Sashe 58
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
************
************
*************
A nutse take kallonsa tace"Bangane kullum kana mafarkina ba, a ina kasan ni ka san uwata da har zaka dunga mafarkin mu"?
Ta karashe maganar cikin mamaki.
"Duk ba wannan na tambaye ki ba,duk wata maganar ki ki aje ta gefe guda ki fara bani amsa ta tunda nine na tambaye ki"
Tab'e baki tayi yana wani murmushi irin na gefan baki nan, girgiza kai tayi ta dago kai tana kallonsa tace"Ni ba wata aba b'ace kamar yadda kake tunani hakanan kuma ni ba "yar kowa bace, Tunda nake da Moddibo bai tab'a turke ni yana tuhumata da dole sai ya San asalina ba,saboda yasan inda yaje ya d'auko ni"
Hararata yayi k'asa-k'asa cikin muskilanci yace"Ni daban Moddibo daban, in zaki fad'a min ki fad'a min banason, bata lokaci"
Ganin fuskarsa babu wasa yasa itama ta gyara tata fuskar ta fara magana kamar haka.
*Sunana Balaraba Ayuba Tanko*
Dago kansa yayi yana kallonta sai ya tuna da lokacin saukar al'kuranin ta.
Basarwa yayi yace"B'angaran uwa fa"?
Ranta ya soma b'aci, dakewa tayi tace"Sunan babata Hafasatu, kakata kuma Kaka Suwaiba gurin haihuwar babana ta mutu"
"Allah sarki, Ubangiji Allah ya jikinta da rahama"
Ya fad'a cikin jimami!
"Uhumm"! Ina sauraron ki"? Yafad'a yana tsatsare ta da ido.
Wasu hawaye ne suke k'okarin biyo kumatun ta, à kufule tace" Wai kai dolene sai kasan Asalina in baka aure na a haka ka fasa ai babu dole. Ni ban san asalin mahaifiya ta ba. Shikkenan Malam" mik'ewa tayi zata bar gurin tazo ta giftashi, kamar kububuwa Dan haushi sai nishi. Take, tana tuno Moddibon ta, duk tsawon lokacin da suka dauka suna soyaya dashi bai tab'a turke ta ba, sai wannan Dan rainin hankalin ai babu dole idan bazai aure ta ba sai ya fasa.
Hannu ya rik'e sosai yana murzawa ta sha kunu! Tana fad'in 'sakar min hannuna"
K'i yayi yanai mata wani irin kallo, me tattare da abubuwa kala-kala a zuciyarsa yace"Ashe dama wannan zafin kan nata yana nan.
Ajiyar zuciya kawai take saukewa idan da tasan tambayar da zai mata kenan babu abunda zai sata ta tsaya ta saurare shi.
Mintuna kusan biyar suna a haka bai sake ta ba. Hannusa a cikin nasa , muryarshi bata futa sosai yace"Naji na janye wancan maganar ta baya, tunda ba kyaso amma wannan dole ne ki amsa min ita, lokacin da kina sai da abunci cikin kasuwar sha tambaya maza nawa kika kula"?
*************
**************
***************
Mabaruka ta futo daga cikin d'akinsu a sukwane jin irin kiran da Lantana take k'uga mata, fad'i take 'wannan tsohuwa da jaraba take wallahi.
Lantana ta shigo gidan tana fad'in "Mabaruka kece me mutanan arzki masu kudi da naira, yau wani Dan sutturar daga cikin mutanen ki ya rufa mana asiri ga kayan arzkiki na......Kafun Lantana ta rufe bakinta Zaratan samari suka dunga shigowa da kayan masa rufi buhu-buhu.
Uwa! Ta futo daga ita sai d'aurin kirji da wata daud'addiyar biriziya duk Tasha d'auri hannuta duk ya saki, kanta inda kasan kan jaka fuskar ta sai maiko takeyi,, wata irin gud'a ta rafka Ayurrrrrrrrrr!!!
