Sashe 48
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushin k'asaita
ya saki lokacin da suka had'a ido da Sadiya dake zaune kan gado,tana wasa da wasu awarwaron Balaraba da ta cire ta aje kan drowar duk wani kwalliye-kwalliye ta daina sai kace me takaba kullum da hijab a jikinta da carbi,kai hatta da d'an kunne ta cire ta aje,gani take itama rayuwarta tazo k'arshe babu Yusuf Moddibo rayuwarta ba zatayi dad'i ba.
Da gudu Sadiya taje ta rungume shi tana dariya tace"Magajin Sarki!yau kwanana bakwai ban gan ka ba,wai ina ka shiga ne?ina Yusuf kullum yayarmu sai tayi kuka idan na tambayeta sai tace babu komai"
Lokaci guda duk tayi masa wannan tambayoyin.
Hannunta ya kama suka zauna cikin wata kujera ya d'ora Usuman a cinyarsa, yana shafa kan yaron cikin tausayi,yace"Na fuskanci Halimatu kina da surutu da yawa, Ok kina son in sanya ki a makaranta ko"?
Cike da farin ciki ta d'aga kai, murmushi yayi kawai yana girgiza kai,yace"Kar ki damu insha'Allah a satin nan zaku fara zuwa school ke da d'an uwanki"
Tsalle ta buga na murna cike da farin ciki tace "Mun gode Magajin Sarki,Allah yasa kazama Sarkin mu"
Murmushi yake sosai yace"Ameen,in dai na zama Sarki kece Gimbiya ta" tsalle Sadiya take tana murna cike da k'uruciya Usuman sai taya ta yake,
Wata tsawa taji wacce tasa tayi saurin shiga taitayin ta d'akin yayi shiru, Balaraba ce ta futo daga toilet taga shashancin da Sadiya take ranta ya b'aci sosai, ta lura shi kuma sai biye mata yake,tana jinta ko gaida shi batayi ba saboda rashin hankali.
Fad'a sosai takewa yarinyar kamar zata kai mata duka Sadiya har ta soma hawaye, ganin hawayen ne yasa ransa ya b'aci ina dalili ita ba'a hakura mata ba,ita zata takurawa wata.
Cikin wani irin voice me kashe jiki yace" Ya isa Malama"
Kallonsa tayi ta gefen ido tayi saurin kauda kanta, kasa-k'asa tace da Sadiyar taje ta gaida shi,
Simi-simi Sadiya taje ta tsuguna tana gaishe shi,ya amsa sama-sama suk hankalinsa na kan Balaraba dake k'okarin ta da sallah,
Rarrashin Sadiya yake har Balaraba ta idar da sallahr ta d'an waigo kad'an bata yarda sun had'a ido ba tace"Ina wuni"
Shiru yayi kawai yana rikitata da mayun idanunwansa masu sa kasala.
Jin bai amsa ba, ta kara maimaita gaisuwar.
Gyaran murya yayi a nutse yace"Lafiya, nake, yayi shiru na minti biyu kana ya cigaba da cewa"Me Martaba na neman ki yanzu"
Cikin fad'uwar gaba ta mik'e tsaye da sauri har tana k'okarin faduwa ta dalilin dogon hijab din dake jikinta
Bakinta na rawa tace"Allah yasa ba wani laifin nayi ba"
Shiru yayi mata yana binta da kallo ganin jikinta na tawa.
Had'e fuska yayi yace"Ji mana, kinga ki nutsu ba wani abun bane,naga kina ta wani rawar jiki, yawwa bayan nan kuma, Wad'an nan yaran da suke gaban ki ki bar ganin k'annan ki ne, to in kika cucesu sai Allah ya saka musu, na fad'a miki"
Yana gama maganar sa ya mik'e ya futa a nutse, bai tsaya kallonta ba balle ya saurari abunda zata ce,ita kuwa binsa tayi da kallo har ya fuce tana mamakin yanda yake mata magana cikin isa!da gadara, lallai ruwa ya daki babban zakara,
[16/08, 14:28] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*
_*MARUBUCIYAR*_
```Nana Khadija```
```Yaro Da kud'i```
```Gimbiya Balaraba```
_*ZAMANI WRITERS*_
_*ASSOCIATION🤝🏻*_
________________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_
________________________
_*DIDEGATED*_
_*TO*_
```RAHAMA ALIYU```
*🙆🏻♂🙆🏻♂BANI BANE🙆🏻♂🙆🏻♂*
_(Zargina ake_)
~BY: MAMA QUEEN~
*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION*💫
*NOTE*
Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark'akiya,rikitarwa dad'i sauransu.....
_Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_
Whatsap numbar
07061553385
*Karku bari abaku labari*
_*BISIMILHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿75*
Cikin nutsuwa, tabi bayansa, Yana gaba tana baya zuciyarta sai wani d'ar-d'ar take, me Martaba yana bala'in yi mata kwarjini don haka suna had'a idoshi ta sunkuyar da kanta a k'asa,gami da zubewa k'asan k'afafun Mama Fulani tana gaishe shi.
Cikin sakin fuska ya amsa yace"Sannu kinji ya k'okari,ya mukaji da rashin Moddibo kuma"?
Cikin rawar murya tace"Alhamdulilahi"
"Allah ya jik'an Yusuf"
Me Martaba ya fad'a,da amin suka amsa.
Sannan yayi shiru na minti biyu kana ya cigaba da cewa"Wato abunda yasa na kira ki, nan gurin shine, ina neman alfarma guda a gurin ki ina fatan zaki bani wannan alfarmar"
A nutse tace"Ai babu abunda zaku nema a gurina in kasa yi muku shi,Allah ya taimake ka"
Me martaba yaji dad'in lafazinta yace"Alhamdulilahi,Allah yayi miki albarka, ina son zan maye miki guribin Yusuf da Almustafa Sarki!kenan, ma'ana zan d'aura muku aure insha Allah rana ita yau, ina fatan ban shiga hakkin ki ba, ko idan ba kya sonsa ki fad'a kar ki rufe min,tamkar "yar cikina kike,domin bazan yi miki dole ba"
Cikin fad'uwar gaba, tace"Duk rin hukuncin da ka yanke a kaina, bani da ja akai domin ka isa dani,saboda haka na amince da zab'in ka"
Albarka me Martaba ya sa mata sosai sannan ya bata umarnin tafiya.
Balaraba ta mik'e a nutse ta bar gurin kai tsaye d'akin da ta futo ta koma.
Tana shiga ta zube kan daddumar da tayi sallah ta fara wani sabon kuka,tana tausayawa kanta,sam takasa cire Moddibo daga zuciyarta, yaya zatayi ta had'a soyyayarsa da ta kowa sam bata jin soyyayar Almustafa cikin zuciyarta,tana ganin bata da babban masoyi. Kamar Moddibo, kuka take sosai,da sosai.
Ganin kukan da yayar tasu take ne yak'i k'arewa yasa Sadiya ta kama hannun Usuman suka futa suna kuka suma.
Babu kowa a falo sai Sarki!dake kwance kan Sofa, yak'i komawa fada, saboda yana buk'atar hutu, sosai kwana biyu sam baya samun ishashan bacci,Moddibo na yawan fad'o masa a rai, mussaman idan ya tuna lokacin da ya had'a hannusa dana Balaraba yana fad'in, d'an uwana ga amana ta nan,wannan magana da Moddibo yayi masa tana tsaye a cikin ransa,
Hangosu yayi sun futo suna share hawaye ya mik'e da sauri yana ware lumsassun idonsa, Sadiya ta k'araso kusa dashi cikin rawar murya tace"Magajin Sarki! ga yayarmu can tana kuka, kuma tak'i taci abunci tun safe take kuka, mu kam munci abunci mun k'oshi abunmu"
Jin da yayi Sadiya tace"Tana kuka sai yayi tunanin maganar da me Martaba ya fad'a matane ta sanya ta kuka, wato tanaso ta nuna masa cewar bata sonsa,amma takasa fad'a gaban me Martaba, ranshi yaji ya b'aci kad'an, cikin zuciyarsa yace "Babu ruwuna da ko tana so ko bata so,insha Allah sai na cikawa d'an uwana burinshi.
