← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 80

Sashe 12

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Iyani ta dago kanta tana kallon Yaron jin ya abanci Gimbiya tasan babu mai wannan sunan sai mutuniyarta Balaraba

Gudar dari biyar ta gani hannun Yaron sabuwa dal

Tayi saurin kallon rumfar Balaraba,aiko suka hada ido Balaraba ta dago mata hannu fuskarta a sake

Iyani ta washe baki tace"Uwar dakina ashe kinzo tun dazu nake tambayar Hauwa'u tace baki karaso ba, kila kina kan hanya, yau kin makara gaskiya"

Fuska a sake tace"wallahi kuwa kinga mun hadu da gosolow a hanya,wai Yaron sarki zai wuce shine fa a ka kashe hanya"

"A'a lallai ai a kashe hanya,cewa zakiyi masu garin ne za su wuce"
Iyani tafada tana tsamo kosai cikin matsami

Tsaki Balaraba ta ja bata kara cewa komai ba ta bar Iyani tana 6a6atun surutunta.

Nan almajirai sukayi dan dazo suna karbar sadaka,ganin haka yasa Balaraba ta kira daya daga cikinsu tace ya shiga kasuwa gurin Delu mai kunu ya karbo na dari biyar shima irin Wanda take daurawa a Leda

Da gudu Yaron ya ruga ya shiga cikin kasuwa sai murna yakeyi

Girgiza kai tayi kawai a fili tace"lallai ko wane Yaro da irin tarbiyarshi, Allah ka shirya mana zuri'armu

Alhaji Yusif ne ya fito yana ta raba ido so yake ya ga inda mutuniyar tashi take sabuda yanzu ya tambayi daya daga cikin yaran ta tace masa sai yanzu ta karaso

Yana sanye da wata muguwar shadda wa gambari mai uban tsada taji sitati sai motsi take yi kanshi da hula zanna bukar kana ganinshi kasan dan birni ne kuma akwai daloli yana da kyau dai-dai misali irin mutanan ne masu qiba amma ba sosai ba

Tana kallonshi yana dube dube tai masa banza,sai ta fito da wayarta ma tana dubawa,

Kamar ance ya kalli gefan damanshi sai ya ganta zaune cikin kujera

Ya kasa boye farin cikinsa sai ya saki dariya,har sai da hakoranshi tas daya yana sanye da hakorin magana, kana ganinshi kasan Alhajin Allah ne.

*🖋YANZU MUKA FARA*
[18/06, 22:42] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

[18/06/2019 3:01 PM] Binta Umar Abbale: [18/06/2019 2:08 PM] Binta Umar Abbale: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_®BINTA UMAR ABBALE_

*MARUBUCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```
08089965176

📚 Zamani writes Association🤝🏻

*Al hayyu Al kayyumu ya Allah*

*🅿27*

_________Kicin-kicin da fuska tayi gami da dauke kanta ta cigaba da danna wayarta tamkar bata san da wata hallita ba a tsaye a kanta.

Gyaran murya yayi fuskarsa dauke da murmushi mai kayatarwa yace"ranki shidade Gimbiyata gaisuwa daban take sarauniyar zuciyar Yusif zuciya takice na baki ki yadda kikeso da ita"

Kanta a kasa tana danna waya har ila yau takasa dago kai ta kalleshi ballantana tabashi gurin zama

Murmushi yayi yace"ko zan iya zama, tun dazu nake nan gurin ina sauraron zuwanki naji shiru, sai yanzu Hauwa'u ta ce dani kinzo"

Dago kanta tayi ta zuba masa idanunta masu rikita masa lissafi, tace"ajiya kabani da zakazo kana nema da sanyin safiyar Allah"

Dariya ya saki mai tattare da shauqi gami da so da kauna sam bai ji haushin kalaman ta ba.

Ya zauna kujerar da take fuskantar ta yace"e mana baki san na baki amanar zuciyata ba"

Mtssss taja kawai ta maida hankalinta kan wayarta gami da duddubawa,ta bawa banza ajiyar Yusuf.

