Sashe 57
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hira suke irin ta abokai Sarki! Yana daga kishin gid'e yake sa musu baki, zumbur! Ya mik'e da sauri ya nufi tv memory ya zura jikin DVD ya kuna sai gasu shida Maddibo sun bayyana jikin faskekiyar TV plasma dake manne jikin bango, suna zaune cikin makaranta a can america new york, can sukai karatunsu, wani abokinsu ne me yawan yi musu photo da vidio, ranar dai Sarki! Ya samu memori ya bashi yace duk sanda suke zaune shida Moddibo suna karatu ko suna wani abun Ku suna hurawa to kawai ya dunga d'aukar su a hota ko yayi musu video aiko Ashir baya gajiya mutuk'ar yana kusa idan yagansu sun keb'e kawai sai ya ciro memori a zura a wayarsa yayi tai musu hotuna had'e da video.
Shahid da Shatima duk sun rud'e ganin Moddibo jikin tv kamar kayi masa magana ya amsa,kai wannan duniyar abar tsoro ce.
Balaraba na shigowa idanunta suka sauka akan fuskar tv Moddibo tayi tozali dashi yanai wa Sarki! Magana yana dariya
Kwandon da yake hannuta ta saki ta k'wala k'ara jikinta ya fara k'arkarwa, "Inallahi wa'ina ilahi raji'un"
Jin gina tayi da bango tana sauke a jiyar zuciya bakinta sai motsi yake.
Dukaninsu kallon ta suke sosai saboda ba suji lokacin da ta shigo ba, sai ihunta da sukaji Shahid ya zubawa fuskarta ido yana tunanin a ina yasan fuskar tabbas yasan me wannan fuskar
Shatima kuwa gulma yake son yayiwa Sarki! Sai ya lura babu fuska yaja bakinsa yayi shiru,amma fa bakinsa da akwai magana, domin yana kokwanton anya ba wannan ce,Balaraba da yaji Mama tana yawan ambatar sunanta ba.
Tv take kallo babu k'iftawa wasu hawaye masu zafi suna biyo kumatunta. Maddibo ne yake magana tamkar ta kirashi ya amsa mata.
In banda sautin kukan Balaraba babu abunda yake tashi a falon, Tsura mata ido yayi babu k'iftawa, wato har yanzu yarinyar nan bata far kukan mutuwar Moddibo ba kenan,a ganinsa ta shigo musu babu sallama kuma tazo tanai musu kuka babu gaira babu dalili.
Shatima ne da ya fuskanci kukan me take ya tashi da sauri yaje ya kashe tv d'in ya dawo ya zauna yana mamakin ta.
Shahid ne ya mik'e ya k'arasa inda take tsaya ya fara rarrashinta da kalmomi masu sanyaya zuciya, ya jima yana tausar zuciyarta sannan tayi shiru tana share hawayen ta, k'okarin futa take ba tare da tace musu komai ba.
Shahid yace"Ranki ya dad'e ai baki bamu abuncin ba, zaki futa kuma bamu gaisa ba, ya kamata kizo ki duba mutumin naki kafun ki futa"
Shahid yana da k'ima da mutumci a idonta, ta lura yasan abunda yake, kallonsa tayi babu yabo babu fallasa ta gaishe ya amsa fuskarsa a sake, tare suka jera suna tafiya har cikin falon.
D'auke kansa yayi daga kansu, yarinyar yau tayi masa kyau sosai tamkar wata balarabiyar k'asar saudia shigar tayi mata kyau, yana so ya ga mace na suturce jikinta.
Hannuta rik'e da kwandon abuncin ta nufi gurin cin abunci,shi kuma Shahid ya zauna kusa da Sarki! Suna magana k'asa-k'asa.
Mik'ewa yayi yana mik'e duk jikinsa ciwo yake masa, Tashi sukayi suka bi bayan sa.
Tsaf! Ta had'a musu kowa da plate d'insa, ta kalli Shatima da yake satar kallonta sosai yarinyar tayi masa kwarjini da yawa.
A nutse tace"Ina wuni"?
Shatima ya amsa da sauri sai murmushi yake yace"Lafiya lau amaryar mu, yo ke haka ake daga shigowa sai ki fara kuka uhum"?
