Sashe 50
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya k'arashe maganar da mahauaciyar dariyarsa, barin gurin yayi yana fad'in ni kam nayi nawa guri domin yau ina cikin farin ciki da annushwa sanadin Balaraba yau na "yantu na zama cikkaken mutum ehe duk d'an bak'in ciki sai dai ya mutu!
fucewarsa yayi ya barsu da baki a sake
Sallau kuwa tuni ya sharb'e a gurin bakinsa ya karkace miyau na dulala, da kyar ya d'aga hannusa guda yana kiran Lantana ta matsa kusa dashi tana salati, baki a mugud'e yace" Lantana muna cikin wani yanayi wannan yarinya da mukai wa rikon sakainar kashi, Allah ya rufa mata asiri tana gidan sarki za'a d'aura mata aure da d'an wazirin gar..... kafin y k'arasa maganarsa Lantana ta fahimci abunda yake nufi, wani uban ashar! ta kurma tamkar ba tsohuwa ba fad'i take, "Me nake shirin ji ni Lantana, Balaraba d'iyar Tanko itace zatayi aure gidan sarauta ni nawa jikokin na nan a zaune lallai da sake! tafad'a wata irin kumfa na futa daga bakinta tsabar tashin hankalin da take ciki sam yanzu rashin lafiyar Sallau din bata gabanba, tunanin ta ya koma gurin ganin yaya zatayi ta futo da Balaraba daga wannan gida ko ta halin k'aka ne.
Shamsiyya ce ta futo daga uwar dakinsu daga ita sai daurin kirji nonuwanta sun cika sun tun batsa sai kace wata matar gida goshinta sai kyalli yake. Lantana ta dube ta sama da kasa tace"Dube ki cikkakiyar mace wacce ta amsa sunanta na mace kina zaune a gida kina tsotsor tsamiyya waccan mutsiyciyar yarinyar ta shallake ki, ai ko ta halin k'aka sai kin zauna gidan sarauta kema"
Lantana ta karashe maganar kmar zautacciya
Shamsiyya tace"Wai hayaniyar me nake ji ne tun dazu ina bacci"
Nan Lantana ta kwashe duk abunda yake faruwa ta fada mata"
Wani irin k'yashi da bakin ciki da hassada ne suka dura a zuciyar Shamsiyya ,rashin abunyi ne yasa ta fashewa da kuka wurjanjan! ta kalli inda mahaifiyarta take zaune kamar mutum mutumi,sai kace wata gunki tace"Uwa! kina raye a duniya haka tafaru damu k'askantacciya ta fimu komai kullum.kina cewa zaki sabautata mata rayuwa, gashinan kina zaune taje ta auri dan gidan sarauta mu muna zaune"
"Wayyo na shiga uku na lalace"!
Sosai Shamsiyya take kurma ihi!
Wata wawar ajiyar zuciya Uwa! ta sauke zuciyarta cike da bakin ciki gami da hassada, a halin da ake ciki yanzu batasan yadda zata fara ba,amma ya zama dole ta bazama k'auyuka gurin malamai da bokaye, domin samawa kanta mafuta lallai maganar hauwa ta tabbata inda suke cewa dan hakin da ka raina shike tsone maka ido, a halin yanzu duk hankalin ya karkarta gurin ganin yaya za'ayi su sabauta Bawa Balaraba rayuwa ko ta mutu ko tai rai ko ta haukace cikin uku za ayi daya
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
。。。。。。。。。。。。。。。
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*
_MARUBUCIAR_
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
_*Zamani writers Association*_
________________________
*We are her to educate motivate and entertain aur Reades*
_________________________
*DIDEGATED*
*to*
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM
``` Tunanin ka kamanin ka d'an uwa ka tsare kanka, Allah yai maka albarka, sai ka gyara makomar ka```
_*Wannan magana taka haka take fasihin mawak'i Musbahu m Ahamad*_
*Allah kasa mu dace*
*🅿79*
Da sauri Uwa!ta mik'e har zanin dake d'aure a jikinta yana k'okarin fad'uwa k'asa, tayi saurin rikeshi ta tsallake Sallau da kwance magashiyan a dandaryar k'asa,sai nishi yake,d'akinta ta afka kamar mahaukaciya,taje ta zura rigarta ta yafo mayafi ta futo, tana kallon Shamsiyya tace"Maza jeki sako riga mu baza ma,domin zama bai gan mu ba"
Da sauri Shamsiyya ta shiga dakin domin sako riga.