Murmushi ne,kwance a kayatacciyar fuskarsa kwata-kwata yarinyar bata bashi haushi asali ma, wani sabon so da kaunarta ne ya mamaye zuciyarsa

Kawai ya zuba mata ido kawai bai ce mata komai ba

Harara ta ban ka masa gami da cewa"bai yuwa kazo ka tasani a gaba kana kallo tamkar Wanda ya samu madubi, ni kam bana son kallo wallahi"

Har yanzu da murmushi a fuskarsa yace" ke kin fi madubi a gurina tunda kullum dake nake kwana nake tashi a zuciyata,Gimbiya kinki ki amince dani, Why"
Yafada muryarshi na karkarwa

A nutse tace"wace irin amince zan yi maka ne? bayan kasan kai kafi qarfina, ko ni sam bana sha'awar auran namiji mai dukiya ko mulki,talaka zan aura dai-dai dani,nafada maka tuntuni"

"Wai me yasa kike magana irin na jahilai ne,Gimbiya, kituna (Annabi Muhammad Slw) ya auri mace mai tsananin dukiya kuma bazawara, kinga kenan babu laifi cikin abin,namiji ya auri mace mai dukiya,ko mace ta auri namiji mai kudi ko mulki,wannan maganar taki bata da tushe ballantana makama"

Shiru tayi sabida bata da abin cewa

Yace"kinyi min shiru Gimbiya"

Wayar ta kashe ta kalleshi fuskarta babu yabo babu fallasa tace"shikkenan kaje kawai zamuyi maganar ko a waya ne,kaga nan cikin kasuwa ne bana son kallon da mutane ke mana"

"Ok baki dauki maganar da muhimanci ba shiyasa kikace zamuyi a waya wannan ba dai-dai ba ne, me makon kice min inzo gida in sameki, zai fi ai"
Ya karashe maganar yana karyar da wuya,cikin nashi salon.

Wani irin kallo tayi masa mai kama da harara wanda hakan ya zame mata jiki shiyasa mutane suke mata kallon mace mai girman kai gami da izza da takama,

"Ban ga dalilin da zaisa in gayyace ka gidanmu ba,babu wata kyakykyawar magana a tsakanina da kai,kabari tukkuna sai an kwana biyu"

Girgiza kai yayi kawai ya mike tsaye yana kallon agogon hannushi yace"duk abinda kikace haka za'ayi Gimbiyata ina jiran kiran wayarki"

"Ok a sauka lafiya"
Tafada gami da latsa wayar hannuta,

Har ya wuce ya dawo fuskarsa a sake yace"yau baki da sako gurin Mama kilishi"?

Murmushi ne ya subuce mata bata shirya ba,tun sanda ta ga hotan matar a wayarshi taji tana mutukar kaunarta,sosai shiyasa duk lokacin ya zo cin abinci take hada mashi waina(masa) sabida ya fada Mama tanason wainar shinkafa, shiyasa kullum take hada masa da yawa ya kai mata,Mama kilishi har tasan da zaman Gimbiya Balaraba,
[18/06/2019 3:02 PM] Binta Umar Abbale: Mikewa tayi a nutse ya bita da wani mayataccan kallo,duk tana kallonshi, kawai sai taja ta tsaya gami da cewa"kayi gaba ganinan zan kawo maka sakon har gurin da ka aje motarka"

"Menene hujjarki ta fadar haka,? Kina nufin in wuce gaba ke kya biyo ni daga baya, ban yadda ba"?
Yafada gami da bin ta da wank kallo mai dauke da so da kauna

Gaba tayi kawai bata saurare shi ba sabida ta riga ta San mugun nacin sa

Bayanta ya bi yana kare mata kallo ji yakeyi in bai auri yarinyar rayuwarshi zata shiga garari,

Hauwa tasa ta hada mata komai cikin wani take away na mussaman an nan nadeshi da wata Leda mai kyalli a sanya leda mai zurfi, ta fito rike da ledar a hannunta,ta mika masa, "gashi a kai mata ace ina gaidata da kyau"

Cikin murumushi ya karbi ledar har yana kokarin hadawa da hannuta tayi saurin zare hannunta ledar ta kusa faduwa kasa, sai harararshi take

Basarwa yayi yace"zataji insha'Allahu, kizo ki rakani gurin motana"

Share shi tayi ta kawai ta koma gurin zamanta, ta zauna gami da dora kafa daya kan daya, babu abinda ya dameta.

