Sashe 26
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anutse ta shiga ciki inda ta tarar da Su Hauwa'u suna ta kai wa da kawo wa komai tsaf duk wani costomas an bashi abunda yake bukata, sama-sama suka gaisa da su, fuskarta babu walwala, kullum haka takeyi sabuda bata son wani ya kawo wargi a cikinsu,can gefe guda ta hango Yusuf zaune cikin kujera, ya zuba mata ido,kamar zai cinye ta,fuskarsa dauke da wani kayataccan murmushi, da sauri ta dauke kanta, ta nai wa Hauwa magana,
Reciptoin ta futo ta zauna kan kujerar ta, kamar ko da yaushe, tana kallon masu shige da fuce, a gurin.
Ganin ta futa yasa Maddibo mikewa a nutse ya bi bayanta, mutanan dake gurin suka bishi da kallo, ganin dukaninsu a gurin suka taddashi,gashi ya mike ya futa batare da yaci komai ba.
Zama yayi kujerar dake fuskantar ta fuskar shi dauke da murmushi har ila yau, yace"Ranki ya dade,barka da zuwa"
Sakin fuskarta tayi tace"kai ma ranka ya dade,fatan ka tashi lafiya"?
Bai yi tsammanin zata sakko da wuri haka ba, ganin yadda ranta ya ba'ci jiya, amma abin mamaki ko a fuska bata nuna masa ba,asali ma yau tafi kowane lokaci sakar masa jiki.
Yace"Lafiya kalau, na tashi ke fa"?
"Nima lafiya kalau"
tafada tana yi masa wani kayataccan murmushi.
"Hakuri nazo na bawa Gimbiya sarauniyar zuciya ta"
Yafada yana wani karyar da kai, gwanin tausayi
"Humm Yusuf kenan, wane hakuri zaka bani, ai kai ba kayi min laifin komai ba,wanda yayi laifi shi ya kamata yazo ya bada hakuri in ana so in huce, fushina"
Ta karashe maganar tana wani fari da ido.
Shiru yayi yana binta da kallo,cikin so da kauna, yace"Ayi masa afuwa,Gimbiya na ari bakinsa naci masa albasa, abunda yayi shi, shine yayi ni, A yafe masa"
Girgiza kai tayi tana tabe baki tace"in kaga na hakura to sai dai idan ka dauko shi ka kawo min shi nan yazo gurina a karo na biyu,wannan zuwan nasa ya zama na bada hakuri ne, a gurinshi, shine kawai zai sa na hakura,
Murmushi yayi yana gyada kai cikin zuciyar sa yace"lallai na kara tabbatar da cewar sarauta a jinin yarinyar nan yake,wato ta na nufi yaje ya dauko Sarki! a karo na biyu ya kawo mata cikin kasuwa, lallai lamarin Balaraba ya shallake tunanin sa, ko mutuwa zai yi baya tunanin Sarki! zai yadda yazo kasuwa gurin ta da zumar bata hakuri, sai dai idan zai rufe masa yaki fada masa gaskiya, amma domin ya nuna mata son ta dake cikin zuciyar sa na gaske ne, yasa yace"duk wannan me sauki ne, mutumi na zai iya zuwa ya baki hakuri kamar yadda kike bukata,sabuda dan uwana yana mutukar son abunda nake so"
Harararsa tayi tana fari da ido tace"ni dashi wa kafi so"?
Dariya yasa yana kallonta yace"matsayin ki daban, nashi daban, a zuciya ta, amma bari ki fara ganin naki matsayin a gurina"
ya karashe maganar yana kokarin futo da wayarsa aljihu,
A nutse tace"me zakayi naga ka futo da waya"?
Kashe mata ido daya yayi ya sai ta Camara ta wayar shi ya hau daukar ta a hoto,
Da sauri ta sanya hannu tana kare fuskar ta domin yayi mata bazata,
"Kabari bana so dan Allah"
tafada tana kauda fuskar ta.
Sai da yai mata kusan goma sannan ya dai na
Shan kunu! tayi tana dauke fuska tace"ka dauki hotana ba da yarda ta ba zakaje ka nunawa abokan ka su kalli munina ko"?
