← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 80

Sashe 2

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*GIMBIYA BALARABA*

📚📚📚📚

*✍🏻,,,,,,,,*
[04/05, 02:50] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀
*🐾GIMBIYABALARABA*🐾
🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀

*✍🏻WRITTEN BY*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

~*MRS AHAMAD GWADABE*~😍

_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176

*🅿3*

Shiru gurin ya dauka jikin duk Wanda yake gurin ya Mace sakamakon karatun Al'kur'ani mai girma da yake ratsa gurin.

Sai da ta karanta Ayoyi goma na farkon Suratul bakara ,kana tarufe da Addua'a cikin Nutsuwa a je lasifiqar Hannuta ,a ma'ajiyarta tafara kokarin barin gurin

Ida nun mutane sukai caaaa! A kanta Sai tafiyarta tafara hardewa tamkar zata fadi.

Cikin isa Ya dago kanshi dalilin Da yasa Abokinshi Shahid ya takura masa da Magana kasa kasa wai lallai sai ya kalli ita wannan mai karatun

Yana ya mutse Fuska gami da Limshe ido yabi bayanta da kallo domin baiyi nasarar ganin Fuskarta ba ,Wata irin ingarmar Mace ya hango game tsawo ga qiba dai dai Misali ga wani Uban Sharp Wanda sai da yafito ta cikin hijab din a nagani ,Sakamakon yadda Allah ya wadata ta dasu ,kafarta ya kalla cikin bakin takalmi Fara Tass tass da'ita ,Da'a lama jikin ma haka take

Ajiyar zuciya ya sauke yayi saurin dauke idonsa daga kanta,jin zuciyarsa tana darsa masa wani Abu,A rayuwarshi yana son farar Mace kasan cewarshi Mai dun fata .Sai tarin kyau Wanda Allah yayi masa

Shiyasa yake son Farar Mace inji hausawa Alkyabbar Mata,

Shahid ya zungure shi kadan yace"yaya ka ganta Yarinyar tayi fa wallahi irin kallar ka gata zata dace da Sarauta dubi zubin tsarin jikinta dagani A kwai qasaita"

Gyaran Murya yayi kadan "yace "yar wane sarki ce ? Waye Babanta a garin nan ? Da kake hada ni da'ita haka kawai daganin Sarkin Fawa sai Miya tayi zaqi!
Yafada Cikin izgili gami da qasaita Wanda hakan yazame masa jiki,

Shiru Shahid yayi sabida yasan halin Abokinshi Dan daukar zafi ne yace"yanzu dai mubar maganar sai muntashi daga nan"

Ta6e baki Sarki! Yayi dake haka yanwancin suke kiransa dashi Sabida isa da takamar da yake da'ita wacce shi kanshi sarki Almustapa baya yi a Matsayinshi na sarkin ,shi da kanshi yake kiran Almansor din da Sarki zamu'iya cewa shine ma yasa masa sunan Sabida yadda yakeyi din tun yana yaro. To shine fa Abokanshi suke kiranshi da sunanan ,cikin gida kuwa da yarima suke kiranshi.

Mai gabatarwa yakara fitowa a karo na biyu ,bayan Maryam taje ta zauna Cikin nutsuwa yace'Alhmdullhi mun saurari karatu daga bakin Dalibar mu Maryam Ayuba tanko dalibar datayi fice tayi zarra cikin Makaranta sabida hazaqarta da tsaftarta biyyarta Nutsuwarta Tabbas Muna Alfahari da ita Kuma munai mata fatan Alkairi gami da samun miji nagari.

Yanzu batare da bata Lokaci ba Mai martaba sarki Mai adalci Uban talakawa Mai tausayin Al'umma ,zai fito ya rarrabawa ko wanne Alonshi gami da sauran kyautittikan da muka tanada ga dalibanmu da Suka Sauke Al'kurani mai girma kimanin Mutum Dari Uku da sha bakwai Muna fatan wata shekarar dalibai na kasa zasu bada himma da jajijrcewa Musamu ninkin waddanda muka yaye Allah yakarawa Mai Martaba Lafiya da Imani,yafada gami da aje lasifiqar ya bar gurin a nutse .