Girgiza kai kawai yayi ya wuce,ya na mamakin izza da mulki na yarinyar ya lura abin a jikinta yake,ko shi da yake dan saurata ba ya yin irin abinda take,asalima sam bayaso a san cewa yana da alaqa da masarautar garin, sai dai dayawa daga cikin abokanshi in sun ganshi cikin kasuwar sai su riqa mamakin mai yakawoshi har dai suka fahimci gurin Balaraba yake zuwa, to babu irin maganar da ba'a fada masa ba a kan Balarabar amma yayi kunnan uwar shegu da jama'a sabida shiyasan wacece Balaraba a cikin zuciyarsa.

*🖋YANZU MUKA FARA*
[20/06, 05:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

[6/19, 12:18] Binta Umar Abbale: [👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*NA*
_®BINTA UMAR ABBALE_

*MARUBUCIYA*
```Nana Khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```

Zamani writes
Association🤝🏻

BISIMILLAHIR
RAHAMANIR RAHIM

🅿28

_______ Biyar saura Ashiru mai Napep ya zo daukarta dama lokacin suke tashi sai da tabbatar su Hauwa sun tsaftace mata gurin komai an wanke an ajeshi in da ya dace sannan ta bawa ko wacce hakkinta sukayi sallama cikin mutumci, Ashiru ya dauketa suka bar kasuwa mutane sai zindanta sukeyi mussaman wadanda suka kawo mata maganar banza a kasuwar ta ci musu mutumci,shiyasa sam basa iyayin munafurce-munafurcensu a gaban idanta sai sun ga bata guri
[6/19, 20:48] Binta Umar Abbale: Abin mamaki suna zuwa dai-dai danja kamar dazu suka tadda uban gosolow gashi yamma tayi duk "yan kasuwa kowa yana kokarin komawa gida, amma an dakatar da jama'a , cikin mamaki Balaraba tace " wai me yake faruwa ne?

kallonta yayi ta cikin mudubin Napep din yana shakkar abinda zai fada mata,yace "ai Sarki Almansor ne ya dawo, ashe sun je daurin aure can gwarzo, maimarta bai samu damar halarta ba sai ya wakiltashi dashi da mai girma waziri Rayyanu"

Tsaki taja tace"Allah ya kyauta, gaskiya an shiga hakkin jama'a dayawa wallahi, daga zai wuce sai a dakatar da jama'a sabida takama da sarauta,sam wannan bazai iya mulkin garin nan ba"
ta karashe maganar tana tabe baki

"yar dariya Ashiru yayi yana satar kallonta gefe guda kuma yana jin tsoran maganar da zai fada mata, amma sai ya dake yace" nura Gimbiya sam Sarki Almansor baya burgeki,kuma baki fahimce shi bane mutum ne shi mai sauqin kai gami da iya mu amula da jama'a yana da tausayin nakasa dashi sosai, matsalarshi kawai muskilanci shiyasa mutane suke masa kallon mutum mai girman kai da izza"

shiru tayi masa batace komai ba, sabida ta lura da Ashiru yayi nisa da kaunar Sarki!

wayarta tafito da ita tana dubawa ranta a bace, ta najin yadda motoci suke gudu kan titi dago kanta tayi tana ya muste fuska, cikin rashin dace idanunsu suka hadu dana juna, cikin sakon daya ya gane ko wacece,sai yayi saurin kauda kanshi gami da gyara kwanciya cikin motar

tabe baki tayi ta kauda kanta,ko daga bacci ta tashi zata iya ganeshi sabida ranar saukarsu ta kare masa kallo, shiyasa in taga ana rububin ganinshi sai tai ta jin haushi sabida ita sam bata ganin kyawunshi da mutane suke zuzutawa

bayan motarshi ta wuce sauran motocin suka dinga wucewa a jere har suka kare,sai sannan a kabawa jama'a damar wucewa,

Agogon dake daure a hannunta ta kalla biyar da rabi sun samu kosan rabin awa a tsaye a titi, giriza kai kawai tayi a zuciyarta tace idan tasan wannan bacin ran zata samu da babu abinda zai kaita fitowa wallahi
Chapter 12 · 0% Book details