Yana dariya kasa-kasa yace"babu wanda zan nunawa sai mutum daya"
"Wanene shi"
tafada cikin sigar tuhuma
"Mutumin ki ne"
Tabe baki tayi tace"har yanzu ban yadda da son da kake min ba har sai kaje ka kawo min shi nan sannan zan yarda da kai"
Wayar shi yake latsawa yana murmushi yace"bari kiga Zahiri,kafin in kawo miki shi bari in kira shi a waya sai kuyi magana"
Numbar Sarki! yafara lalube cikin wayar tasa
Shiru tayi kawai tana kallon shi, duk layin da ya kira a kashe, na ukun ne ya shiga,sai da ta kusa katsewa sannan yaji an daga wayar, da sauri ya bude handsfree ya mika mata,
Ta karbi wayar cikin basar wa
Muryar shi taji kamar ta me bacci, yace"Assalamu alaikum"
Gabanta ne ya fadi! jin muryar shi duk da kasa-kasa take bai hanata jin dadin ta ba,
Cikin jarumta! tace"Amin wa'alaikassalamu"
Jin muryar mace yasa shi sauri tashi zaune, dama a kwance yake a kan wata katuwar Sofa, Mamaki yake, me ya kai wayar Maddibo hannun mace, kwata-kwata bai dauki muryar ta ba,
Gabanshi ya fadi kad'an,tunowar da yayi yanzu haka Maddibo yana gurin yarinyar nan me abunci, sabuda da zai tafi ya fada masa.
Muryar shi ya bude sosai sauti,da a mo suka bayyana, yace"Wacece keee? ina me wayar"?
kitttt!! ta kashe wayar ta mikawa Maddibo, cikin dauriya tace"kiranshi a waya bashi ne zai sai in hakura,kawai ka kawo min shi nan"
Tafada cikin bada umarni"
Girgiza kai yayi kawai yace"ta kwana gidan sauki insha Allah zan kawo miki shi nan"
Sakin jiki tayi suka cigaba da hira cikin nishadi cikin zuciyar ta kuwa murna take ta kusa daukar fansa a kan abunda Sarki! yayi mata.
*Ni ko nace anya zaki iya kuwa Balaraba,amma dai muje zuwa😀*
Bangaran Sarki! kuwa kashe wayar da tayi, yayi mutukar bata masa rai sosai,domin ya tsani yana waya a kashe masa, ranshi a mugun bace! ya fara kiran wayar, lokacin Maddibo ya kashe, sabuda ya san dole zai kara kira yaji ba'asi sabuda yasan Wayar sa ce,
*Comment*
*Vote and Share*
[13/07, 06:19] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®REAL BINTU BATULA👄*
*MARUBUCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```
_*Zamani Writes Association*_🤝🏻
_*DEDIGATED*_
_*TO*_
```{RAHAMA ALIYU}```
*🅿47*
```Bisimillahir-rahamanir-rahim```
Sau uku yana kiran wayar bai dauka ba,gashi ta na ringin, amma sabuda tsabar rainin hankali irin na Maddibo yaki dagawa,kashewa wayar yayi ransa a bace, yanzu ya tabbatar da cewar Maddibo ya kira wayarsa ne domin ya bawa yarinyar tai masa wulakanci.
Sai kusan Sha biyu da rabi na rana Maddibo ya yi wa Balaraba sallama, har inda yayi parking din motarsa ya ta rakoshi, mutane suka dinga bunsu da kallo, wadanda suka san Maddibo suka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa.
Balaraba, Zuciyar ta ta amunce da Maddibo sabuda kyawawan halayen sa,ta lura ya san abunda yake,a rayuwa, zata iya auransa, zata cigaba da addu'a Allah ya yi mata zab'i mafi alkairi a gareta,
amma duk da haka ta nan a kan bakanta, ba zata nuna masa yardar ta da wuri ba har sai ya kawo mata Sarki! tarama abunda yayi mata.
