← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 80

Sashe 5

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuma tun tasowarsa mutum ne mai Auri saki ,Matarshi ta Farko Lantana itace Uwarsu Kawu Sallau da Kawu Maman ,Matarshi ta biyu "yayanta duk mata ne su biyar ,haka ta zubesu gaban Lantana ,tayi tafiyarta ,Lokacin da Auran ya Mutu.

Lantana wata irin mace ce mai zuciyar kafurai bata da imani ko miskala zarratin,ita ke daura yaranta a kan mumun dabi'a

Idan Tanko ya fita sana'arsa sai ta daurawa "yayan kishiyarta ,mata talla ,tace duk inda zasuje suje su siyar mata tallah har da daddare daura musu take ,idan suka qi kuwa tasa Sallau ya Zane su.

Tun Tanko bai Sani ba har yazo ya sani ,yayi tai mata fada,budar bakinta sai cewa tayi itafa baza ta zauna da gurda gurda "yan mata gida daya ba batare da ta more su ba idan baya so ta daura musu tallata to yayi musu Aure,

Dake Tanko Jan wuya ne a gidanshi ,ya tsawar mata ,yace "gidansa takyale masa yara suyi karatu ,tukkuna idan Miji ya fito ai za'ai musu Auran.

Lantana taqi ji ,Tanko yana sa kafa yana fita zata fafaki yaran da faratin tallah ,suna kuka suke tafiya,

Karshe Suka yanke shawarar guduwa gurin Uwarsu,

Aiko ranar da Asubah suka fito dukkaninsu suna labewa suna jiran babansu ya fita sallah su gudu

Tanko ya fito kamar yadda ya saba ,ya tsaya shagon su Sallau ,domin tashinsu ,suje massalaci ,daga bakin kofa ya tsaya gami da bubbuga kyauran ,ya wucewarsa

Su sallau ko sunajinsa ,da suka fahimci ya kauce daga gurin sai suka cigaba da baccinsu ,dakin sai tsami ne yake tashi ,sabida ,dama bawata tsaftace dasu ba ,sai su fi sati basiyi wanka ba.

Su Atika kuwa bayan sun tabbatar da wucewar babansu ,sai suka fito sadaf sadaf zasu gudu.

Abin Mamaki ! Sukayi gware da Tanko ya dawo domin daukar chazbah ,

Sai ya kara haske fitilar dake hannunsa yana kallonsu daya bayan daya,ga Atika riqe da katuwar jaka.

Yace"INA zakuje ne"?

Sai suka fashe da kuka dikanninsu ,

Kukan da yayi sanadiyar Farkawar Lantana daga Barci duk da tana cikin Uwar dakinta,

Tafito da sauri jin kukan da soro ,tana Addu'a Allah yasa ba daya daga cikin "yayanta bane ya mutu ,kanta ko Dan kwali babu.

Me za ta gani su Atika ne tsaye riqe da jaka suna zabga kuka ,ga babansu a tsay"

Tace"Malam Lafiya dai in ce ko "? Wa"yan nan shashashan yaran sun tashe ni daga bacci"

Ko sauraronta bai yi ba ,ya cigaba da tambayar su Atika ina zasuje da Asubar nan.

Atika tace "babah mungaji da Azabar da ake gana mana ,zamu tafi gurin babarmu,

Lantana tayi salati kamar gaske tace"Au!sharri zaku kullamin gurin Ubanku "ooo ! Ni Lantana Na hadu da "yayan zamani,
Sai ta hau kwala Sallau kira.
"Sallau" Sallaau!! Sallau"!!

*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

📚📚📚📚
_in kana bukatar cigabansi ga number nan_
08089965176
[04/05, 03:05] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀

*✍🏻writting by*
*Binta Umar*
_*MAMAN ABDUL WAHABU*_

_Bissimillahi _Rahamanir rahim_

*🅿11*

Sallau ya taso a fusace Sallau ,yafito gami da cewa "wai menene kin tashe ni ina bacci"

Sai tafashe da kuka tana nuna su Atika da hannu tace"ga sunan suna kulla min sharri a gurin Ubanku ,har da zagina"

Ai ko sallau ya yi tsalle ya gaurawa Atika Mari yana zaginta ta Uwa ta Uba,kwata kwata bai lura da Malam Tanko dake tsaye a gurin ba.

