Sashe 11
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan rasuwar iyayensu da kwana arba'in ,Balaraba ta hada "yan kudin da suka samu ita da "yan uwanta, ta shiga kasuwa ,ta siyo kuloli da farantai ,hade da manyan tukwane, tazo ta dira abincin siyarwa, a lokacin shekarun ta basu wuce sha shida ba, dake yarinya ce mai girman jiki ,shiyasa in ka kalle ta zakayi tunanin ta zarta haka, Balaraba tana da kyau sosai ,tana da diri na jiki, fara ce tas! Dan idan tayi kwalliya ta fita baza ka taba cewa a wannan gidan take rayuwa ba,tana da kirki sosai abin ta bai rufe mata ido ba domin ko abinci tayi kafin ta fita dashi duk wanda ya kwana ya tashi a gidan takan zuba masa ,sannan yaran da suke fitar mata dashi su dauka a kura, su kai mata bakin kasuwar,(sha tambaya) anan take siyar da abincin ta,wanda da an fita dashi yake karewa,wani ma sabida kawai yazo ya gan ta yasa yake zuwa cin abincin ,rumfa ce da ita, sosai komai a tsare ,a kwai yaran da suke yi mata wanke wanke da goge goge,tana zaune aikin ta kawai in mutum yazo siya ,ta hada mishi duk abinda yakeso,domin babu abinda babu,wani abin ma idan ba tayi a gida,ba to a kwai mata masu girka mata anan su hada komai tsaf! In kasuwa ta tashi ta basu hakkinsu,
duk wannan ,bai hanata karatu ba, yanzu haka ta kammala scondry scoohl , gashi tayi saukar Alkur'ani mai'girma,
Iro yana mutukar son Balaraba, yayin da ita kuma tayi masa wata muguwar tsana,sabida halinshi,yanan bai sauya ba,
Shamsiyya da Mabaruka dama sai sufi kwana da kwanaki basa magana da ita sai dai in zasu ari wani abin a hannunta kamar kayan kwalliya ko mayafi ko takalmi,wataran har kayan sawa suke ara,in zasuyi zance
Ita ko Balaraba in ta basu bata kar6a in sun dawo mata dashi sai tace su riqe ta bar musu.
Amma hakan baya hanasu zaginta gami da ai batata in zata fita,sana'ar ta si ta zinden ta ,suna yi mata dariya,wai zata tafi yawon iskanci ,cikin kasuwa, Balaraba bata sauraronsu sabida bata daukesu masu hankali ba daga su har uwarsu.
Sallau ko tsoran ta yake ji ,kwata kwata bayason laifin ta, sabida bata masa koro in yazo maula gurinta, haka zata dauki dubu biyu ko uku ta bashi
Shiyasa kullum cikin tsinewa su Shamsiyya yake.
*wannan kenan*
Kadan daga cikin halayen Balaraba
Macace mai mutukar son girma bata son rai ni ko kadan,kuma bata son harkar qaranta,ko sitturunta babu kanana,duk manya ne ,shiyasa mutane da dama suke mata kallo mace mai girman kai da izza! sabida bata dariya ,sai ta kama kan kaga dariyar ta zaka dade,a kwai samari wadanda suka amsa sunansu a cikin unguwar amma tsoran tun karar ta suke da wani zan ce sabida kwarjin da take dashi
Ko cikin kasuwar da take sana'ar ta akwai manya manya mutane da suke son ta amma sun kasa furtawa, sabida kwarjini ,sai kace mai bakin Aljani a jiki.
Sai dai a gani da ido amma babu fuska,
*Wannan shine jigon labarin*
_in sha Allah zan cigabah bayan Allah in Allah yasa muna Raye_
*Yanzu a ka fara labarin gimbiya Balaraba*
~*Sadaukarwa*~
~*Maraici*~
~*Soyayya*~
~*Bakin kishi*~
~*Mulki*~
~*Izza*~
~*Takama*~
~*Sadaukarwa*~
_DUK A CIKIN WANNAN LITTAFIN ,WATO GIMBIYA BALARABA_.