Sosai Sarki! ya nunawa Maddibo bac'in ransa a kan abunda yayi masa, yace"dan tsabar rainin hankali,ka kira waya ka bawa wata, ina magana,a kashe min waya,kar ka k'ara yi min haka"
Ganin yadda Sarki! yake masa hayaniya yasa yayi masa shiru har sai da ya yi mai isarar sa,sannan Yace"in kagama fadan sai ka saurare ni"
Ko kallonsa baiyi ba, ya cigaba da karka'da kafar sa,
Maddibo yace" tabbas Na kira wayarka, kuma na bawa Balaraba, sabuda ina so in dai-dai ta alakar ku da ita, ni nakasa gane, wace irin gaba ce a tsakanin ku, yanzu da zan tawo ma tace in gaishe ka" Ya karashe maganar yana satar kallonsa, ganin ko kallonsa bai yi yasa ya cigaba da cewa"ga hotonan da nayi mata ma"nuna masa wayar yake, wai ya kalla, shi kuwa ya wani sha kunu yak'i kalla sai ma ya dauki tashi wayar dake gefe a jiye ya hau latsawa, Maddibo bai yi zuciya ba, yace"Mutumi na kalli nutsuwa da kamun kai gurin yarinyar nan dan Allah"
Kamar da dutse yake magana, Sarki! ya share shi,
Girgiza kai kawai yayi yana murmushi, ya aje wayar kan kujerar ya mike ya nufi bedroom din Sarki, domin yin wanka, badan baiyi da safe ba,kawai shima yanayin sa kamar na Sarki! ne baya son zafi,kullum cikin wanka, duk da haka Sarki ya fishi, sabuda shi ko da sanyi ne, sai ya kunna AC sannan yake iya bacci.
Minti biyar da ta tashin Maddibo, ya dago kanshi yana kallon wayar Maddibo dake aje kusa dashi, a zuciyar shi, sai yaji yana son yaga hotan Yarinyar, har ya mika hannu zai dauki wayar wata zuciyar tace masa,me zakayi da hotanta, yarinyar da ta zage ka, kawai sai ya dauke hannushi yq cigaba da duba wayarsa yana jin wani abu cikin ransa a game da yarinyar,
Kasa hakura yayi ya mika hannushi a karo na biyu ya dauko wayar, ya fara dubawa,
Shagala yayi da kallon hotonan,Sosai yake kare mata so yake ya hango wani abu na aibu a tattare da ita bai hango ba, Jikinshi ne yayi sanyi, sosai tabbas wannan yarinyar itace wacce yake gani cikin mafarkin sa, da sauri ya dauki wayar sa a gurguje a tura hotonan cikin wayar sa baya so Maddibo ya futo ya same shi yana duba masa waya,aikuwa motsin sa yaji yayi sauri ya mai da wayar ya aje inda take,Allah yasa ya gama turawa
Cikin jallabiya me yankakken hannu ya futo, ya zauna kusa dashi, da murmushi a fuskar sa yace"Mutumi na ina labari, ya kamata fa ka dai na wannan fushin domin auran Balaraba babu fashi" yafada yana dariya, ya cigaba da cewa"kai nifa daga yau na zama Balarabe,na Balaraba,kaga wanda zai yi mana wak'ar bukinmu ya huta"
Dariya ce ta sub'uce wa masa bai shirya ba, yace"Wallahi kasa ni nayi dariya, ban yi niyya ba naji haushin abunda kayi min d'azu"
Shima dariyar yake yace"ko dai naji haushin abunda kayi min jiya, haka kawai, zaka sanya ni a kwana, badan na buga sammako naje na wanke kaina ba, a gurin ta, da tuni sai dai in ga ana yi"
Gaskiya ina son yarinyar nan sosai, ka dubi Allah ka tayani sonta, ka sauke duk wani abu dake damun ka a kanta"
ya karashe maganar yana kwantar da kai.
Tab'e baki yayi hankalin shi na kan wayar sa yace"kai ka kyale ni don Allah, kowa yaji da tasa matsalar, meye alaka ta da ita,da zaka ce dole in saki jikina da ita, ni babu ruwana, tunda kana ganin zaka iya zama da ita,Allah ya sanya al'kairi amma a zuciya ta sam ba nai maka sha'awar ka aure ta"
"Meye dalilin ka na fadin haka"?