Tanko yace"yanzu Lantana yaushe yaran nan suka zage ki Dan sharri" to tunda Abin ya zama haka zan dauke yaran nan daga hannunki ,ya mai da idonsa kan Sallau dake tsaye yace"kaji kunya sallau ,da zaka din ga biyewa Uwarka da duk Abinda tace da kai , Allah ya shirye ka,ya mai da idonsa kan su Atika yace su koma ciki ,kafin yadawo daga masallaci.

Yana fita Sallau ya riqa zaginsu shi da Lantana,sukayi masu shiru ,Lantana tace baza su koma ba cikin gidan ba tunda suka fito sun fito kenan ,sai subari Ubansu mai daure musu gindi ya dawo sannan.

Bayan Sun fito daga Massalaci Tanko ya tsaya shida Amininsa yake fada masa halin da a ke ciki.

Budar bakin Malam iliyasu yace"mai zai hana muha da Atika da Yunusa mana ina ganin hakan zaifi.

Malam Tanko yaji dadi hakan ,ai nan suka tsayar da Magana.

Bayan sun karya da kansa ya fita dasu yasa su a mota ban da Atika domin yafada halin da ake ciki.
Tana kuka suka rabu da "yan Uwanta.

****

Lantana kamar ta mutu jin cewar Atika zata Auri yunusa Dan gidan Malam iliyasi ,ita San samunta yaran suyi tazama babu Aure sabida tsabar qiyyaya.

Ranar daurin Aure Abin sai yabawa jama'ar dake gurin Mamaki jin ana daurawa Uba da "ya Aure.

Da Labari ya iski Lantana gurin daurin Auren tafito tamkar mahaukaciya tariqa dure duren Ashar
Da kyar su Sallau suka jata suka mayar da ita gida.
Tace"Yanzu Sallau Abinda Malam zai yimin kenan ,ya muna furce ni ,Ashe Aure zai yi ban sani ba niko mai zan yiwa Malam in wuce bakin cikin da ya kunsa min"
Sai ta fashe da kuka har dasu fyatar majina.

Sallau yace"ki rabu dashi Lantana,mune maganin Matar tasa wallahi ,tunda tasa ki zubar da hawaye Sai mun hanata zaman lafiya"
Maman yace "kwarai kuwa sai mun daukar miki fansa a kanta"

Sai tai ta shi musu Albarka ,tace"ai dama nasan zaku share min hawaye shi kuma Malam din zai shigo ya same ni wallahi"

****

Lantana babu irin cin mutumchin da bata yiwa Malam Tanko ba ,ya share ta ,kawai bai kulata ba ya cigaba da hidimarsa,

Gidan Malam Ilayisu nan a ka kai Atika,sosai Tanko yayi mata kayan daki babu laifi ,nan ma da labari ya iski lantana ,tai ta zuba ruwan bala'i a gidan ,tana cewa Tanko ya kwashe dukiyar "yayanta yayiwa wata banza kayan daki ,ai "yaya maza sune "yaya
A takaice dai ranar Lantana bata barsu sun rintsa ba.

Ashe Abu Na gaba,
Sabida kayan dakin Amaryar Malam Tanko iri daya ne da Na Atika ,da Alama duk shi yayi musu.

Wata makociyarsu tazo tana tsoguntawa Lantana ,Aikuwa "yan jeran nafita ,suka shiga dakin Amaryar ita dasu Sallau ,duka wargitsa shi,gami da debo kwata suka yaba jikin gadon da tsakiyar dakin ,sannan suka dinga kuza ruwa a tsakiyar gadon da dakin,sai da suka jiqa katifar jagab sannan suka futa daga dakin ,gami da barinshi a bude.

Ko da "yan kawo Amarya suka zo Lantana Na kuryar dakinta ta tasa redio tana ji ,tana jin shigowarsu sai ta rage redio n tayi lif tana jiran me zai faru.

Abin Mamaki gami da daure kai dak in suka gani a bude ,suna San ya kafafunsu ciki suka ga Abin mamaki ,Komai a fashe ga katifa jagab dakin yana ta warin kwata,

Matar Liman ,ta ce"innalilahi wa'ina ilayi rajiun"! Ai ba haka muka bar dakin nan ba,kai! Jama'a wai kishi hauka ne?