Shiru tayi tana satar kallon Sarki! Da yake juya abunci da alama yunwa yake ji, tunda yake Neman abunci da kansa, tarasa wani irin mutum ne shi da baka gane gabansa da bayansa fuskarsa a sake take amma ko da wasa yak'i kallon inda take, abuncin sa yake ci kawai, su Shatima sun rik'eta da suturutu ita kuma tana ta k'okarin yaya za'ayi ta gudu domin mutuminta da yayi mata wani mugun kwarjini gashi tana so ta gaidashi amma babu fuska. Da k'yar dai tace" Barka da yamma"?
Shiru gurin yayi su Shahid suna kallonsa sun san da shi ake"
Lumshe idonsa yayi ya cigaba da cin abuncin sa, bai amsa ba. Shatima yace"Ana magana fa"
Da gefen ido ya kalleta ya d'an tab'e bakinsa yace" Naji ai bazan amsa ba, tunda duk sai da ta gama wulak'ancin ta sannan"
Shatima yace"Amarya ce fa kasan amarya bata laifi komai tayi dai-dai ne"
Wani irin kallo yayi mata me d'auke da ma'anoni daban-daban yayi wani murmushi irin na gefan baki,yace"Ai ba ita kad'ai gare ni ba, Anjima kad'an nasan Halisa nan tafe,kaga kuwa ai bazan damu ba"
Balaraba sarkin d'aukar zafi! Fuska ta turb'une duk idanta ya rufe,wani kallo ta watsa masa,suka had'a ido dashi, tsaya wa yayi yana mamakinta, wani irin Abu tayi da idonta ta kalli su Shatima muryar ta a cunkushe tace"Ni zan wuce ku tashi lafiya"
Sauka tayi daga kan step d'in ta fara tafiya a nutse zuciyarta duk babu dad'i ta lura Sarki! Zuma ne shi ga zak'i ga harbi,dubi yadda kwana ki ya dunga lallab'ata har tana yi masa d'aukar mutum me saukin hali a she ba haka bane,wannan halin nasa nan, halin wulaknci da raina mutum,yo ita ina ruwanta ko mata dubo zai aura a rana d'aya ba damuwar ta b'ace,shine bai sani ba ita tafi sha'awar zamanta a haka tunda tayi rashin babban masoyinta Modiibo.
Shatima yace"Allah ya huci zuciyar gimbiyar mata, ai dukaninsu kin sha gaban su, kar ki manta ke fa amanrmu muce,bayan haka kuma kina da babban matsayi a zuciyarmu ki kwantar da hankalin ki.
Ko waigo wa batayi ba, ta bud'e Kofa tai fucewarta Rahila na tsaye na jiran futuwar ta sai ta take mata baya.
Shahid yace"Lallai addu'a ta ta karb'u, wannan yarinyar ba itace wannan yarinyar da sukayi saukar alk'urni shekaru biyu da suka wuce ba"?
D'aga kansa yayi kawai.
Shahid yace"Allah sarki Moddibo Lallai na yarda zuciyoyinku d'aya duk abunda kuke so iri d'aya ne,Allah bai hukunta zai aure ta,ba sai ya kawo maka ita har gida"
Shatima yace"Ni wallahi abunda kayi mata ne ya bani haushi da alama yarinyar tana da hankali da nutsuwa,kawai sai ka ci mata fuska, kasan dole taji babu dad'i a zuciyarta.
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*
_*MARUBUCIAR*_
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_
_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
*🅿91*
Balaraba tayi k'asa da idanunta domin baza ta iya jurar had'a ido dashi saboda kwarjini da Allah yayi masa.
Niyar koma dakin take, yayi gyaran murya tsayuwa tayi. Ta d'an waiwayo suka had'a ido lumshe nasa yayi ya bud'e baki a hankali yace"Jimana"
Sak tayi jin abunda yace wai jimana! Sai kace Wanda bai san sunanta ba.
Ahankali ta taka ta k'arasa inda yake zaune, mik'ewa yayi yana gyara zaman sa,idanunsa a kanta, ita kuma tana tsaye gefansa duk jin ta take a takure, sai gyara fuskarta take.