*BINTA UMAR ABBALE*
_MARUBUCIYAR_
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
08089965176..
[13/06, 14:43] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*GIMBIYA BALARABA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*25*
Cikin bacin rai Balaraba ta fita daga gidan Uwa naji Mabaruka tana zaginta sabida nai man fitina amma sabida ta daure musu gindi suyi abinda suka ga dama shiyasa batace komai ba ita take kara ingiza "yar tata cewar tayi duk abinda ta gadama babu mai takura mata gidan ubanta ne
Kicibus sukayi da Sallau ya dawo daga majalisarsu, sai ya tareta yana washe baki tamkar zai fadi yace"dama sai sauri nakeyi ina addu'ar Allah yasa baki fita ba"
A nutse ta ke kallonshi bakinshi duk yayi gaja gaja da dattin goro jikinshi in banda warin taba da ganye babu abinda yakeyi, zuciyarta sai tashi take.
Da kyar ta gai dashi ta bude jakarta sabida tasan abinda yakewa ta ciro gudar dari biyar ta mika masa
Jiki na rawa ya sanya hannu ya karba yace"Allah yayi miki albarka Balaraba, ai ni kin fimin wadan can shegun "yan iska kawai Wanda ba 'acin ko kwabonsu uwarsu kawai suka sani ni mai zanyi dasu shegu "yayan asara"
Mamaki da tsananin takaici ne ya kama Balaraba, jin irin zagin da yake ma "yayanshi, wai sai yaushe Kawu Sallau zai yi hankali ne.?
Cikin bacin rai tace"gaskiya Kawu abinda kake ba dai-dai bane dan Allah ka daina zagin "yayanka kanai musu mugun baki, sam abinda kakeyi bai dace ba"
"Rabu dasu shegu tsinannu jiya ina ganin Shamsiyya ta shi go da dubu uku ta bawa uwarta babu yanda banyi da ita ba tabani ko Dari biyu ce amma sabida batada mutumci taki, ni mai zanyi dasu"
Takaici bai bar Balaraba tace komai ba kawai ta wuce tabarshi tsaye a gurin yana zage-zage da alama kwakwalrwarshi ta soma samun matsala
Tun kafin ta karasa bakin titi mai Napep din dake kaita ya karaso dama tayi mamaki rashin zuwansa da wuri abinda ba ya yi sabida yasan lokacin fitarta,shiyasa itama tayi mishi uziri kila wani abin ne ya tsare shi
Cikin mutumci suka gaisa dashi,ta Shiva ta zauna cikin nutsuwa
Shi kuma ya dauki hanyar zuwa kasuwar sha tambaya
Danja ce ta tsayar dasu dai-dai babban titin da zai sadaka da kasuwar, Balaraba ta kalli agogon dake daure a hannuta karfe goma shaura lallai yau ta makara da yawa, ranta ya baci ganin yadda masu mashina da motoci gami da motocin haya kowa yayi cirko cirko a cikin mota, kawai sai ta ziro kanta waje domin ganin abinda yake faruwa a gurin gashi danja ta sakesu amma kowa ya tsaya da abin hawarshi
Motoci ta gani manya manya irin na gidan sarauta sun tawo a jere daga daga dayan titin wanda zai sadaka da gidan sarki Almustapah, wani mai sai da pure water taji yana cewa na kusa dashi "Sarki Almansor ne zai wuce shiyasa humm masu abu da abunsu"
Motarshi na karasowa ya sauke glass din motar gami da ziro kanshi waje ya daga sannunshi, kan kace kabo gurin ya kaure da hayaniya wasu sai kokarin fitowa suke daga abun hawansu duk dan suyi tozali dashi, abin mamaki har da mata "yan mata da masu aure duk sun fito suna daga masa hannu
Balaraba na hakimce cikin Napep din ranta in yayi dubu ya baci domin mai Napep din nata ma yayi ficewarsa, can ta hangoshi cikin jama'a sai kurdawa yakeyi wai lallai sai yaganshi
Sai da motar da yake ciki ta shige sannan a kafara samun saukin cinko San da a kasamu a titin
Mai Napep din ya dawo sai washe baki yakeyi ya ce "ranki shidade kowa na rubibin zuwa ya ga Sarki Almansor ke kina zaune cikin mota, yau dai nayi tozali da Sarki sarkin kyauta da karamci, Allah yaja zamanin masarautar Sarki Almusta......