Lantana Na jiyo Abinda take cewa sai tafito a fusace tana gyara daurin zaninta ,Dan kwali a hannu,
Ta nuna Matar liman da hannu tace"ke Shattu bana son munafurci da kankanba ,ehe! Duk wata kutun gwila da kuka hada naji labari da sanya hannuku gurin bawa Malam ,waccan Mutsiyaciyar yarinyar tsintaciyya wacce ba'a San daga in da take ba ,wato ni za ai wa rufa rufa ,an lullube kura da fatar Akuya ,an dauko Mayya an kawo min gida salon tazo ta leshe ni da "yaya Na,to wallahi baza ta sabu ba ehe!! Tafada tana buga cinya cike da neman tashin hankali!

*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

_IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN_
08089965176
[04/05, 03:05] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀

*✍🏻writting by*
_*BINTA UMAR*_
*Maman Abdul Wahabu*

_Up_
_up_
_up_
*BINTA UMAR FAN'S*

_INA MUGUN YINKU SOSAI DA SOSAI INA JIN DADIN YADDA KUKE KAUNAR NOVELS DINA ,NAGODE DA GOYAN BAYANKU DARI BISA DARI_

_*HAKIKA BANI DA BAKIN DA ZAN YI AMFANI DA SHI GURIN GODE MUKU ,SAI DAI IN CE ALLAH YABARMU TARE ,ALLAH YABAR KAUNA TA DAN ALLAH*_


*"YAN QUNGIYAR ZAMANI WRTERS ASSOCIATION*

_INA YINKU OVER ,MUSSAMAN ,RAEL SHAXXI ,HUSAIN 8K "YAR MUTAN ARKALLAH ,HAFSAT SISI ,HALINKU YANA BURGE NI HALINKU ABIN KOYI NE_

*ALLAH YAQARA DAUKAKA ZAMANI*

*🅿11*

Shattu tace"kinga lantana mu ba tashin hankali ne ya kawo mu ba Alkairi ne ya kawo mu duk dai wannan da yayi nagari kan shi," takarashe magana tana kama hannun Amaryar Malam Tanko
Da nufin shigar dai ita cikin dak in'

Mutanen dake ciki suna ta faman tsane ruwan dake kwance gurin ,suka ce "Aa shattu yanzu in kinshigo da ita nan ina guri ,ki kai ta makota tukkuna mugama gyara gurin.
Duk abinda mutum yayi kansa.

Shatu tace "to bara muje gidan Baba Laraba I Dan kun gama sai kuzo Ku fada,

Da sauri Lantana ta tare hanya tana buga cinyarta tace"Ahayye nanaye Akin bur in ji tusa ,dole Dan ace da Mijin iya baba ni warki CE daidai da qungun kowace shegiya,ihe! Muna fukar Banza kawai!

Shattu tace"wai Lantana Lafiyarki kalau kuwa kishi fa ba hauka bane"A tunani Na zaki dauki Suwaibah a matsayin "yarki tunda kin San kome ya faru da rayuwarta"

"Ke!! Dakata shatu" Lantana tafada ta na turo dauri gaban go shi

Tace"dadin baki zaki yi min Dan bake a kaiwa kishiyar ba.

Baki San yanda zafin Abin yake bane shiyasa kike shishshigi a kan Maganar,
Nafada Na kara fada ni Lantana,in dai ina raye babu macan da ita sa in zauna da ita ,ko wacece kuwa"
Ta karashe maganar tana buga cinya.

Shatu kawai sai taja hannu Suwaiba ,wacce take ta kuka tsora ya cika ta,dama tuntuni take jin labarin matar a bakin mutan gari.

Lantana ta koma ta zauna ,gami da kunne redion ta tasaka kasat din wakokin bar mana coge tana ta zubda habaici a gidan,jira kawai take su tanka ayi wace za'ayi

Su dai sukayi mata shiru suna Aikinsu,

Bayan da suka gama ne daya ta tafi domin Kiran shattu ta shigo da Amarya dakinta.
Chapter 5 · 0% Book details