"Zauna zamuyi magana dake"
Cikin k'asaita gami da jan'aji ta zaune kujerar gefansa.
Cikin bada umarni yace"Ki dawo wannan domin maganar da zamuyi dake tanada muhimanci"
Kujerar da yake nuna mata ta kalla, ita fa bataso tana had'a ido dashi domin. Idanunsa suna mutukar kashe mata jiki. Dakewa tayi tace"Duk maganar da zamuyi muyi ta anan da can da nan duk d'aya ne"
Shiru yayi na minti biyu, yace"Na fi so ina kallon fuskarki maganar zata fi armashi"
Tab'e baki tayi tana d'an hararsa, minti biyu da maganar tasa ta mike a nutse taje ta zauna kujerar da ya nuna mata, zama tayi irin Wanda ake Dora kafa d'aya kai d'aya.
Kallonta yayi yana mamakin zaman k'asaitar da tayi, babu Wanda ya isa yayi irin Wannan zaman a gabansa, ba tare da ya karb'i hukunci ba, amma da yake ya san halinta sai ya share kawai ya gyara fuskarsa sosai idanunsa ya zuba mata babu wasa yace"Inaso ki yi min bayanin Asalinki dana mahaifiyar ki, domin inajin a jikina akwai wani al'amari a game dake, bazan b'oye miki ba, nafi k'arfin shekara goma shabiyar ina mafarki dake tare da wata mata da alama mahaifiyar ki CE,tunda kullum tare nake ganinku kuna zuwan min cikin mafarkina, wannan mafarkin babu Wanda yasan dashi sai ni sai ke, yanzu Dana fad'a miki"
******
******
******
A kori kura guda biyu aka cika da kayan masarufi, su Shatima suka nufi gidan su Balaraba inda suka samu rakiyar daga Bubu direba tunda shi kadai ne yasan gidan.
Sosai Shahid yayi mamakin inda mahaifar Balaraba take,ashe dama 'yar talakawa ce tilis, Lallai so babu ruwanshi ko a mafarki bai tab'a tunanin zai iya zuwa irin wannan gurin ba, Soyayar da Moddibo yakewa Balaraba ta gaske CE. Tabbas yayi mamaki da ya kalli yanayin jikinta da fatar ta, idan zata kwana tana rantsuwar babu Wanda zai CE a cikin irin wannan guri take rayuwa.
Yara ne suka fara taruwa a gurin suna tsale suna d'ane mota sai su ruga da gudu, hankalin Samar in dake can tsallake ya dawo Kansu da sauri suka k'araso gurin, Buba Direba ya bud'e mota da sauri ya futo ya bud'e wa su Shahid suka futo, ganinsu cikin kayan sarauta yasa yara zurawa da gudu zuwa gidajansu suna ihu! Suna fad'in ga sarki! Sarki ga sarki! Mutane suka fara lekowa daga gidajansu. Da sauri Shahid ya umarci matasan nan dake tsaye a gurin yace su fara d'ibar kayan nan suna shiga dashi, lungun su Balaraba, Buba yayi gaba, sukuma suka koma cikin motar saboda hayaniyar jama'a, yuuuuuu!! Jama'ar dake gurin yara da manya suka rufa musu baya domin ganin ina za a shiga da wannan uban kayan masarufi.
Lantana ta sawo Kai kenan zata futo daga cikin gidan suka buga karo da Sauri ta koma da baya tana masifa!
Abokin Walidi yace"Lantana ina zakije ne"?
D'ago kai tayi a fusace za tayi masa masifa"Aik.. Idonta ya sauka kan k'aton buhun shinkafar dake kansa ta bud'e baki kenan za tayi magana, sai ta hango matasa hud'u kowanne kansa da buhun shinkafa irin na kan Abokin Walidi kuma da alama suma gidan zasu kaita,, Zanin jikinta ne ya sabule garin sauri ta buge da kyaure bata damu ba, da sauri ta tsugans ta dauki zaninta da ya fad'i k'asa tana tafiya tana d'aura wa gami da k'walawa Maburuka kira.