"Kaga Ashiru"
Balaraba ta katseshi a fusace
Ta cigaba da cewa "idan ban ba danci zakayi to kaje kasameshi inda yake, dan tsabar wulakanci da rainin hankali a kan zai wuce kawai sai a dakatar da mutane, sabida ba'a damu da damuwar kowa ba, wato in mutum wani uziri mai karfi ya fito dashi shikkenan shi abin ya shafa sabida rashin imani, dubi time dan Allah munfi karfin rabin awa a tsaye a titi, sabida an rainawa mutane hankali, Mtsss dan Allah ni kai ni inda na nufa, Allah ka tsaremu da irin wannan mulki"
Ta karashe maganar a zafafe!
Cikin mamaki Ashiru mai Napep yaja Napep din yana satar kallonta ta cikin mirrow din din Napep din nashi, mamakin karfin halinta yakeyi da yadda take magana cikin gadara gami da takama ita ba "yar kowan kowa ba sai mugun bacin rai,a zuciyarsa yace" wallahi kika sake kika fadi wata magana akan masaurar garin nan sai kin kare rayuwarki a kurku ko kuma mutan gari suyi kuli kulin kubara dake in basu kashe ki ba ma, yana so ya fada mata haka a fili amma sabida yadda take masa mugun kwarjini yasa ya yi gum da bakinshi sai satar kallonta yakeyi
Ganin yadda tayi wani kicin-kicin da fuska.
_Binta Umar Abbale_
08089965176
[17/06, 02:59] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
[16/06/2019 9:50 PM] Binta Umar Abbale: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA BALARABA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA
```YARO DA KUDI```
````GIMBIYA BALARABA```
08089965176
```BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
*🅿26*
_____ Sha daya saura minti biyar Balaraba ta shiga kasuwar lokacin costomas dinta sun cika gurin, da ka dubesu zaka san sun ci sun ta da kai, sabida kudi, Balaraba ta shiga gurin cikin tafiyarta da qasaita kamar wata basarakiya, fuskarta babu walwala ta din ga bin gurin da kalo sabida kwata-kwata bata san kazanta ko kadan, wasu "yan mata ne guda uku suna kai wa da kawowa kokarinsu su sallami duk Wanda yake gurin cikin nutsuwa suke komai.
[16/06/2019 10:25 PM] Binta Umar Abbale: Ta nemi wata kujera ta zauna tana duba wayarta, bata so ta shiga inda mutanan suke sabida ta lura da motar Alhji Yusuf a gurin mutumin ya takura mata, babu irin korar karan da batayi mishi ba a gurin amma sabuda tsabar bakin naci yaki hakura da dai na zuwa cin abinci
Tana zaune tana kallon mutane na kaiwa da kawowa cikin kasuwar kowa yafito nema,a fili tace"Allah ka bamu sa'a
Wani al'amajiri ta hango kusa da wata me kosai sai ta kirashi da hannunta,
Da sauri yaron ya taso har yana hadawa da gudu,
Gudar dari biyar ta ciro cikin pose din ta ta mika masa, gami da cewa"je ka bawa mai kosai kace ta yi muku sadaka in jini"
Hannunshi yana karkarwa ya karba, yana godiya sosai, ya wuce da Sauri
Iyani, mai kosai soya kosai kawai takeyi tana addu'ar Allah yasa kar tayi mata bandaro gashi sha daya na safe har ta wuce ji take tamkar ta dora hannu a ka taita kurma ihu sanin da tayi in kosai nan yayi kwantai bata da yadda zatayi a gida sabida tabar marayun"yayanta,
Almajirin yace"Iyani gashi in Gimbiya wai ki mana sadaka da kosan ki"