← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 80

Sashe 70

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Yau ne girki Balaraba ya kama,, duk dama wancan kwanakin ya na Cikon na Halisa ne, sai Azima da yayiwa kwana uku, wannan mutuwar da akayi yasa Balaraba taga kamar kwanakin sunyi sauri, ita fa bata lissafin komai yanzu duk bata cikin hayyacin ta domin mutuwar Sallau sai ta dawo mata da ta iyayen ta sabuwa,, jiki a sanyaye take yin komai, k'arfe shida ta kammala girki mai rai da lafiya tayi Wankanta gami da fesa turare ko ina a jikinta, tana sanye da wani material sky blue yayi mata masifar kyau, inda tayi amfani da k'aramin mayafi tayi rolling dashi,, anyi mata kitso ta tattare shi a tsaki ta sanya manya-manya ribom sai ya zama kamar a cuci tayi kyau sosai d'inkin Riga da sket ne,, tayi fuskarta fayau,, ko kwalli babu sai mai leb'e da ta goga,, a nutse ta dunga d'ibar kayan abuncin tana kaiwa part d'insa,, su Amina da Hadiza bayinta sukayi-sukayi ta barsu su d'aukar mata tak'i tace"su barshi itama ladan take so, sai suka hak'ura suka k'yaleta ,, lokacin yana sama ta gama shige da fucen ta, ta koma part d'inta sai bayan tayi Sallahr magariba ne, sannan ta kimtsa, da niyar komawa part din nasa.

Da shirin zuwa masalaci ya sauko hankalin sa bai kai kan daining ba, sai Mai dafa masa abunci fa ya gani a tsaye tsakiyar falo ya sunkuyar dakai kasa, gyaran murya yayi da sauri ya dago yana masa barka da sakkowa, Yace"Kana tsaye gashi ana shirya-shiryen tayar da sallah" Yace"Allah ya taimaka ke Nazo zan jera abunci na ga an jera wani nace Allah yasa ba laifi nayi ba"
Kallon daining teble din yayi yaga wasu had'addan kuloli ba Wanda aka saba zuba masa abunci ba,, girgiza kai yayi kawai, yasan aikin Gimbiya ne, yana k'okarin tafiya yace"Yau an hutar sheka, gobe ma kar kayi gudun asara ka futar muku da Wanda ka girka" Yana gama maganar ya futa,, Shi kuma ya koma kicin, cikin zuciyarsa take cewa amma wannan matar tasa ta tarbiyantu ba kamar sauran ba, Allah ya kyauta.
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

```MARUBUCIYAR```

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_

_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

*🅿107*

Sai bayan sallahr Isha'i ya shigo, zama yayi a falo da carbi a hannunsa yana ja,, a hankali ya dunga jin wani sanyayyen k'amshi na ziyartar hancin sa, d'aga kansa yayi yana kallon inda yake jin motsi, Balaraba ce take saukowa daga matattakala cikin nutsuwa, a sirance ya sauke ajiyar zuciya ya su kunyar da kansa wani Abu na tsunkullin sa,, ta k'arasa daining cikin nutsuwa ta gyara komai ta tako a hankali ta zauna kujerar dake kallon sa, kansa na k'asa bai dago ba, a hankali tace"Barka da dare" d'ago kansa yayi yana kallon ta, minti biyu yace"Barka kin wuni lafiya"? "Lafiya Lou ta fada'a tana wasa da hannunta,, yace" Ya k'arin hakuri kuma" ? "Alhamdullahi" Shiri falon yayi sak'e-sak'e take a zuciyarta, shi kuma yana k'okarin ya cika carbin sa,, sai da ya kammala sannan ya aje ya d'auki wayar sa, numbar Halisa ya kira tans d'auka yace"Ki futo muci abunci " kashewa yayi ba tare da ya saurari abunda zata CE,ba, numbar Azima yake nema, sai gata ta shigo cikin uban kwalliya ta k'ananun kaya wanda suka d'ame ta,, b'ata fuska yayi lokacin da yayi arba da ita, kusa dashi ta zauna tana gaishe shi cikin wani irin salo,, a dakile ya amsa, yace"Wannan wane irin iskanci ne zaki futo da wannan kayan na jikin ki"? Azima ta sunkuyar da kai tana fad'in 'Yallab'ai me ye laifin su" A fusace! Yace"Ba duguwar magana na nema ba,, magana ta farko ta k'arshe kar ki sake futowa da irin wannan kayan in zaki saka kayan ki ki saka Ke ka dai a daki ba sai kin nunawa jama'a ba, gida cike da mutane ki futo min da wannan shashancin" Ganin ransa ya b'aci yasa ta fara bashi hakuri , ko sauraron ta baiyi ba ya mike ya nufi gurin cin abunci ransa in yayi dubu ya baci"! Balaraba kuwa taji dadin abunda yayi wa Azima ta lura tayi shigar ne Dan Taja hankalin sa, a randa ba girkin ta ba, dariya kawai take mata Cikin zuciyarta tace"Wallahi wani lokacin mutumin nan na burge ni da halinsa baudadden mutum ne!

Gyaran murya yayi Balaraba ta mike da sauri kar ta samu rabon ta,, Azima ma ta mike jiki a sanyaye,zama tayi, daya daga cikin kujera ita kuma ta fara zubawa kowa nashi cikin nutsuwa, Halisa tayi sallama ta shigo,,, itama ansha kwalliya kamar masu zuwa gasar fidda kyau!! Gwara ita material ne, a jikinta dinkin riga da sket kusan irin na Balaraba kala ce kawai ta banbanta,, gaishe shi tayi ya amsa ba tare da ya kalle ta ba,, sama-sama suka gaisa da junansu ko wacce na danne Kishi a zuciyarta. Balaraba ta zubawa kowa nashi ta zauna ta fara cin nata cikin nutsuwa.
Chapter 70 · 0% Book details