Lantana ta kalli Uwa!dake tsaye tana zazzage kud'i a cikin banki irin na gwangwani,tana lissafawa, tace"Uwa!yanzu, waye zai kula da Sallau gashi a kwance, kin san nima futa zanyi,yau na tashi bani da ko kwabo"
Hararta Uwa!tayi tace"Ai yau dole ki hak'ura da zuwa ko ina ki tsaya ki kula da d'anki daga nan har zuwa lokacin da zan dawo, domin kema zaman jiyya ya kama ki"
Lantana ta karyar da kai gwanin tausayi tace"To tunda kince haka shikkenan zan zauna, nasan dai zaki sammin abunci da zansa a baki na"
Uwa!tace"Idan Shamsiyya ta dawo daga talla ta ciri dari biyu tayi cefa ne,ina da sauran garin kwaki,sai ta tuk'a muku teba,daga nan har dare,in kun ga bamu dawo ba to ku rufe Gida kawai domin in na futa yanzu sai inda mai ya tsaya"
Lantana tace"To to shikkenan ai,Allah dai ya bada sa'a, a samo nasara"
Uwa!tace"Ameen, ai in kana da kudinka komai me sauk'i ne, dama Dan me nake neman kud'in duk dan "yayana,saboda haka yau ranar sune"
Tafad'a tana lissafa kudinta sun kai kusan dubu goma sha bakwai.haka ta zufa basu cikin wata karamar jaka, ta rataya ta a kafad'a Shamsiyya ta futo daga daki.
Suna futa tsakar gida suka ci karo da Sadiya matar Kawu Mamman tana tsaye bakin k'ofar ta duk abunda yake faruwa a kunnenta.
Kallonsu tayi tana me tausaya musu,ganin suna nema su jefa kansu cikin halaka,tace"Uwa!kiji tsoron Allah, ki tuna akwai ranar tsayuwa, me Balaraba tayi miki kike nema ki jefa rayuwarta cikin musiba,ki sani da shi sharri d'an aike ne, zuwa yake ya dawo saboda haka Ina mai tunasar dake cewar babu abunda yake d'orewa a duniyar nan sai ikon Allah,duk sharrin ku gami da hassadar Ku a kan Balaraba,dukanin abunda Allah ya hukunta, a kanta na alkairi sai ya faru, babu makawa, sai dai Ku mutu da b'akin cik...... "Ke Sadiya rufe min baki munafuka"
Uwa!ta fad'a a fusace!ta cigaba da cewa" Wato ke dan baki haihu ba,shine kike min bak'in ciki, a dukanin lamarina da "yayana, to bari kiji, yanzu na fara bin malamai akan " yayana, sai ki mutu,baki san bin malamai ma sai me kud'i ba, aikin banza kawai"
Shamsiyya ta rik'e hannun Uwa!tana fad'in "Don Allah k'yaleta munafuka ce zo mu tafi tana b'ata mana lokaci"
Futa sukayi suna zagin Sadiya, gami da kwashe mata albarka.
Ita kuwa Sadiya bayan futarsu girgiza kai tayi kawai ta shige d'akinta tana nema musu shiriyar Allah.
*Wannan kenan*
*********
Sosai Sarki!ya sakarwa Halisa fuska sukaiyi hira ta fahimta, abunda yasa ya saki jiki da ita,shine ya fad'a mata maganar auransa da Balaraba yaga ta Saki jikinta, bata nuna kishi ba, yaji dadin hakan sosai,kuma suna tare Azima ta kirashi a Waya, nan ma bata nuna b'acin ranta ba, ta burgeshi sosai, har wajan magariba suna tare da juna.
Balaraba na cikin d'aki shiru, zuciyarta duk babu dad'i gasu Sadiya masu d'ebe mata kewa suna can falo har yanzu basu shigo ba. Mik'ewa tayi a nutse ta futa daga d'akin.
