iya na kwance kan dadduma bayan ta idar da sallah wani bacci ne me dad'i yake fuzgarta, zazzab'in ya sauka domin har wani gumi take, Sadiya tayi sallama, d'akin Iya ta mik'e zaune tace"Lafiya Sadiya"?

Iya kular abuncin mu zan dauka"
Iya ta koma ta kwanta,tana cewa "in kin futa ki ja min k'ofar, nan Sadiya ta d'auki kular ta futa daga d'aki,

Bud'e kular Balaraba tayi tana duba abuncin, babu abunda yayi duk da yake dafa duka ce, har yanzu da zafinsa, nan ta zuba musu suka fara ci pure watar ta dauko musu guda biyu, Usuman yace" Yayarmu ke bazaki ci abuncin ba"?

"Zanci mana Usuman kai da kuci ku koshi" tafad'a cike da tausayin yaran, bayan sun gama ta rakasu suka wanke hannuwan su, suka dawo ta gyara musu kwanciya suka kwanta, nan ita kuma ta cigaba da had'a "yan kayanta da suka rage tana sakawa cikin a kwatu, domin taci alwashin barin gidan gobe daga yau ta bar kwana a gidan,

Sai wajan karfe d'aya saura na dare sannan ta kwanta, cikin ikon Allah a subar fari ta tashi daga bacci ta futo ta d'aura alwala ta koma d'aki da sauri ganin ana iska sosai hadari ya had'u har an fara yayyafi, tanaji massalacin bayan gidansu sun tayar ta bisu sallah, bayan an idar da sallahr rayi addu'onta, ta cigaba da zama kan dadduma tana jan carbi kamar yadda ta saba, wajan karfe shida, ta fara jin motsin mutanan gidan, sun fara futowa, bacci ne yake fuzgar ta kad'an-kad'an sai taji hayaniyar Uwa! tana buga kyauran d'akinta ta tare wa Sallau hanyar wucewa tana kunzuma masa ashar! "Wallahi tallahi babu wanda zai yi min wannan d'anyan aikin sai kai,domin dama kasha auna fasa min asusu na,ina kama ka,shine jiya ka faki idona, sai da kabari nayi bacci kafasa ka kwashe min kud'i ,wallahi Sallau ko ni ko kai a gidannan domin bazan sha wahalar neman kud'i na ba,ka dinga bin dare kana sacewa, eheee! ba zata sab'uba bunduga a ruwa!
Ta karasa maganar tana tattaro wuyan rigarsa ta cukume shi,

" Shikkenan daga kin ga an fasa miki banki an kwasar miki kud'i sai kice nine sabuda kin raina ni duk b'arayin "yayanki bakya tuhumar kowa sai ni, to komai masifar ki dole ne ki sake ni,inje inyi alwala inyi sallah tunda ke baza kiyi ba, baza ki hanani yi ba"

"Kai dallah! rufe min baki"
tafada tana kai hannuta dai-dai bakinsa kamar zata gwab'e ta cigaba da cewa"kai har kana da bakin da zaka fad'i wata magana a kan sallah, akwai babban makiyin Allah irinka, ai Sallau in kaga na cika ka agurun nan to tabbata ka futo min da kud'ina"
Tafad'a tana k'ara tattaro wuyan rigar sa, k'arfi yasa ya angije ta, tafad'i k'asa ragwajab! ya futo daga d'akin da sauri, ya nufi k'ofar futa daga gidan, da gudu ta biyo bayanshi tana huci! cikin tashin hankali da masifa tace" ni ka tunkud'e ko, har kasa na fad'i a gaban yara na, to yau zanga yanda za'ayi ka futa daga gidan nan mutukar ba kud'ina ka bani ba"

Mutan gidan duk sun futo suna kallon ikon Allah, Uwa! ta shak'e wuyan Sallau sai huci take, dama d'azu shammatar ta yayi ya ingije ta d'azu domin Uwa tana da mugun k'arfi sai kace doki haka take,

K'ifta ido yake kamar b'era a ruwan zafi, bakin sai karkarwa yake,ya rasa abun cewa, duk alamu na rashin gaskiya ya bayyana a tattare da shi.

"Ke dan ubanki sakar min wuyan d'ana kar ki kashe min shi ki cuce ni"
Lanatana tafad'a lokacin da ta karaso inda suke, cikin tashin hankali take k'okarin b'anbare hannun Uwa!daga wuyan Sallau, doke hannun Uwa tayi, cikin rashin kunya tace"kinga Lantana, matsa dan Allah sam baki iya komai ba sai munafurci da kwad'ayi, in kinga na sake shi to sai ya futo min da k'udina ehee!"

Gefe guda Lantana ta matsa tana rik'e hannun ta domin taji zafin buge mata hannu da tayi
tace"shikkenan,to kashe shi ki huta mara kunyar yarinya kawai, a gidan ubanwa naje nayi k'wadayi da har kike kirana da haka"

"Sai kiyi kuma kanki a keji"
Uwa! tafad'a tana k'ara matse Sallau jikin garo

Walidi ne ya shigo gidan, tashin sa kenan daga bacci ya fara jiyo hayaniya sabuda haka a fusace ya shiga gidan, cikin mamaki yake bin iyayen nasa da kallo,

"Ke!dallah, wai menene haka, kuke sai kace wasu yara,k'ananu, ke Uwa! sakar masa wuya" yafad'a cike da bada umarini kamar shine Ubansu,

"Walidi in kaga na saki wannan mutumin to sai ya futo min da kud'ina, da ya fasa min banki jiya da daddare ya kwashe min"

Sallau duk yayi tsuro-tsuro, gwanin tausayi

Wani irin kallo yayi wa mahaifin nasa yace"Kai! ya akai ka fasa mata banki ka kwashe mata k'udi? wallahi baba zuciyarka ta mutu, eh! ka cuce mu daka haife mu, ina tur! da futowa ta tsatstson ka!!

Kasa cewa komai Sallau yayi duk ya muzanta, jikinshi yayi sanyi k'alau sai ya sunkuyar da kai k'asa
Chapter 30 · 0% Book details