Mik'ewa yayi ya rik'e hannunwan su suka nufi d'akin da take ciki, tabbas bazai lamunci zama da yunwa ba
Tana kwance kan daddumar har yanzu kuka take ya k'ofar d'akin ya shiga,da sallama ciki-ciki, sam batasan da shigowarsa ba, yazo ya tsaya kanta,yana k'are mata kallo, inuwar mutum dogo ta gani akanta, tayi sauri d'ago da fuskarta wacce taji jage-jage da hawaye, had'a ido sukayi, yana mata wani kallon kurulla.
Da sauri ta mike zaune tana goge fuskarta da k'asan hijab dinta,hararasa take k'asa-k'asa ta takure jikinta cikin hijab tana sauke ajiyar zuciya.
Yafi minti biyar a tsaye a kanta yana nazarinta, gyaran Murya yayi ya kira sunanta cikin yanayin muryar shi, sunkuyar da kai tayi bata amsa ba.
Tsugunawa yayi kusa da ita ya d'ora gwiwarsa k'asa yana k'okarin d'ago fuskarta,da tafukan hannayensa,a zabure ta matsa gefe tana watsa masa harara,k'asa-k'asa, fuskarsa ya had'e sosai yace"Kukan me kike yi"?
Shiru tayi masa gabanta na faduwa saboda kusancinsu da shi yayi tsanini Wanda har hucin futar nuffashinsa tanaji ga k'amshin turaransa duk ya baibayeta.
Kaurara murya yayi yace"Wannan shine magana take da ta karshe mutuk'ar zan dunga yi miki magana kina raina min hankali, kinajin abunda nake cewa kinyi shiru ko"?
D'ago kanta tayi tana kallansa,cikin dauriya tace"Me ya dame ka da kukana"?
"Saboda ke amana ta ce"
Cikin mamaki ta kalleshi jin abunda ya fad'a.
"Anyway,nasan abunda yasa kike kuka saboda ance dake ki aure ni ne,shine dalili, ko"?
Yafad'a cikin sigar tambaya.
Shiru tayi tana takure jikinta,so take ya tashi daga kusa da ita duk a takure take.
Wani murmushi yayi yana d'an girgiza kansa cikin damuwa abubuwan da suka da meshi yace" Tabbas kinyi rashin masoyi, mu kuma munyi rashin d'an uwa managarci hak'ika Moddibo ya taka muhimiyar rawa a rayuwar ki, tabbas duk abunda ya tafi ya bari a doran duniyar nan dole in d'ora daga inda ya tsaya, ko da me Martaba be yanke wannan hukuncin ba, ni ina da wannan kudirin na auranki araina saboda wasiyar da d'an uwana ya tafi da ita" Nuffashi ya sauke yayi shiru,gami da tsura mata ido, kana ya cigaba da cewa, mutuk'ar kikaga ba'ayi wannan auran ba,to sai dai in ke kika bujere,wa buk'atar mu,saboda haka, inason ki kwantar da hankalin ki a kaina ni ba,bak'on zafi bane duk irin zaman da kike so muyi ni dake haka zamuyi"
Tsitt!! D'akin yayi bakajin komai sai k'arar AC da sautin nuffashinsu, da k'yar ta d'ago kanta tana kallonsa,bata tab'a tsammanin ya iya kyawawan lafazai irin wannan, wani irin kwarjini yayi mata,wanda yasa tayi saurin kauda da kanta daga kansa, muryarta na rawa tace" Ka matsa daga kusa dani"
Girgiza kai yayi kawai yana sakin murmushi,yace"Sadiya tace"tun safe baki ci abunci ba,hakane"?
D'akin take bi da kallo tana neman su Sadiya,basa nan, gabanta ya fad'i ta zaci suna d'akin a tunaninta ko Sarki!yayi niyyar yi mata wani abu ganinsu zai sa ya fasa.
[17/08, 15:30] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

_*BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM*_
*🅿76*
Ganin yadda take rarraba ido yasa ya mik'e tsaye cikin nutsuwa yace"Ki futo falo kici abunci,ki sake da mutane, sannan ki cigaba da walwalarki,wannan zaman da kike cikin d'aki ke kad'ai duk bashi ne mafuta ba,a gareki, ita rayuwa ta duniyanan bata tabbata, ki sanya tawakkali a cikin zuciyarki, kisa a zuciyar ki cewa inda Moddibo ya tafi kema zaki tafi,domin can d'in shine tabbas,a garemu"
Yana gama maganar sa ya futa daga d'akin,a nutse.