*Muje zuwa*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*
```MARUBUCIYAR```
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*
_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________
_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_
*🅿92*
Uwa! sai zabga gud'a takeyi babu ji babu gani, sai da tayi me isarta sannan, ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya tace"Yau "yan bak'in ciki zasu mutu, nima lokacina yayi, haihuwa tayi min rana, Mabaruka farar aniya farar haihuwa,nasan wannan alkairin kece silar shi"
Ta k'arashe maganar tata tana dafa kafad'ar Mabarukan.
Ita kuwa tunani takeyi waye ya kawo mata wannan shatara ta arzkin domin basuyi da wani daga cikin samarin ta ba, wata zuciyar tace mata ko dai Alhaji Saminu ne, mutum da yake so yayi luwad'i da ita.
Nan take ta yardar ma kanta cewa shi d'in ne.
Bak'in ciki kamar ya kashe Shamsiyya domin suma a junansu hassada suke ma junansu.
Shigo da kaya abunci ake nau'i -nau'i tsakar gidan ya cika, sai suka fara d'orawa akai.
Sallau ya rarrafo ya futo duk ya rame ya susuce, ganin uban himilin kayan dake jibge a tsakar gidan yasa ya kusa fad'uwa ya kalli Lantana yana wani irin murmushi yace" Hak'ika Haihuwar Maburuka tayi min rana, yanzu wannan mutsiyaciyar matar zata San ni bak'ashin yar wa bane, ni mutum ne Wanda ya cancan ci a had'a jini dashi"
Aikuwa Uwa! Tayi kansa da masifa sai kuza masa ashar take tana fad'in k'arya yake ya zage ta ko yace ita ba me kashin arziki bace,
Fad'a suke sosai suna fad'a ma junansu bak'aken maganganu, da tada tsohon Abu da ya faru a tare dasu.
Gidan ya cika da matasa da yara "yan unguwa kai harda matan aure wasu sun futo daga gidajansu domin su bawa idanunsu hakkinsu.
Abokin Walidi ne yace" Don Allah kuyi shiru mana arzki yana Neman Ku kuna kokarsa, wannan da kuka gani a zube to ake ne daga gidan me Martaba Almutafah Allah ya gafarta masa.
Shamsiyya najin abunda abokin Walidi ke fad'a sai kawai ta zabga wani ihu!!! da gudu ta shige d'akinsu tana ihu tana tsalle fad'i yake "An yanka ta tashi, dama ni nasan tunda Arrama yace" In saurara komai zai zo da sauk'i nasan lokacina yayi, tabbas aikinka kamar yankan wuka ne a gurina, Mabarukan banza ina taga arzikin da zata kawo wannan kayan"
Gudar dubu d'aya ta futo da ita a hannuta,bakinta kamar gonar auduga ta mik'awa Abokin Walidi tana fad'in "Karb'i tukwuci ai dole ne In biya ka, irin wannan alkairi haka"
Karb'a yayi yasa a aljuhunsa yana godiya ya kalli Lantana yana fad'in wasu Samari biyu sunaso su shigo Ku gaisa don haka sai Ku gyara guri"
Yana gama fada r maganar sa ya juya ya futa sauran abokansa da yaran suka rufa masa baya, d'aya bayan d'aya mutane suka futa suna ta gulmar su.
[9/8, 5:19 PM] Akwai Citta💵💵: Sallau da Uwa! Cigaba da fad'an sukai Lantana tace"Sakarkaru kawai a gaban "yayan Ku kun zauna kuna fad'a ai sai kuje kuyi tayi"
Ta k'arshe maganar tana marmatsar da tarkacen takalman dake bakin k'ofa.
Sam! Baka jin sallamarsu saboda Hayaniyar Sallau da Uwa! Sai da abokin Walidi ya buga musu tsawa sannan suka dawo nutsuwar su,, suka hau washe baki sunawa su Shatima barka da zuwa.