Can ta hango su, wani keb'antaccan guri suna wasa babu abunda ya dame su
Kwata-kwata bata kalli inda suke zaune ba, ta nufi inda su Sadiya suke, tunda ta futo yake satar kallonta ta kasan idonsa, har Halisa ta fahimta,ranta ya b'aci amma ta danne, kawai bata nuna ba.
Mik'ewa yayi shima ya d'an kalli a gogon hannunsa bakwai shaura, Yace"Lokacin sallah yayi ya kamata, kije kiyi sallah ko" Halisa ta mik'e tsaye tana gyara zaman rigarta, tace"Idan nayi sallah zan dawo mu cigaba da hira, yau naji dadin hiraramu,babu fad'a bare hantara"
A kasalance yace"Baki da abunyi ne,shiyasa kike wannan maganar, hirar haka ta isa, gobe ma bance kizo ba, domin nasan halinki"
Cikin shagwab'a tace"Me yasa"?
"Ba ranar ki bace gobe,zan zauna da Azima kamar yanda na zauna dake yau"
Tab'e baki tayi,amma bata yarda ya gani ba,tayi shiru da bakinta kawai bata sake magana ba.
Tsakaninsa da Balaraba ido ne,ko da tazo ta wuce su bata ce masa komai ba shima haka haka suka shige d'aki ita dasu Sadiya, su kuma suka futa tare.

🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
_*Soyayyar gaskiya*_
🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
_Jin jina gare ki marubuciyar wannan littafin,( Mugirat Musa 66) Nagode da addu'ar ki a gare ni, Ina miki fatan alkairi a rayuwar ki,Ubangiji Allah ya biya miki buk'atanki na alkairi damu kanmu al'umar musulmi baki d'aya._
BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM
*🅿80*
Sai bayan sallahr Magariba Mama ta shigo, sun sha hira da Hajiya Kattime sosai,taji dadin ziyarar da Mama ta kaima ta,domin ta d'ebe mata kewa sosai, ko da Waziri ya futo daga turakarsa ya ganta,shan kunu yayi ya fucewarsa ba tare da ya amsa mata gaisuwarta ba, inda akwai wacce ya tsana a duniya,bai wuce Mama Fulani, da d'anta ba,wato Sarki! Ko da ya futa babu inda ya nufa sai sashen Hajiya Kulu me d'akin kudu wato Uwar gidan me Martaba kenan.
*****
Tana hakimce kan wata kujera me cin mutum d'aya k'afarta d'aya kan d'aya bayi ne zagaye da ita suna fadanci, ita kuma sai zuba mulki take, Waziri yayi sallama ya shiga d'akin.
D'aya bayan d'ayan bayin da suka futa,bayan sun kwashi gaisuwa gurinsa.
Guri ya nema ya zauna yana fuskantar Hajiya Kulu sosai, suka gaisa cikin barkwanci kamar yarda suka saba, yace magana ce, nake tafe da ita"
Hajiya Kulu ta gyara zamanta tana kallonsa,tace"Ai tunda na ganka nasan akwai magana a bakin ka, kasan abokin kuka shi ake fad'awa mutuwa, nima dama ina neman ka"
Girgiza kai yayi, yaja wata ajiyar zuciya me zafi, yace"Mijinki yana samun nasara akaina ta ko wane hali,to wannan karon nayi rantsuwar sai dai ayi mutuwar kasko, ko ni ko shi,wallahi tallahi, mulki sai ya dawo hannu na,domin inaji ina gani, bazai bawa d'anshi mulki ba,ni ina zaune ban hau kurarar naji yaya take ba, ajiyar zuciya ya sauke,ya cigaba da cewa"Ina me tabbatar miki da cewar wannan karon idan ya tsananta to zan kawar dashi, daga duniyar nan,sai dai yaga ana mulki a k'iyama,idan yaje can"
Ya k'arashe maganar bakinsa na kumfa"
Hajiya Kulu,tace"Wannan maganar da kake tafe da ita,nima a kanta nake,a kintse nake,a shirye nake,zan mara maka baya gurin ganin burinmu ya cika,akansa ko d'ansa,domin kwata-kwata bana sha'awar mulki ya koma hannun wancan d'an shegiyar,ina me tabbatar maka da cewa kashinmu ya bushe"