Gurin yayi tsitt! Mai Martaba yayi gyaran Murya Cikin Abin Maganar ,Wanda yana zaune gurin zamanshi wani bafade yake riqe dashi,

Ya dauki Allon Farko

Sunan *BALARABA AYUBA TANKO* yagani jiki yace'Alhmdullhi.

*Balaraba Ayuba tanko*

Wannan karon ba tayi nawar fitowa ba ta mike tafara ratsa jama'a a karo na biyu Cikin qasaitarta da yanayin tafiyarta ta durfafin inda Mai martaba yake zaune

Idon Mutane yayi caaaa! A kanta kamar dazu ,tsaki taja a ranta tace wallahi na tsani kallo ko kadan"

Ta kasan idonshi yake kare mata kallo har tazo ta durqusa kusa da Mai martaba gami da gaidashi Cikin Nutsuwa,

Yayi saurin dauke idonshi daga kanta ganin ta dago kai ba yaso taga yana kallonta duk da cewar ta kasan idonshi ne idan ba mai kurrala ba ma babu Wanda zai fahimci ita yake kallo ciki ko harda ita balaraba n.

*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
📚📚📚📚
*✍🏻,,,,,,,,,*
[04/05, 02:51] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀

*✍🏻Writting by*
~*Binta Umar*~

~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

~*MRS AHAMAD GWADABE*~

_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176

*🅿4*

Mai martaba ya Maka mata Alo gami da kyautitikan ta na musamman ,Masu photo da video sai aikinsu suke a gurin.

Sannan ta mike hannuta riqe da Allon Fuskarta cike da Walwala,Mai martaba ya kara lasifiqa a bakinshi yace" Ma haifin wannan Yarinya mai Albarka yafito a kwai kyauta ta musamman da na tanadar domin ku iyayen yara"

Raurau rau idanunin Balaraba yayi jin Furucin Maimartaba sai ta fara kokarin mayar da kwallar da tataro a kwarmin idonta domin bata son zubowarta anan.

Tana tsaye masu hotona da Video sai daukarta a keyi.

Mai gabatarwa ya Mike yaje yatari lasiqa yace"Allah yaja da ran sarki mai Adalci wannan yarinyar marainiyace Ubanta ya rasu shekuru goma da suka wuce ita kanta batayi wayo ba Mahaifiyarta ma haka yanzu shekarunta uku da rasuwa sai ita da qqnnenta Guda biyu"

Mai martaba yayi gyaran Murya cike da tausayin Balaraba"yace Allah ya jikansu da Rahama to yanzu muna bukatar waliyyinta yafito domin ya karbar mata Abinda muka tanadar mata"

Diri Diri Maigabatarwa yayi yana waige wai ko zaiga Sallau ,Amma ko Alamarsa bai gani ba cikin mutuwar jiki yakara tarar Lasifiqa yace Allah shi taimaki sarki sarakuna ae wakilin nata bai samu damar halartar taron ba"

Girgiza kai Maimarta yayi yana Nazarin wani Abu kana yagara Murya A nutse yace"ina bukatar *Sarki!! Yarima Almansor yafito na wakiltashi ga wannan yarinyar mai tarin Albarka*

Yana zaune a hakimce yaji wannan Furucin na Maimartaba sai yaji faduwar gaba kadan Amma kwata kwata Fuskarshi bata nuna ba ,shifa ba kowane kare da doki yake so Maimartaba ya riqa Alaqantashi dashi ba yanzu fisabillahi inashi ina jera kafada da kafada da wancan "yar gidan fukara'u wacce ba'asan Matsayin taba.

A nutse ya mike cike da qasai ta gami da izza kamar yadda ya zame masa jiki ya karasa kusa da da maimartaba gami da mika gaisuwa domin yana mutukar girmama Mahaifin nashi sosai da sosai baya son bacin ranshi ko kadan shine yasa ma duk Abinda maimarta ba yace baya musawa ko dako Abin baiyi masa ba,

Cikin nutsuwa Mai Martaba ya mike tsaye wani bafade biye dashi a bayanshi riqe da tarin mukulai da wasu takkadu cikin Ambulan,

Maimartaba ya karbi Mukuuli guda biyu ya mika Sarki!! daya na gida ne da yake ginasu can bayan gari sabida irin haka daya kuma na wani katafaran shago ne cikin wata kasuwa datayi shura cikin jahar tasu nan ma ya mika mata a karo na biyu ko wanne da takkadunshi na mallaka hade da sa hannun shi maimartaba.