Amsa sukeyi cikin mutum ci da karrama d'an Adam, Lantana ce tayi musu iso har rumfar ta, ta shimfida musu tabarma, bakinta kamar ya tsage dan fara'a sai wani sunkuya musu take tamkar wacce za'ayi musu sujjada, shi kanshi Shahid din ya fuskanci abun take yayi yawa, yace"Baba ya isa,ki nutsu kinji zauna sosai magana me muhimanci muke tafe da ita"
Lantana ta gyara zamanta har da tankwashe kafafu tana fad'in "To Allah ya jisshemu alkairi, ko da yake ai alamar karfi tana ga me k'iba, ina sauraron Ku"
Shahid ya zuba mata ido yana nazarinta daga busani yace"Ina mahaifin Balaraba? Gurin shi muka zo"
Wata irin faduwar gaba ce ta rikitowa Lantana bata shirya ba, baki na rawa tace"Wac...wace Balaraba..kuke tambaya?
Ashe duk abunda yake faruwa a kunnen Sallau da Uwa! Jan jiki yake domin ya k'arasa rumfar domin yajiyewa kansa tabbas,a sukwane Uwa! Ta tsallake shi,har tana take masa cinye, ta bankad'a labule ta afka cikin rumfar babu, Sallama fad'i take"Wace Balaraba kuke tambaya"?
Shatima ransa ya b'aci sosai ganin rashin mutumcin da Uwa! Take tazo ta tsaya musu aka, tunda ta shigo dakin ya d'ume da tsamin hammata,, sauri yake su tashi.
Shahid ya daure zuciyarsa domin ya fara fuskantar akwai babbar Matsala a tartare a gidan.
Yace"Balaraba Ayuba Tanko"
Lantana tace"Ayuba ya mutu shekara da shekaru Balaraba bata da uba kamar wannan Wanda yake zaune"tafada tana nuna Sallau dake rawar jiki.
Shahid ya kalleshi yana fad'in "Kaine Waliyyin ta"
Kamar wani k'aramin yaro Sallau ya d'aga kansa, yana sauraron abunda zai biyo baya
Shahid yace"Ga kaya can daga gurin Mama Fulani tace akawo muku a matsayin Ku na iyayen Balaraba mata ga Sarki! Me jiran gado wato Sarki! Almansur insha Allahu gobe za'a d'aura mata aure dashi"
Ihu!! Shamsiyya ta kurma ta afko cikin dakin tana fad'in "K'arya kukeyi Wallahi baku isa, ni za'a yaudara da muna furci billahillazi bazan lamunta, wannan kayan nawa ne, kuma gobe dani za'a d'aura auran ba da wancan shegiyar ba"
Cikin ihu da tashin hankali Shamsiyya take maganganun sai dara take tana tsalle, Uwa! Ta dunga zabga zagi tana habaice habaice
Sallau da Lantana kuwa Shiru sukayi suna mamakin wannan al'amari
Ganin sun gama abunda ya kawo su yasa suka mike cike da mamakin dabi'ar mutanan gidan tsallake Sallau sukayi Wanda yayi rashe-rashe a bakin Kofa suka futa cikin tashin hankali domin Sam Shatima baya San hayaniya da yawa yanzu kansa zai fara ciwo.
Ganin sun futa yasa Lantana mik'ewa da sauri ta bi bayan su, sai kuma ta dawo da sauri ta koma cikin d'akinta ta d'auko wani Abu tana boyewa cikin hijab, rad'a tayiwa Uwa a kunneta ta futa a sukwane!
Lokacin Buba Direba har ya kunna mota ta karasu gurin tamkar sabuwar mahaukaciya tana fad'in Ku tsaya kutsaya"
Shahid yace da Buba ya tsaya Lantana ta iso gurin tana haki!! Tace"Inaso in biku gidan sarautar domin a gudanar da harkokin buki dani, a matsayina kamar Balaraba.
Shatima yace"Bud'e mata Kofa ta shigo, aikuwa Buba ya bud'e kofar mota Lantana ta shiga ta zauna tana k'ara damk'e abun da yake hannuta.
[9/8, 9:34 PM] Akwai Citta💵💵: **********
**********
**********
Wata irin fad'uwar gaba taji lokacin da taji abunda yake cewa, kar dai wannan mutumin zarginta yake.
Take fad'ar haka cikin zuciyarta.