A nutse Sarki! Ya karba gami da karasawa in da take tsaye gabanta na dukan Uku Uku,

Da sauri wani bafade ya karaso gurin ya kara lasifiqa bakin Sarki! Domin yasan zaiyi magana dole.

Gyaran Murya yayi yana duba takkadar farko,

Ya Mika mata Cikin Wani irin Voice yace Maimartaba Sarki Almustapah ya Mallakawa Balaraba Ayuba tanko daya daga cikin gidajensa na bayan gari halak malak sakamakon kokarinta da tayi gurin saukar Alku'ani maigirma Allah yaja da ran sarki Yakara maka Lafiya Balaraba na godiya,yafada yana Dan ya mutse fuskarsa kadan gami da mika Mata takkadun ,Akwain guri ya dauki kabbara gami da kirari ga sarki Almustaph Masu photo da vidio suka fara Aikinsu ,duk wani Masoyin Balaraba a gurin ya tayata murna makiyanta kuwa tamkar su mutu.
Sallau wanda ke can rabe jikin katanga ji yake kamar yaje ya cinnawa kanshi wuta ya huta da wannan bakin ciki

Ta sanya hannu biyu ta karba fuskarta cike da walwala Amma taki yadda ko kadan ta kalli Fuskarsa haka masu photo suka riqa daukarsu.

Kamar yadda ya mika mata takkadar farko haka ya mika mata tabiyu hade da Dan mukkulin shagon da yin bayani domin kowa ya shaida

Zubewa Sallau yayi gumi ya tsinke masa yana mamakin yanzu Balaraba ce ta mallaki shago cikin kasuwar sha tambaya Wanda shiga wannan kasuwar sai wane da wane domin kasuwa ce ta masu kudi ,nuffashin sa ya riqa fita sama sama tamkar zai bar gangar jikinshi tsabar bakin ciki ae bai gama dawowa daga dimuwar da ya shiga ba yajiyo muryar Sarki!! Yace "Ni Almansor Almustapah na baiwa Balaraba Ayuba tanko kujarar Maka sakamakon hazakarta da kokarin ta muna fatan sauran dalibai zasu kara zage damtse gurin jajircewa da bada himma a kan karatu muna fatan wata shekarar daliban dazasu sauke Alku'ani mai girma su ninka na yanzu.

Yana gama fadar haka ya Fara kokarin barin gurin cikin ginshera wacce tazame masa jiki cikin kasaita yaje ya zauna gurin zamanshi yana kallon kowa daidai.

Gefe guda yana mamakin yarinyar da Girman kanta ganin ko kallon in da yake taqiyi ko dame take taqama oho!

*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

📚📚📚📚✍🏻
[04/05, 02:51] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀🧝‍♀

*✍🏻writteng by*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

~*MRS AHAMAD GWADABE*~

_WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU_
08089965176

*🅿5*

Daya bayan daya dalibai suka riqa fitowa suna karbar Allonsu hannun maimartaba kamar yadda yayiwa Balaraba kyauta haka ya riqa yiwa kowa daidai da Matsayinshi.

Sulaiman Ahamad shine yasamu kyauta kwatankwacin ta Balaraba nan shima Sarki! Almansor ya bashi kyautar kujerar maka kamar yadda yabawa Balaraba,

Guri ya hautsine kowa yana taya nashi murna gami da karbar Allon ana sanya Albarka ,nan kaf dalibain da malamai gami da iyayen yara suka jero reras gaban sarki masu photo suka riqa daukarsu domin tarihi .

Sarki ya jiro wasu takkadu ya mikwa shugaban Makarantar wato Arrama Malam Idiris yace" ni Almustaph na malakawa wannan Makaranta Filina dake hayin diga halak malak kuma Na dauki nauyin ginashi da izinin Allah muna fatan zaku kara zage damtse gurin kula da tarbiyar yara da basu ilimi mai amfani.

Allahu Akubar Allahu Akubar Allahu Akubar

Guri ya hautsine da Akabbar Malam idirs ya zube gaban sarki tamkar zaifashe da kuka sabida dadi sai zanba godiya yakeyi
Chapter 2 · 0% Book details